Connect with us

Manyan Labarai

Mun kama ‘yan shaye-shaye a gidan kallo- NDLEA

Published

on

Gamayyar jami’an tsaro dake yaki da sha da fataucin miyagun Kwayoyi karkashin hukumar (NDLEA) a jihar Kano ta kai sumame wani gidan Kallo tare da kame mutane fiye da (30) da ta ke zargi suna ta’ammali da miyagun kwayoyi.

Shugaban gamayyar jami’an tsaron Ali Ado Kubau, ya bayyana hakan bayan kammala sumamen a daren jiya Laraba.

Kubau, ya kuma ce ‘Alamu na nuni da cewar Matasa na neman mayar da gidajen kallo wani sansanin shaye-shaye, wanda hakan ke takurawa wadanda basa sha”.

Ali Ado Kubau, ya kuma gargadi masu gidajen kallo wajen tabbatar da cewar ba a shigar da kayan maye gidajen kallo.

Wasu cikin wadanda ake zargin sun bayana nadamar su tare da neman afuwar hukumar ta NDLEA.

Wakilinmu Abba Isah Muhammad, ya ruwaito cewa hukumar ta NDLEA ta ce za ta dauki matakin da doka ta tanadar dazarar sun kammala bincike.

Labarai

Rahoto: Mu tuba ga Allah domin fita daga tsanani – Limamin Na’ibawa

Published

on

Limamin masallacin Juma’a na Nana Aisha da ke unguwar Na’ibawa Gabas, Malam Abubakar Jibril ya ce, al’umma su tuba zuwa ga Allah, domin ya musanya tsanani zuwa yanayi na walwala.

Malam Abubakar Jibril, ya bayyana hakan ne ta cikin Huɗubar Juma’a da ya gabatar.

Mu na da cikakken rahoton a muryar da ke ƙasa.

Continue Reading

Labarai

Rahoto: Rashin wadatar zuci ke janyo zalinta a tsakanin al’umma – Limamin CBN Quarters

Published

on

Limamin masallacin Juma’a na Faruq Unguwa Uku CBN Quarters, Dr. Aminu Ismai’l, ya ce, rashin wadatar zuci ke janyo zalunci da cutar wa a tsakanin al’umma.

Dr. Aminu Isma’il, ya bayyana hakan ne, yayin da ya ke yi wa Dala FM ƙarin bayani dangane da Huɗubar Juma’a da ya gabatar.

Domin jin cikakken rahoton saurari wannan.

Continue Reading

Labarai

Rahoto: Mu guji yin ƙarya da yaɗa ta – Limamin Chiranchi

Published

on

Babban limamin masallacin Juma’a na Sheikh Aliyu Harazimi da ke unguwar Chiranchi, a ƙaramar Hukumar Kumbotso, Dr Rabi’u Tijjani Rabi’u, ya ja hankalin al’ummar Musulmi da su guji yin ƙarya da kuma yaɗa ta.

Dr. Rabi’u ya bayyana hakan ne, yayin da yake ƙarin haske dangane da abin da huɗubar sa ta ƙunsa.

Wakilin mu na ƴan Zazu, Abba Isah Muhammad na da cikakken rahoton.

Continue Reading

Trending

error: Content is protected !!