Connect with us

Nishadi

Fadakarwa muke a fina-finan mu -Furodusa

Published

on

Shahararren mai shirya fina-finan Hausar nan Sani Ali Abubakar Indomie ya bayyana cewa wa’azi da fadakarwa sune ayyukan da suke yi a fina-finan Hausa da suke gabatarwa.

Yayin wata zantawa da jarumin yayi da Dala FM kan sabon shirin sa na “Karamin Sani” Indomie ya ce manufar yin fina-finan sa, shi ne don fadakarwa da wayar da kan al’ummar mu, a don haka ya ke maida hankali wajen ganin fina-finan sa sun dace da addinin islama.

Kazalika Indomie ya ce al’umma na nuna gamsuwarsu kan fina-finan da yake yi ba tare da waka ko kida ba, domin dai su dace dai-dai da addini.

Wasu al’umma dai na ganin cewa fina-finan Hausa na wannan zamanin ko kadan sun sha bam-bam da al’ada da addinin malam Bahaushe.

Sai dai wasu na ganin cewa wannan hobbasa da su Sani Ali Abubakar Indomie keyi zai bada gudummuwa matuka wajen kara farfadowa da martabar masana’antar shirya fina-finan Hausa.

Labarai

Kannywood: Ina nan ban mutu ba – SK

Published

on

Jarumi a masana’antar shirya fina-finan Hausa ta Kannywood, Sani Garba (SK), ya ce, labarin da a ke yaɗawa a shafukan sada zumunta na cewar ya mutu labarin ba gaskiya ba ne ba.

Jarumi Sani SK ya bayyana hakan ne a tattaunawar da a ka yi da shi ta hanyar ɗaukar faifan hoton bidiyo, domin tabbatar da ya na nan da rai bai mutu ba.
Sk ya ce,”Idan lokacin mutuwar ya yi dole ne na mutu kamar yadda mutuwar ta ke a kan kowa. Wa su mutane su na yaɗawa cewar, ƴan masana’antar Kannywood sun wofantar da ni wai ba su tallafa min ba, a yanzu haka kungiyar Kannywood ne ke ci gaba da daukar dawainiyar lafiya ta har ganin na samu sauƙi”.

Idan dai ba a manta ba a ƴan kwanakin nan ne a ka rinƙa wallafa cewar SK ya mutu a shafukan sada zumunta, sai kuma gashi daga bisani jarumin ya fito ya ƙaryata hakan da kansa.

Wakilin mu Hassan Mamuda Ya’u ya rawaito cewar Sani SK ya kuma ce, zahirin gaskiya cutar da ta ke damun sa itace Ciwon Siga, saɓanin jita-jitar da a ke yaɗawa, izuwa yanzu kuma yana cigaba da samun sauƙi.

Continue Reading

Labarai

Matasa sun gudanar da bikin cin nama a Kano

Published

on

Kungiyar Teburin mai shayi na unguwar Ja’en a yankin ƙaramar hukumar Gwale, Aminu S Gandu, ta gudanar da bikin cin nama na musamman a yankin.

Taron ya wakana ne a daren Laraba a unguwar Ja’en dake jihar Kano.

Yayin bikin shugaban kungiyar, Aminu S Gandu ya gargaɗi matasa da su kaucewa sanya kan su a cikin halin shaye-shaye, domin rayuwar su ta zamo abar koyi a nan duniya dama ranar gobe alƙiyama.

Ya na mai cewar,”Mu kan shirya bikin cin naman ne a tsakanin mu matasa, domin wayar da kan matasa musamman ma dominn kaucewa faɗawa cikin halin shaye-shaye. Duk shekarar mu kan shirya taron ne, tare da taya juna nishaɗi, bisa yadda matasa ke ba mu haɗin kai a dukkanin lokacin da mu ka shirya taron”.

Wakilin mu Hassan Mamuda Ya’u ya rawaito cewa, a yayin bikin al’adar da suka saba gabatarwa, matasa da dama ne ke halarta, inda bayan kammala jawabai aka kuma shiga fagen cin naman ragon da sukan yanka kamar yadda suka saba, cikin annushuwa da jin daɗi.

Continue Reading

Duniyar Bollywood

Kannywood: Mu kaucewa yin kalaman da ba su dace ba – Ali Nuhu

Published

on

Jarumi kuma mai shirya fim a masana’antar fina-finan Hausa ta Kannywood, Ali Nuhu, ya gargadi ƴan masana’antar da su kaucewa yin amfani da kalaman da ba su dace ba.

Ali Nuhu ya yi kiran ne jim kaɗan bayan fitowa daga cikin shirin Bollywood na gidan rediyon Dala FM Kano, wanda ya mayar da hankali a kan shirin fim din sa mai suna Bana Bakwai, wanda ya gudana a safiyar yau Laraba.

Ya na mai cewa”Matuƙar ƴan masana’antar ta Kannywood za su ƙara tsaftace kalaman na su, babu shakka za a samu gyara masana’antar”.

Ali Nuhu ya kuma ce fim ɗin sa mai suna Bana Bakwai ya zo da sauye-sauye wanda za a iya dangantashi da fina-finan Bollywood na ƙasar Indiya, inda ya ce shirin yafi mayar da hankali ne wajen magance ta’addanci da garkuwa da mutane da a ke fama dashi.

“Shirin Bana Bakwai zai samar da aikin yi ga matasa da dama dake Arewacin Nijeriya, bisa yadda a ka tsarashi”. Inji Ali Nuhu.

Wakilin mu Hassan Mamuda Ya’u ya rawaito cewa, Jarumin kuma mai shirya fim, Ali Nuhu ya ce, cutar Korona bairus ta kawo tasgaro a cikin masana’antar su ta Kannywood, ba dan haka ba da tuni sun kammala shirin.

Continue Reading

Trending

error: Content is protected !!