Connect with us

Wasanni

Kai tsaye: Sharhin wasannin gasar Premier na yau

Published

on

Ku cigaba da bibiya ana sabunta wannan shafi da sabbin bayanai.

01:25pm

Za mu kawo muku sharhin wasa tsakanin West Ham United da Tottenham Hotspur da karfe 1:30 sai wasa na biyu Crystal Palace da Liverpool da karfe 4:00 kai tsaye daga tashar Dala FM ya yin da BBC za su kawo muku sharhin wasan Manchester City da Chelsea da karfe 6:30.Ku kasance da Tijjani Adamu da Abba Haruna Idris, zaku iya bibiyar yadda wasannin ke gudana kai tsaye ta shafin mu na Facebook a Dala FM Kano ko t adireshin mu na internet a www.dalafmkano.com

Continue Reading

Labarai

Dan wasan Kano Pillars ya chanja sheka

Published

on

Tsohon dan wasan kwallon kafa ta Kano Pillars wato Gambo Muhammad, wanda ya can ja sheka zuwa kungiyar kwallon kafa ta Katsina United, ya bayyana cewa ya koma kungiyar da kafar dama.

Gambo Muhammad din yace daga komawar sa kungiyar ta Katsina United ya zira kwallaye biyar a raga sannan ya kuma taimaka an zura kwallo uku a raga.

Don haka ya sha alwashin cewa a kakar wasa ta bana zai baiwa mara da kunya, domin yadda ya saba zura kwallaye a raga to a bana ma ba fashi.

Gambo Muhammad ya bayyana hakan ne a wata ganawar sa da wakilin mu Abubakar sabo a gidan sa dake unguwar Sani mai Nagge dake karamar hukumar Gwale.

Yayin da kungiyar sa ta Katsina United suka zo nan Kano Dan buga gasar cin kofin Rabi’u Sharif Ahlan.

Ya kuma baiwa magoya bayan sa hakuri, bisa canjin kungiya da ya samu a kakar wasa ta bana, amma yana mai tabbatar musu da cewa, babu shakka, zai taka rawa mai kyau a kakar wasa ta bana yadda za su yi farin ciki mai yawa.

Daga karshe Gambo Muhammad ya yi fatan daukar matsayin dan wasan da yafi kowanne dan wasa jefa kwallo a raga a kakar wasan bana.

Continue Reading

Wasanni

Anyi kunnen doki tsakanin Nigeria da Brazil

Published

on

Nijeriya da Brazil sun fara hamayya ne a tsakanin juna tun a gasar Olympic na shekarar 1996 wanda aka gudanar a birnin Atalanta na kasar Amurka wanda Nijeriya ta doke Brazil da ci 4-3.

Kungiyar Kwallon kafa ta Nijeriya ta yi kunnen doki 1-1 da takwararta takasar Brazil a wani wasan sada zumunci da aka fafata a babban filin wasa na kasar Singapore.

Dan wasan gaban Nijeirsa Aribo wanda ke taka leda a Glasgow Rangers ta kasar Scotland shine ya fara zura kwallo a ragar Brazil a cikin minti na 35 daga bisani dan wasan Brazil Casemiro ya farke
kwallon da ka.

Sai dai kuma tin farkon take wasan cikin minti 12, dan wasan gaban Brazil Neymar ya fice daga wasa sakamakon dingshi da ya fara wanda a zu kawai sakamakon lafiyar sa ake jira da wurin likitan sa.

Wasan wanda kayatar ga duban magoya baya a fadin duniya yadda suka mayar da hankali kan wasan sabida hamayar dake tsakanin kasashen biyun.

Nijeriya da Brazil sun fara hamayya ne a tsakanin juna tun a gasar Olympic ta shekarar 1996 wanda aka gudanar a birnin Atalanta na kasar Amurka wanda Nijeriya ta doke Brazil da ci 4-3.

Rubutu masu alaka:

Dalilin cafke Sadiya Haruna

Mutum guda na rasa ransa  cikin sakan 40

Amarya ta zama mai jego a wata hudu

Continue Reading

Trending

en_USEnglish
en_USEnglish