Connect with us

Manyan Labarai

Jam’iyyar PDP ta magantu kan kalaman Tinubu.

Published

on

Tambarin jam'iyyar PDP
  •  PDP tayi Allah wadai da kalaman Tinubu na cewa yazo kano ya taka rawa.
  • Tinubu bai fadi wani abu da zai ciyar da Kano gaba ba.

 

Jam’iyyar PDPn Kano ta bayyana rashin jindadin ta kan kalaman da Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC Asuwaju Bola Ahmad Tinubu yayi a taron bayar da tuta da jam’iyyar tayi anan Kano ranar Laraba.

Sakataren tsare-tsaren jam’iyyar na Kano Hon Sunusi Surajo Kwankwaso shi ne ya bayyana hakan yayin ganawar sa da wakilin Dala fm.

Akwai abubuwa da dama da suka damu Jihar kano, Kamar kwacen waya, rashin aikin yi, matsalar ilimi da sauran matsaloli, amma Tinubu bai fada mana manufar sa ko daya akan wadannan abubuwan ba, sai kawai cewa yayi yazo kano yayi rawa.”

“Mu Jihar kano ba ma bukatar masu rawa, a don haka jam’iyyar PDP tana Allah wadai da wadannan kalamai.”

A ranar larabar ne dai 04 ga watan Janairu 2023 Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC Asuwaju Bola Tinubu yazo Jihar kano, wanda a kalaman da yayi yace yazo kano ne domin yayi rawa.

Manyan Labarai

Gawuna ya taya Abba Gida Gida murna

Published

on

Dan takarar Gwamnan Kano na jam’iyyar APC a zaben 2023 Dakta Nasiru Yusuf Gawuna ya bayyana karbar kaddara tun bayan da ya Fadi zaben 18 ga watan Maris.

Cikin Wani Sakon murya, Dakta Nasiru Gawuna ya godewa magoya baya, tare da yin fatan alkhairi ga sabuwar gwamnati.

” Wannan sabuwar gwamnati Allah ya Bata ikon yiwa al’umma adalchi, mu Kuma Allah ya bamu ikon yin biyayya.”

 

 

Continue Reading

Manyan Labarai

Abba Gida Gida ya karbi shaidar lashe zabe

Published

on

Sabon zaɓaɓɓen gwamnan jihar Kano Injiniya Abba Kabiru Yusuf wanda aka fi sani da Abba Gida gida ya karbi shaidar lashe zaben Gwamnan Kano.

Ya karbi wannan shaida ce yayin wani taro da hukumar INEC ta shirya domin bashi shaidar satifiket, bayan nasarar da ya samu a zaben ranar 18 ga watan Maris 2023.

Taron dai Wanda ya samu halartar da dama daga cikin manyan jihar Kano dama shiyyar arewa maso yamma, ya gudana ne a dakin taro na ofishin hukumar zabe INEC na jihar Kano.

Continue Reading

Labarai

Marayu na buƙatar tallafi sosai – Kwamared Abu Saleem

Published

on

Shugaban ƙungiyar tallafawa Marayu da ci gaban al’umma ta ƙaramar hukumar Birnin Kano Kwamared Adam Umar Abu Saleem, ya ce ƙarancin samun tallafi daga masu ƙarfi ne ke sanyawa Marayu ke faɗawa cikin mawuyacin hali.

Kwamared Adam Abu Saleem na wannan jawabin ne yayin zantawarsa da gidan rediyon Dala FM, lokacin musabaƙar Alƙur’ani mai girma na marayu ƴan ƙaramar hukumar Birni 5 yayin da ɗalibi dake Karkasara Ja’afar Aliyu Abubakar ya zama gwarzon shekara na ƙaramar hukumar wanda aka ɗauki nauyin al’amuran rayuwarsa baya ga kyaututtuka da ya samu, wanda Musabaƙar ta gudana cikin Firamen Salanta a ranar Asabar.

Wakilinmu Hassan Mamuda Ya’u ya rawaito cewa Kwamared Adam ya ce sukan shirya Musaɓakar ne domin zaburar da Marayu akan harkokin karatun Alkur’ani mai girma, da kuma rage musu wani tunanin maraici da suke kasancewa a maban-banta lokuta.

Continue Reading

Trending