Connect with us

Labarai

An yi wa matasa fintinkau a karatun Kur’ani –Mallam Ahmad Rufa’i

Published

on

Malamin addinin musulunci a jihar Kano, Mallam Ahmad Rufa’i Mai Kasida, ya ce dole ne al’ummar musulmai musamman ma matasa maza sai sun kara bada himma a wajen neman ilimi, domin rayuwar su ta zama abar koyi a nan duniya dama gobe kiyama.

Mallam Ahmad Rufa’i, ya yi kiran ne a yayin saukar karatun Al’kur’ani mai girma da makarantar Madarasatul Ta’alimul Qur’an Islamiyya dake unguwar Ja’en a yankin karamar hukumar Gwale ta gudanar da saukar karshen makon da ya gabata.

Ya na mai cewa” Kara bada himma da neman ilmin yakan taimakawa matasan wajen kaucewa fadawar su cikin wani hali, sakamakon dole sai da ilimi rayuwa ke samun ci gaba”. Inji Mallam Ahmad.

Da yake nasa jawabin shugaban makarantar, Mallam Aliyu Hamza Hassan, cewa ya yi” Makarantar a mafi yawan lokuta takan fuskanci kalubale daga bangaren iyaye, musamman wajen nuna halin ko in kula da iyayen suke nunawa da karatun ya’yansu a makarantar, kuma wajibi iyaye dasu kara bada kulawa da karatun ya’yan nasu ba tare da gajiyawa ba”. Inji Mallam Aliyu.

Suma wasu daga cikin daliban da suka yi saukar karatun Al’kur’anin wanda suka kasance mata goma sha daya namiji daya, sun bayyana farin cikin su dangane da saukar da sukayi, sannan sun ce za su yi amfani da abun da suka samu.

A yayin saukar dai wakilin mu Hassan Mahmuda Ya’u ya rawaito cewa, al’umma da dama ne suka samu damar halarta daga yankin na Ja’en, daga ciki kuwa akwai mai unguwar Ja’en Yamma (A) Mallam Ya’u Musa Wakili.

Ilimi

Mun shirya yin aiki tare da masarautar Gaya – SEDSAC

Published

on

Kungiyar bunkasa ilimi da ci gaban demokradiya ta SEDSAC ta ce masarautar Gaya itace masarauta ta farko da kungiyar za ta yi hadin gwiwa da ita, domin ci gaba da samar da shirye-shirye da ya shafi rayuwar al’umma.

Sanarwar ta fito ne ta hannun daraktan kungiyar, Kwamrade Umar Hamisu Kofar Na’isa, ta na mai cewa, za ta yi hadin gwiwa da dukannin masauratu Biyar na Kano, domin bunkasa rayuwar al’umma tare da samar da ci gaba a kasa.

SEDSAC ta kuma yabawa gwamnan Kano, Dr Abdullahi Umar Ganduje da kuma ma su zaben sarki a Gaya, bisa nada Alhaji Ali Ibrahim Abdulkadir Gaya, a matsayin sabon sarkin Gaya, wanda kuma ya na daya daga cikin jigon iyaye na kungiyar SEDSAC.

Haka zalika SEDSAC ta kuma taya sabon sarkin murnar sarautar da ya samu tare da yi wa marigayi tsohon Sarkin Gaya, Alhaji Ibrahim Abdulkadir Gaya, addu’ar neman gafara a wajen Ubangiji.

Continue Reading

Labarai

Ba ma samun kulawa a wajen Gwamnati – Masu sana’ar Shuke-shuke

Published

on

Kungiyar masu Shuke-shuke ta kasa reshen jihar Kano ta koka dangane da rashin kulawa daga gwamnati wajen siyan tsirrai daga wurin su.

Shugaban kungiyar, Aliyu Shehu Kabara, ya bayyana hakan, yayin taron shekara da suka gudanar a jihar Kano a karshen makon da ya gabata.

Ya na mai cewar, “Yawancin lokuta gwamnati kan tashi masu sana’ar Shuke-shuke ba tare da samar musu da wasu wuraren ba”. Inji Aliyu Shehu Kabara.

A nasa jawabin, wani masani a kan harkokin tsirrai daga Jami’ar Bayero ta Kano, Malam Hassan Usaini, ya ce, “Akwai gudunmawa mai tarin yawa da masu lambuna ke bayarwa, a fannin muhalli da kuma ilimi, wanda suma mata akwai bukatar su shigo cikin harkar domin bayar da gudunmawa”.

Wakilin mu Abba Isah Muhammad ya ruwaito cewar, masu lambunan sun yi fatan gwamnati da sauran hukumomi, za su hada hannu da su, domin samar da ingantaccen muhalli.

Continue Reading

Labarai

Za mu hana shan Shisha a bainar Jama’a – Hukumar yawon bude ido

Published

on

Hukumar yawon bude ido ta jihar Kano ta ce, za ta hana shan Shisha a bainar Jama’a tare da hana kananan yara zuwa Otel da zarar gwamnati ta sanya wa dokar hannu.

Babban Manajan Daraktan hukumar, Yusuf Ibrahim Lajawa ne ya bayyana hakan,  a ganawar sa da gidan radiyon Dala a ranar Litinin.

Ya ce, “Tsofaffin wuraren da ake gudanar da Rini, dama wuraren da ake gudanar da Jima, na daya daga cikin ababen da mu ka sanya, a cikin  kasafin kudin hukumar a Bana”. A cewar Lajawa.

Wakilin mu Nasir Khalid Abubakar ya rawaito cewa, Yusuf Ibrahim Lajawa ya kuma ce, aikin hukumar ta su ya ta’allaka ne kadai wajen janyo ra’ayoyin al’umma, daga ko’ina domin zuwa jihar Kano domin yawon bude ido.

Continue Reading

Trending

error: Content is protected !!