Connect with us

Labarai

Maganin cutar Lassa da abun da yake kawo ta

Published

on

Shugaban Kungiyar jami’an lafiya a jihar Kano, Salman Adamu, ya shawarci al’umma da su kara kulawa da muhallisu domin kaucewa kamuwa da cutar Lassa.

Sulaiman Adamu, ya bayyana hakan ne jim kadan bayan kammala shirin Wannan Rayuwa na Gidan Rediyon Dala a ranar Alhamis, yayin tattaunawa a kan cutar ta Lassa wanda a cikin makon nan a ka samu rahoton bullarta a asibitin koyarwa na Mallam Aminu Kano (AKTH).

Ya na mai cewa “Kulawa da muhallin na mu ya kan taimaka musamman wajen kaucewa kamuwa da cutar ta Lassa da a ke fama da ita a wannan lokaci. A kan kamu da cutar Lassa ne ta hanyar yawun Beraye da kuma karancin tsaftar muhalli da a kan samu wasu mutanen na yi”. Inji Sulaiman Adamu.

Ko a cikin makonnan sai da gwamnatin jihar Kano ta tabbatar da bular cutar zazzabin Lassa a jihar Kano, amma ta ce ta na kokarin dakile cutar tare da hana ganin ta yadu a fadin jihar baki daya.

Kwamishinan lafiya na jihar, Dr Aminu Ibrahim Tsanyawa ne ya tabbatar da hakan a yayin ganawa da manema labarai.

Ya ce” Mun tabbatar da bullar cutar ta Lassa a Kano, kuma wannan cuta an fara samun bullar ta ne a shekarar 1969 a wani kauyen Lassa dake jihar Borno harma ta yi sanadiyar mutuwar jami’an lafiya na asibiti, kuma daga nan ne ma cutar ake kiran ta da suna Lassa. Cutar mai dauke da kwayar cuta ta mai zafin zazzabi mai tsananin gaske wanda ake kira a turance ‘Viral Hemorrhagic Fever’ wato (VHF) a takaice”.

“Kuma cutar an samu bullar ta a wasu sassan jihohin kasar nan guda (8) wadanda suka hadar da Bauchi,Ondo,Edo,Ebonyi,Taraba,Ogun,Pilateau da kuma jihar Kano a yanzu wadanda kaso 20 kawai aka samu a Kano sauran kuma kaso 60. Kuma ina fada mu ku cewa cutar an samu barkewar ta a ranar 20 ga watannan da muke ciki, kuma ma’aikatar lafiya ta jihar Kano ta tura jami’an ta da suke kula da cututtuka na karamar hukumar Tarauni, an kuma tabbatar cewa wasu likitoci 2 da jami’ar kula da lafiya sun kamu da cutar kuma wanda aka gwada kwayar cutar a dakin gwaji na Gaduwa dake Abuja kuma an tabbatar da bullar cutar ta Lassa”.

“A don haka gwamnatin jihar Kano, ta ware cibiyar kula da cutar ta Yar Gaya wanda yanzu haka a bude take, da sauran dukannin wuraren kiwon lafiya domin ganin an kare yaduwar cutar, sannan kuma nan gaba kadan zamu fara wayar da al’umma yadda zasu kare kansu ta hanyar kafafan gidajen rediyo tare da masu rike da masarautun gargajiya da limamai yadda zasu fadakar da al’umma kan cutar, sannan ga kuma lambobin da za a kirawo kai tsaye dazarar an ji wani alamu na zazzafan zazzabi, 08039704476, 08034988560, 08050595019, 08176673447”. Inji Kwamishinan lafiya na jihar Kano, Dr Aminu Ibrahim Tsanyawa

Yanzu haka dai mutane kusan 292 su ke a killace sakamon wadanda sune suka yi mu’amala da masu cutar ta Lassa.

 

 

 

Labarai

Rahoto: Dokar hana shan shisha ta fara aiki gadan-gadan a Kano – Hisba

Published

on

Hukumar Hisba ta jihar Kano ta kai simamen shagunan da ake sayar da Shisha a kan titin Bompai da ke jihar Kano, inda ta samu nasarar kama dillalan Shishar, domin tabbatar da dokar hana sha da siyar da ita.

A zantawar daya daga cikin masu shagunan sayar da Shisha da wakilin mu na ‘yan Zazu, Ibrahim Abdullahi Soron Dinki, ya bayyana cewar, ya yi tunanin dokar hana shan Shisha ta tsaya kan masu wuraren shan Shisha ba masu sayarwa ba.

Mu na da cikakken rahoton a muryar da ke kasa.

Continue Reading

Labarai

Rahoto: Shekaru 10 ina sarrafa Turoso amma ko ciwon kai ban taba yi ba – Mai Turoso

Published

on

Wani magidanci mai sana’ar sarrafa Turoso a yankin Kududdufawa ya ce, sama da shekaru goma ya na aikin sarrafa Turoso, amma ko ciwon kai bai taba yi ba.

Malam Isah Musa Katsinawa mazunin karamar hukumar Ungogo a jihar Kano, ya bayyana hakan ne, a zantawarsa da wakilin mu na ‘yan Zazu, Yusuf Nadabo Isma’il.

Domin jin cikakken rahoton saurari wannan.

Continue Reading

Labarai

Rahoto: Gobara ta lakume ran mutane 3 ciki harda dattijuwa

Published

on

Hukumar bayar da agajin gaggawa ta jihar Kano, ta kai tallafi wani gida da aka samu iftila’in gobara, wanda ta yi sanadiyar rasa mutane Uku  a unguwar Gama A, da ke karamar hukumar Nasarawa.

Wakilin mu na ‘yan zazu, Abba Isah Muhammad, ya rawaito cewar, hukumar karkashin shugabanta Salihu Aliyu Jili, ta kuma kai tallafi gidan iyayen Hanifa, dalibar da aka yi zargin malaminta ya kashe ta.

Domin jin cikakken rahoton saurari wannan.

Continue Reading

Trending