Connect with us

Manta Sabo

Kotu ta aike da wata mata gidan Yari kan zargin ta da yanke maƙarfafar mijin ta a Kano  

Published

on

Kotun majistret mai lamba 54 ƙarƙashin jagorancin mai Shari’a Ibrahim Mansur Yola a jihar Kano, ta fara sauraron wata ƙara wadda ƴan sanda suka gurfanar da wata mata mai suna Maryam Imam mazauniyar garin Tofa, inda ake zargin ta da laifin yanke makarfafar mijinta Abubakar Imam.

Yayin da aka karanta wa matar ƙunshin tuhumar da ake mata ta amsa nan take, ta kuma shaidawa Alkalin kotun cewar tun farko auren dole akayi mata, kuma shi mai gidan nata duk da yasan cewar bata kaunarsa amma kullum sai ya ɓata mata rai.

Mai Shari’a Mansur Yola ya ayyana cewar za a yi hukunci ranar 11/6/2024 dan gudun nama ya dawo romo ɗanye, tunda dai ance Abubakar din yana kwance a asibiti yana ci gaba da samun kulawar likitoci.

Kotun ta kuma umarci a ajiye matar a gidan gyaran hali zuwa waccan ranar da aka sanye domin yanke hukuncin.

Wakilunmu Yusuf Nadabo Ismail ya so zantawa da matar da ake zargi da yankewa mijin nata maƙarfafa, sai dai dogarawan gidan gyaran hali sun shiga tsakani, hakan ya sa lamarin ya gagara.

Manta Sabo

Kotu ta zartas da hukuncin rataye wani mutum har sai ya dai na numfashi a Kano

Published

on

Babbar Kotun jahar Kano mai lamba 11 ƙarƙashin jagorancin mai Shari’a Nasir Saminu, ta zartas da hukuncin kisa akan wani mutum wanda kotun ta samu da laifin fashi da Makami.

Mutumin mai suna Abdurraham Yakubu mazaunin karamar hukumar Bele dake jihar Nassarawa, kotun ta same shi ne da laifin yi wa mutane da yawa fashi da makami ta hanyar amfani da muggan Makamai.

Cikin mutanen da mutumin ya yi wa fashin hadda wata mata mai suna Barrister Hajara Lawal Ahmad, wadda ya yi wa fashin mota da kuma Kuɗi.

Yayin da ya ke zartas da hukuncin mai Shari’a Saminu ya ayyana cewar, Kotun ta gamsu da shaidun da lauyan gwamnati Barrister Umar Yakubu ya gabatar, inda kotun ta yi watsi da shaidar da Abdurraham ya bayar domin kare kansa.

Kotun ta kuma bayyana cewar ta gamsu da muggan makaman da aka samu a hannun Abdurraham haramtattu ne, kuma ana tasarifi da su ta haramtacciyar hanya dan haka kotun ta yi umarnin a kashe shi ta hanyar rataya.

Wakilin Dala FM Kano, Yusif Nadabo Isma’il ya ruwaito cewa, bayan yanke hukuncin mai Shari’a Saminu ya yi masa addu’ar cikawa da kyau.

Continue Reading

Manta Sabo

An yanke wa wani Matashi hukuncin kisan kai ta hanyar rataya bayan samun sa da laifi a Kano.

Published

on

Babbar Kotun jaha mai lamba 7 karkashin jagorancin mai Shari’a Amina Adamu Aliyu, ta zartas da hukuncin kisa ta hanyar rataya akan wani matashi mai suna Abba Sulaiman, bisa samunsa da laifin kisan kai.

Tun da fari gwamnatin jahar Kano ce ta gurfanar da matashin a gaban kotun da kunshin tuhume-tuhume guda biyu.

An dai yi zargi matashin Abba da laifin hada baki da kisan kai.

Tashar Dala FM Kano, ta rawaito cewa, ƙunshin zargin ya bayyana cewar wani lokaci a cikin shekarar 2019, Abba Sulaiman ya haɗa baki da wasu matasa waɗanda a yanzu suka tsere, bayan da suka kashe wani matashi a unguwar Sauna Kawaji.

Yayin da take karanta hukuncin mai Shari’a Amina Adamu ta ayyana cewar, kotun ta karɓi shaidun masu gabatar da ƙara yayin da aka yi watsi da shaidar da Abban ya bayar dan kare kansa.

Wakilinmu Yusuf Nadabo Isma’il ya ruwaito cewar, kotun dai ta kuma ɗaure Matashi Abba Sulaiman shekaru biyar a laifin haɗa baki.

Continue Reading

Manta Sabo

Kotu ta tsayar da ranar sauraron shaida a shari’ar Mai Kayan Miya da ake zargi da binne gawarwaki a cikin gidan sa a Kano.

Published

on

Babbar kotun jiha mai lamba 24 karkashin jagorancin mai Shari’a Aisha Mahmud, ta sanya ranar 12 ga watan gobe dan sauraron shaidu a kunshin tuhumar da gwamnatin jaha ta ke yi wa wasu mutane 2.

Gwamnatin jiha ce dai ta gurfanar da mutanen biyu masu suna Abdul’aziz Adamu, mai kayan miyar nan da aka samu gawarwaki guda biyar a gidan sa da ke ƙaramar hukumar Dawakin Kudu, a baya, da kuma Abdullahi Alhassan, waɗanda ake zargi da laifin haɗa baki da garkuwa da mutane da kuma laifin kisan kai.

Lauyan gwamnati Lamido Abba Soron Dinki ne ya roki kotun da ta yi umarnin a karanta kunshin zargin, inda kotun ta amince da rokon.

Ƙunshin zargin ya bayyana cewar mutanen sun haɗa baki sun ɗauke wani mutum mai suna Alhaji Ali Alhassan, sun yi garkuwa da shi, tare kuma da karɓar Kuɗi har Naira Miliyan 15, a hannun iyalinsa da zummar za su sake shi, a karshe an yi zargin sun buga masa wani karfe a kansa har ya riga mu gidan gaskiya.

Yayin da aka karanta wa mutanen ƙunshin zargin da ake yi musu a kotun sun musanta, sai dai mai gabatar da ƙara ya bayyana cewar suna da shaida inda aka kuma umarci shi da ya kawo shaidar akan shari’ar.

Lauyoyin waɗanda ake zargi sun roki kotun da ta yi umarnin a basu kundin bincike, inda kotun ta amince da rokon.

Bayan fitowa daga kotun wakilinmu Yusuf Nadabo Ismail ya zanta da lauyan gwamnati Lamido Abba Soron Dinki Wanda ya bayyana cewar za su gabatar da shaida akan shari’ar.

Da yake nasa jawabin lauyan wanda ake ƙara na farko, Barrister Muhammad Sulaiman Ahmad, ya ce aikin lauya shi ne ya taimaka a gano gaskiyar magana yadda take.

Wakilinmu Yusuf Nadabo Isma’il ya ruwaito cewar, an samu gawarwaki guda biyar a gidan Abdul’aziz Aziz Adamu mai kayan miya, da ke zaune a ƙaramar hukumar Dawakin Kudu, wadanda ake zargi da kashe su sama da shekara daya.

Continue Reading

Trending