Connect with us

Wasanni

Anyi kunnen doki tsakanin Nigeria da Brazil

Published

on

Nijeriya da Brazil sun fara hamayya ne a tsakanin juna tun a gasar Olympic na shekarar 1996 wanda aka gudanar a birnin Atalanta na kasar Amurka wanda Nijeriya ta doke Brazil da ci 4-3.

Kungiyar Kwallon kafa ta Nijeriya ta yi kunnen doki 1-1 da takwararta takasar Brazil a wani wasan sada zumunci da aka fafata a babban filin wasa na kasar Singapore.

Dan wasan gaban Nijeirsa Aribo wanda ke taka leda a Glasgow Rangers ta kasar Scotland shine ya fara zura kwallo a ragar Brazil a cikin minti na 35 daga bisani dan wasan Brazil Casemiro ya farke
kwallon da ka.

Sai dai kuma tin farkon take wasan cikin minti 12, dan wasan gaban Brazil Neymar ya fice daga wasa sakamakon dingshi da ya fara wanda a zu kawai sakamakon lafiyar sa ake jira da wurin likitan sa.

Wasan wanda kayatar ga duban magoya baya a fadin duniya yadda suka mayar da hankali kan wasan sabida hamayar dake tsakanin kasashen biyun.

Nijeriya da Brazil sun fara hamayya ne a tsakanin juna tun a gasar Olympic ta shekarar 1996 wanda aka gudanar a birnin Atalanta na kasar Amurka wanda Nijeriya ta doke Brazil da ci 4-3.

Rubutu masu alaka:

Dalilin cafke Sadiya Haruna

Mutum guda na rasa ransa  cikin sakan 40

Amarya ta zama mai jego a wata hudu

Wasanni

Cassilas ya rataye safar hannun sa daga kama kwallo

Published

on

Tsohon dan mai tsaron ragar kungiyar Real Madrid kuma dan kasar Andulusiyya, Iker Casillas ya jingine safar hannun sa ta kamun kwallo daga harkokin tamaula.

Dan wasan mai shekaru 39 wanda ya buga wasanni 725 a Real Madrid tun ya na shekaru 16 wanda ya lashe kofin zakarun kungiyoyin nahiyar Turai guda 3 da kuma gasar La Liga guda 5 a lokacin sa.

Casillas ya kuma tallafawa kasar sa ta lashe gasar cin kofin duniya na shekarar 2010 tare da lashe gasar cin kofin nahiyar Turai na kasa da kasa har sau biyu na shekarar 2008 da kuma 2012.

Casillas ya koma kungiyar Porto a shekarar 2015, amma tun a shekarar 2019 bai kara yin atisaye ba da kungiyar sakamakon ciwon zuciya da yake fama. Sai dai a lokacin da ya farfado ya koma cikin jerin sawun masu horaswa a watan Yuli na shekarar 2019.

Casillas, ya kuma buga wasanni 156 a kungiyar Porto ya kuma lashe gasar Primera Liga sau 2 tare da kofin kasar Portugal guda 1.

Daga shekarar ya kuma bugawa kasar sa wasanni 167 tsakanin shekarar 2000 zuwa da 2016 wanda dan wasa Sergio Ramos ne kawai ya fi shi taka leda a kasar sa.

Continue Reading

Wasanni

Liverpool: Kocin mu zai iya lashe kofi a nan gaba – Alisson

Published

on

Mai tsaron ragar kungiyar Liverpool, Alisson Backer ya ce mai horas da kungiyar Jurgen Klopp ya ce yanzu ya fara samun nasara a kungiyar Liverpool.

Alisson mai shekaru 30 ya ce kungiyar Liverppol yanzu haka kara karfi take yi domin kara samun nasarorin da su ka samu a baya.

Ya ce”Mun lashe kofi da dama, duk abun da ake bukata kocin mu ya san mai yake yi kuma ya na da hazaka ya yarda damu kuma ya na son mu, ba wai a iya wajen atisaye ba ko da yaushe”.

 

Continue Reading

Wasanni

Ba na tunanin daukar babban dan wasa a bana -Klopp

Published

on

Mai horas da Liverpool, Jurgen Klopp ya ce ba ya tunanin daukar manyan ‘yan wasa a kaka mai kamawa.

Kungiyoyi da dama a Firimiya na ta kokarin daukar manyan ‘yan wasa domin tunkarar kakar 2019-2020.

Duk da cewa mai horaswar ya ce a yanzu ya kuduri niyar kara samun nasarori na kai farmaki ba wai ya kare kambun sa ba.

Continue Reading

Trending

error: Content is protected !!
en_USEnglish
en_USEnglish