Manyan Labarai
Gwamnan jihar kaduna ya umarci yan jihar da su cigaba da amfani da Tsofaffin kudi

Gwamnan Jihar Kaduna Malam Nasir El-Rufai ya umarci al’ummar jihar da su cigaba da amfani da tsofaffin takardun kuɗi na naira 500 da 1000 bayan da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya fitar da sanarwar matsayin Babban Bankin ƙasar na soke amfani da kuɗin.
A wani jawabi da gwamnan ya yi ga al’ummar jihar da yammacin ranar da Shugaban kasa yayi jawabi,ya bayyana shirin canja kuɗin a matsayin wani makami da jiga-jigan jam’iyya mai mulki da makusantan Shugaba Buhari suka ɓullo da shi domin dakatar da ɗan takarar shugaban ƙasa na APC, Bola Tinubu nasara a zaben 25 ga watan nan na Fabrairu.
Gwamnan ya bayyana shirin a matsayin na rashin adalci, wanda ya haddasa talakawan ƙasar tsananin wahala, waɗanda ya ce su ne shirin ya tagayyara.
El-Rufa’i Ya ce shugabancin Babban bankin ƙasar, CBN, ya yaudari Shugaba Buhari da cewa an ɓullo da shirin ne da nufin daƙile ‘yan siyasa da suka tara maƙudan kuɗade domin sayen ƙuri’a lokacin zaɓe.
Gwamnan ya kuma ba al’ummar jihar shi tabbacin su ci gaba da amfani da tsofaffin 500 da 1000 kamar yadda ya ce Kotun Kolin kasar ta bayar da umarni.
Yadda ta Kaya a taron masu ruwa da tsaki kan karancin kudi a kano
Ya ce babu wani wa’adi da zai sa kuɗin su daina aiki,inda ya kara da cewa bayan zaɓe shi da sauran ‘yan majalisa zaɓaɓɓu da hukumomin gargajiya za su tattara kuɗin daga hannun jama’a su mika su ga Babban Bankin domin a sauya su.

Manyan Labarai
Gawuna ya taya Abba Gida Gida murna

Dan takarar Gwamnan Kano na jam’iyyar APC a zaben 2023 Dakta Nasiru Yusuf Gawuna ya bayyana karbar kaddara tun bayan da ya Fadi zaben 18 ga watan Maris.
Cikin Wani Sakon murya, Dakta Nasiru Gawuna ya godewa magoya baya, tare da yin fatan alkhairi ga sabuwar gwamnati.
” Wannan sabuwar gwamnati Allah ya Bata ikon yiwa al’umma adalchi, mu Kuma Allah ya bamu ikon yin biyayya.”

Manyan Labarai
Abba Gida Gida ya karbi shaidar lashe zabe

Sabon zaɓaɓɓen gwamnan jihar Kano Injiniya Abba Kabiru Yusuf wanda aka fi sani da Abba Gida gida ya karbi shaidar lashe zaben Gwamnan Kano.
Ya karbi wannan shaida ce yayin wani taro da hukumar INEC ta shirya domin bashi shaidar satifiket, bayan nasarar da ya samu a zaben ranar 18 ga watan Maris 2023.
Taron dai Wanda ya samu halartar da dama daga cikin manyan jihar Kano dama shiyyar arewa maso yamma, ya gudana ne a dakin taro na ofishin hukumar zabe INEC na jihar Kano.

Labarai
Marayu na buƙatar tallafi sosai – Kwamared Abu Saleem

Shugaban ƙungiyar tallafawa Marayu da ci gaban al’umma ta ƙaramar hukumar Birnin Kano Kwamared Adam Umar Abu Saleem, ya ce ƙarancin samun tallafi daga masu ƙarfi ne ke sanyawa Marayu ke faɗawa cikin mawuyacin hali.
Kwamared Adam Abu Saleem na wannan jawabin ne yayin zantawarsa da gidan rediyon Dala FM, lokacin musabaƙar Alƙur’ani mai girma na marayu ƴan ƙaramar hukumar Birni 5 yayin da ɗalibi dake Karkasara Ja’afar Aliyu Abubakar ya zama gwarzon shekara na ƙaramar hukumar wanda aka ɗauki nauyin al’amuran rayuwarsa baya ga kyaututtuka da ya samu, wanda Musabaƙar ta gudana cikin Firamen Salanta a ranar Asabar.
Wakilinmu Hassan Mamuda Ya’u ya rawaito cewa Kwamared Adam ya ce sukan shirya Musaɓakar ne domin zaburar da Marayu akan harkokin karatun Alkur’ani mai girma, da kuma rage musu wani tunanin maraici da suke kasancewa a maban-banta lokuta.

-
Nishadi3 years ago
Ina neman mijin aure – Rayya
-
Manyan Labarai3 years ago
KAROTA: An baiwa Baffa Babba wa’adin kwanaki bakwai
-
Labarai3 years ago
Auren dan Panshekara da ba Amurkiya ya samu cikas
-
Nishadi3 years ago
Mansura Isah ta yi kaca-kaca da Sadiya Haruna
-
Labarai2 years ago
Hamisu Breaker ya kai kan sa wajen ‘yan sanda
-
Lafiya10 months ago
Rahoto: An gano wani gida da ake gini da takardun Kur’ani da Alluna
-
Nishadi3 years ago
An gano daliban da Adam Zango ya dauki nauyin karatun su
-
Manyan Labarai3 years ago
Sabuwar damfarar da ta fito a Kano