Connect with us

Nishadi

Ina rokon jama’a su daina kallo na a mafadaciya –Adaman Kamaye

Published

on

Fitacciyar jarumar fina-finan Hausar nan Zahra’u Saleh wadda akafi sani da Adama matar Kamaye acikin wasan kwaikwayon nan na Dadin Kowa ta roki al’umma da suyi mata kyaky-kyawar fahimta su daina yi mata kallon masifaffiya.

Jaruma Adama ta bayyana cewa ita a zahiri ba mafadaciya bace, hasalima duk inda zaman lafiya da hadin kai yake to a nan take, amma sai dai jama’a suna yi mata kallon mafadaciya sakamakon rawar da take takawa a film din Dadin Kowa na fitowa mafadaciya.

Cikin wata tattaunawa da gidan Rediyon Dala yayi da jarumar a yammacin jiya Laraba ta bayyana cewa ita bata taba yin fada da wani jarumi a masana’antar Kannywood ba, sai dai ma taji labarin ana yin rigima.

Labarai masu alaka:

Kannywood: Kotu ta kori shari’ar Amina Amal

Abinda yasa nayi hijira daga Kano –Adam Zango

Continue Reading

Nishadi

Tsun-tsun soyayyata ya koma kan Lukuman –Rayya

Published

on

Jarumar fina-finan hausar nan Surayya Aminu wadda akafi sani da Rayya ta bayyana cewa a yanzu tsun-tsun soyayyarta ya tashi daga kan Yakubu Kafi Gwamna, da Yawale ya koma kan dan gidan gwamna mai ci wato Lukuman.

Rayya ta bayyana hakan ne ya yin da take zantawa da Dala FM a safiyar litinin da ta gabata, ta ce a yanzu Kafi Gwamna yana gidan gyaran hali, don haka ya barar da soyayyarsa, shi kuwa Yawale dama son maso wani yake.

Biyo bayan cigaban wasan kwaikwayon nan mai nisan zango na “Kwana Casa’in” da tashar Arewa 24 ke hasakakawa ya nuna yadda sabuwar soyayya ta fara kulluwa tsakanin jaruma Rayya ‘yar aikin gidan tsohon gwamna Bawa Mai Kada da kuma dan gwamna mai ci Malam Adamu wato Lukuman.

Idan zaku iya tunawa dai a kwanakin baya ne jaruma Rayya ta karyata rade-radin da ake yadawa na cewa sun fara soyayya ta zahiri da abokin aikinta wato Yawale.

Labarai masu alaka:

Ina neman mijin aure – Rayya

Kanyywood: Anyi bikin jaruma Hafsat Shehu

Jarumi Madagwal na fama da rashin lafiya

Continue Reading

Nishadi

Ina neman mijin aure – Rayya

Published

on

Fitacciyar jarumar fina-finan hausar nan Surayya Aminu wadda aka fi sani da Rayya ta bayyana cewa a kasuwa take tana neman miji domin tayi aure.

Jaruma Rayya ta bayyana cewa a shirye take ga duk wanda yake so da kaunarta tsakani da Allah zai aure ta, kuma shi aure lokaci ne “ina sa ran nayi aure nan bada jimawa ba cikin ikon Allah” a cewar Rayya.

Idan zaku iya tunawa dai a kwanakin baya a wata tattaunawa da Dala FM tayi da abokin aikin Rayya jarumi Yawale ya bayyana cewa a shirye yake kuma zai iya auren Rayyan a zahiri.

Sai dai a wancan lokacin jaruma Rayya ta bayyana wa Dala FM cewa abu biyu ne zai hanata auren Yawale, na farko yana da aure ita kuma bata son kishiya, sannan Yawale bashi da kudi ita kuma mai kudi take so.

Amma daga bisani jaruma Rayya ta sanar da janye wannan kalaman a shafinta na Instagram.

Labarai masu alaka:

Mu muka haifi Kannywood –Inji Kamaye

Nayi mamakin baiwa Fati Washa Gwarzuwar Kannywood –Kamaye

Continue Reading

Nishadi

Mu muka haifi Kannywood –Inji Kamaye

Published

on

Hoton Jarumi Kamaye

Fitaccen jarumin nan Dan’azimi Baba wanda akafi sani da Kamaye ya bayyan cewa sune suka tsungunna suka haifi masana’antar shirya fina-finan Hausa ta Kannywood.

Yayin wata tattaunawa da Kamaye yayi da tashar Dala FM ya bayyana cewa iya tsawon shekarun da masana’antar tayi, sune suka tsugunna suka haife ta, amma rikon sakainar kashin da sukayi mata ya haifar da koma baya a masana’antar.

Sai dai yanzu zamani ya kawo cigaba wajen kayan aiki na zamani a cewar Kamayen.

Wannan dai na zuwa ne a lokacin da manazarta ke kallon masana’antar na fama da tangal-tangal wajen rashin tabbataccen jagoranci.

Labarai masu alaka:

Nayi mamakin baiwa Fati Washa Gwarzuwar Kannywood –Kamaye

Akwai tarbiyya tsan-tsa a masana’antar Kannywood –Khalisa Muhammad

Continue Reading

Trending

en_USEnglish
en_USEnglish