Manyan Labarai
Saurari Shirin Baba Suda na jiya Laraba 25/09/2019

A cikin shirin kunji cewa wata mata ta tsinci kanta a gaban Alkali sakamakon zargin ta da kasha wata mata.
Sannan kunji cewa wani tsoho na cigaba da zaman gudun hijira a birnin Kano saboda sharrin maita da akayi masa a kauyensu.
Haka zalika mun baku labara cewa wasu mutane da suke sha’awar zuwa kasar waje an karbe musu makudan kudade da sunan za’a kaisu Ingila.
Ayi Sauraro Lafiya

Manyan Labarai
Gobara ta ƙone tarin shaguna a kasuwar Kurmi da ke Kano – ACFO Saminu Yusuf

Hukumar kashe Gobara ta jihar Kano, ƙarƙashin jagorancin babban daraktan ta Alhaji Sani Anas, ta tabbatar da ƙonewar shaguna guda shida ƙurmus a kasuwar Kurmi Jakara Ƴan Jagwal da ke jihar, sakamakon tashin Gobara.
Jami’in hulɗa da jama’a na hukumar ACFO Saminu Yusuf Abdullahi, shi ne ya bayyana hakan ta cikin wata sanarwa da ya aikowa tashar Dala FM Kano, a ranar Juma’a 18 ga watan Afrilun 2025.
“Sashin mu na karɓar kiraye-kirayen gaggawa ya karɓi kiran gaggawa daga baturen Ƴan Sandan Jakara, wanda ya sanar da tashin gobarar a safiyar Juma’ar nan; ko da jami’an mu suka je wurin sun tarar wutar ta ƙone shaguna 6 ƙurmusu, da kuma wasu shaguna biyar da wani ɓangaren su ya ƙone, “in ji Saminu”.
Kazalika, Hukumar kashe Gobarar ta jihar Kano, ta ce jami’anta sun yi nasarar kashe wutar ba tare da ta tsallaka zuwa Maƙota ba, tare da ƙoƙarin tseratar da Miliyoyin Naira a lokacin.
ACFO Saminu Yusuf, ya kuma ce hukumar za ta yi duk mai yiyuwa domin ganon musabbin tashin gobarar, kasancewar ko a baya ma kimanin sati biyu da suka gabata, sun samu makamancin tashin wutar, ko da dai ya ce babu rasa rai ko kuma jikkata a tashin gobarar.

Hangen Dala
Kofar APC a bude take ga masu shiga – Abdullahi Abbas

Jamiyyar APC a Jihar Kano tace Kofar ta a bude take ga dukkanin masu son shigowa jamiyyar.
Shugaban jamiyyar na Kano Hon Abdullahi Abbas ne ya bayyana hakan yayin wani taron manema labarai.
Abbas yace labarin dake yawo cewa akwai wadanda ke Shirin shigowa jamiyyar, su sani Kofar APCn a bude take tare da maraba ga dukkanin wadanda zasu shigo.
Koda dai Abdullahi Abbas yace shigowa APC ba zai hana tuhuma kan zargin cin hanci da rashawa ba, koma kaucewa hukumar EFCC da ICPC.
A baya bayan nan ne dai aka rinka yada cewa mabiya jamiyyar NNPP kwankwasiyya na Shirin shiga jamiyyar APC tare da madugun ta Sanata Rabiu Musa Kwankwaso.

Hangen Dala
Gwamnoni sun bukaci a kawo karshen matasalar Filato

Ƙungiyar Gwamnonin kasar nan (NGF) ta buƙaci jagororin jihar Plateau su haɗa kan al’ummar jihar mai yawan al’adu da ƙabilu domin dakatar da kashe-kashen mutane da ake yawan samu a jihar.
Shugaban ƙungiyar, wanda kuma shi ne gwamnan jihar Kwara – Abdulrahman Abdulrazaq, ne ya bayyana haka ranar Alhamis lokacin da ya kai ziyarar jaje.
“Muna kira da jagorori da masu faɗa a ji a duka garuruwan jihar da sauran fannoni da su haɗa hannu da gwamnan jihar wajen haɗa kan al’ummar jihar tare da dawo da zaman lafiya mai ɗorewa”, in ji shugaban ƙungiyar ta NGF.
“Ya kamata shugabannin matasan al’umomin jihar su fito su haɗa kai wajen yin Allah wadai da tashin hankalin da ake samu a jihar, muna kira da a riƙa sasanta duka matsalolin da suka taso ta hanyar tattaunawa da lalama tare da girmama juna,” a cewar Abdulrahman Abdulrazaq.
Fiye da mutum 100 ne aka kashe cikin mako biyu da suka gabata, lokacin da wasu mahara suka kai hari a wasu garuruwan ƙananan hukumomin Bokkos da Bassa a jihar.
A ranar Talata ne babban sifeton ƴansandan ƙasar, Kayode Egbetokun ya ziyarci jihar inda ya sha alwashin kamo waɗanda suka ƙaddamar da kashe-kashen, da ya bayyana da na rashin imani, domin hukunta su.

-
Nishadi5 years ago
Ina neman mijin aure – Rayya
-
Labarai5 years ago
Hamisu Breaker ya kai kan sa wajen ‘yan sanda
-
Nishadi6 years ago
Mansura Isah ta yi kaca-kaca da Sadiya Haruna
-
Manyan Labarai5 years ago
KAROTA: An baiwa Baffa Babba wa’adin kwanaki bakwai
-
Labarai5 years ago
Auren dan Panshekara da ba Amurkiya ya samu cikas
-
Lafiya3 years ago
Rahoto: An gano wani gida da ake gini da takardun Kur’ani da Alluna
-
Manyan Labarai5 years ago
Sabuwar damfarar da ta fito a Kano
-
Nishadi5 years ago
An gano daliban da Adam Zango ya dauki nauyin karatun su