Connect with us

Wasanni

Magoya bayan Pillars su zama masu da’a yayin kallon Wasa -Jide

Published

on

Shugaban kungiyar magoya bayan kwallon kafa ta Kano Bashir Pillars, Mu’azu Jide, ya gargadi magoya kungiyar da su kasance masu biyayya da zaman lafiya a yayin karawar da Kano Pillars za
ta yi da abokiyar hamayyarta ta Katsina United.

Bashir Mu’azu Jide ya tabbatar da hakan ne, a yayin wata tattaunawa da Dala Fm ta yi da shi a yau dinnan.

Ko ya ka ke ganin karawar da za a yi da Kano Pillars a yau dinnan, ka na da wata shawara ne ga magoya bayan ku?
Sai ya ce “Kirana ga magoya baxan Kano Pillars shi ne da su kasance masu da’a da biyayya sakamakon hayaniya sam bai dace ba a tsaknin juna, domin ko a zaman da muka yi tsakanin Kano Pillars da Katsina United a watan Nuwambar da ta gabata mun tattauna a tsakanin juna
mun yarda cewa Kano da Katsina abu daya ne sabida da  haka rigama ta zama tarihi a yanzu. Wannan ya nuna cewa Kano da Katsina mun zama daya tun da harma mun kara zama na biyu a tsakanin juna“. Inji Bashir Mu’azu Jide.

Ko magoya bayan Pillars nawa ne suka tafi kallo a yanzu haka?

Ya kuma ce “Aaa ai magoya bayan Pillars sun fi mutane  dubu suka tafi kallon wasan yanzu haka, ko ni  mutanen da suka tafi a gabana a tashar Kofar Ruwa sun fi motoci (17)”.

Shugaban magoya bayan Kano Pillars, Bashir Mu’azu Jide, ya kuma yi fatan samun nasara ga kungiyar ta Kano Pillars a wasan.

Wasanni

Cassilas ya rataye safar hannun sa daga kama kwallo

Published

on

Tsohon dan mai tsaron ragar kungiyar Real Madrid kuma dan kasar Andulusiyya, Iker Casillas ya jingine safar hannun sa ta kamun kwallo daga harkokin tamaula.

Dan wasan mai shekaru 39 wanda ya buga wasanni 725 a Real Madrid tun ya na shekaru 16 wanda ya lashe kofin zakarun kungiyoyin nahiyar Turai guda 3 da kuma gasar La Liga guda 5 a lokacin sa.

Casillas ya kuma tallafawa kasar sa ta lashe gasar cin kofin duniya na shekarar 2010 tare da lashe gasar cin kofin nahiyar Turai na kasa da kasa har sau biyu na shekarar 2008 da kuma 2012.

Casillas ya koma kungiyar Porto a shekarar 2015, amma tun a shekarar 2019 bai kara yin atisaye ba da kungiyar sakamakon ciwon zuciya da yake fama. Sai dai a lokacin da ya farfado ya koma cikin jerin sawun masu horaswa a watan Yuli na shekarar 2019.

Casillas, ya kuma buga wasanni 156 a kungiyar Porto ya kuma lashe gasar Primera Liga sau 2 tare da kofin kasar Portugal guda 1.

Daga shekarar ya kuma bugawa kasar sa wasanni 167 tsakanin shekarar 2000 zuwa da 2016 wanda dan wasa Sergio Ramos ne kawai ya fi shi taka leda a kasar sa.

Continue Reading

Wasanni

Liverpool: Kocin mu zai iya lashe kofi a nan gaba – Alisson

Published

on

Mai tsaron ragar kungiyar Liverpool, Alisson Backer ya ce mai horas da kungiyar Jurgen Klopp ya ce yanzu ya fara samun nasara a kungiyar Liverpool.

Alisson mai shekaru 30 ya ce kungiyar Liverppol yanzu haka kara karfi take yi domin kara samun nasarorin da su ka samu a baya.

Ya ce”Mun lashe kofi da dama, duk abun da ake bukata kocin mu ya san mai yake yi kuma ya na da hazaka ya yarda damu kuma ya na son mu, ba wai a iya wajen atisaye ba ko da yaushe”.

 

Continue Reading

Wasanni

Ba na tunanin daukar babban dan wasa a bana -Klopp

Published

on

Mai horas da Liverpool, Jurgen Klopp ya ce ba ya tunanin daukar manyan ‘yan wasa a kaka mai kamawa.

Kungiyoyi da dama a Firimiya na ta kokarin daukar manyan ‘yan wasa domin tunkarar kakar 2019-2020.

Duk da cewa mai horaswar ya ce a yanzu ya kuduri niyar kara samun nasarori na kai farmaki ba wai ya kare kambun sa ba.

Continue Reading

Trending

error: Content is protected !!
en_USEnglish
en_USEnglish