Connect with us

Labarai

Za’a fuskanci hazo mai duhun gaske na kwanaki biyu – NIMET

Published

on

Hukumar hasashen yanayi a Najeriya NiMet) tayi hasashen fuskantar hazo mai yawa daga ranar Juma’a 6 ga wata zuwa Lahadi 8 ga watan Janairu a fadin kasar nan.

Bayanin hakan ya fito ta cikin wata takardar hasashen yanayi da NiMet ta fitar a babban birnin tarayya Abuja.

Jihohi daga Arewacin kasar nan da suka hada da Yobe, Kano, Katsina da Jigawa zasu fuskanci hazo mai duhun gaske a kwanakin.

Hakazalika, sauran jihohin yankin na Arewa, manyan birane da yankunan Kudanci su ma za su fuskanci hazon

Jihohin Kwara da Oyo kuwa, za su shaida hazon da ya yi kasa da na Arewaci da kuma kudancin kasar nan kamar yadda hasashen ya nuna a cikin kwanakin uku masu zuwa.  Hukumar na shawartar ‘yan kasar nan da su dauki matakan kariya domin magance matsalolin da ke tattare da wannan yanayi.

A bangare guda su ma kamfanonin jiragen sama an shawartar su da su dakata da zirga-zirga da keta hazo cikin kwanakin har sai yanayin ya koma daidai.

Labarai

Mu yawaita karanta Alƙur’ani da aikin alkhairi a watan Ramadan – Malam Ibrahim Bunkure

Published

on

Limamin masallaacin Juma’a na Salafussalih dake unguwar Ɗorayi ƙarama Malam Ibrahim Abdullahi Bunkure, ya shawarci al’ummar musulmi da su ƙara himma wajen karanta Al-ƙur’ani mai girma, tare da aikata ayyukan alkhairi domin rabauta da rahamar Allah S.W.T a nan duniya dama gobe ƙiyama.

Mallam Ibrahim Bunkure ya bayyana hakan ne lokacin da yake tsokaci kan huɗubar Juma’ar da ya gabatar yau a masallacin.

Ya ce, kamata yayi musulmai su ƙara yin koyi da kyawawan ɗabi’un Annabi Muhammadu Sallallahu alaihi Wasallama, domin zama ababen koyi a rayuwa.

Wakilinmu Hassan Mamuda Ya’u ya rawaito cewar Mallam Ibrahim Abdullahi Bunkure, ya kuma shawarci al’umma da su ƙara kasancewa masu yafiya musamman a lokacin da aka yi mutu abinda bai musu daɗi ba, bisa mahimmancin da hakan yake da shi.

Continue Reading

Labarai

Marayu na buƙatar tallafi sosai – Kwamared Abu Saleem

Published

on

Shugaban ƙungiyar tallafawa Marayu da ci gaban al’umma ta ƙaramar hukumar Birnin Kano Kwamared Adam Umar Abu Saleem, ya ce ƙarancin samun tallafi daga masu ƙarfi ne ke sanyawa Marayu ke faɗawa cikin mawuyacin hali.

Kwamared Adam Abu Saleem na wannan jawabin ne yayin zantawarsa da gidan rediyon Dala FM, lokacin musabaƙar Alƙur’ani mai girma na marayu ƴan ƙaramar hukumar Birni 5 yayin da ɗalibi dake Karkasara Ja’afar Aliyu Abubakar ya zama gwarzon shekara na ƙaramar hukumar wanda aka ɗauki nauyin al’amuran rayuwarsa baya ga kyaututtuka da ya samu, wanda Musabaƙar ta gudana cikin Firamen Salanta a ranar Asabar.

Wakilinmu Hassan Mamuda Ya’u ya rawaito cewa Kwamared Adam ya ce sukan shirya Musaɓakar ne domin zaburar da Marayu akan harkokin karatun Alkur’ani mai girma, da kuma rage musu wani tunanin maraici da suke kasancewa a maban-banta lokuta.

Continue Reading

Labarai

Lokacin zaɓe: Rundunar ƴan sanda ta shirya daƙile tayar da tarzoma – SP Kiyawa

Published

on

Rundunar ƴan sandan jihar Kano ta ce, ta shirya wajen samar da tsaro, tare da ɗaukar matakin da ya dace ga ɓata garin da suke shirin tayar da tarzoma.

Jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ƴan sandan jihar Kano SP Abdullahi Haruna Kiyawa ne ya bayyana hakan ga Wakilinmu Hassan Mamuda Ya’u a yau juma’a, yayin da yake tsokaci kan shirin da rundunar su ta yi kan zaɓe.

Continue Reading

Trending