Connect with us

Labarai

Dogaro dakai zai magance talauci a cikin gida –Dr Zahra’u Muhammad

Published

on

Kwamishiniyar mata da walwala ta jihar Kano, Dakta Zahra’u Muhammad Umar, ta yi kira ga al’umma musamman ma mata dasu kara riko da sana’o in dogaro da kai domin kaucewa zaman kashe wando a cikin al’umma.

Dakta Zahra’u Muhammad Umar na wannan bayanin ne ta bakin, Hadiza Aliyu Kabara, wadda ta wakilce ta a yayin taron da Gidauniyar Light House ta shirya, na ya ye matan da suka koyi sana’a daban-daban da kuma tallafa musu da jari, wanda ya gudana a makarantar koyon harshen Larabci ta S.A.S a karshen makon da ya gabata.

Ta ce” Riko da sana’o in dogaro da kai yakan taimakawa mutane ta fannin zama ba tare da sana’a ba ga matasan musamman ma mata”.

A nasa jawabin shugaban Gidauniyar ta Light house, Kwamred Ilyasu Sulaiman Dawakin Tofa, ya ce”Burin kungiyar ta samarwa da matasa aiki tare da rage zaman kasha wando a cikin al’umma”.

Wasu daga cikin matan da sukaci gajiya a yayin taron sun ce za su yi amfani da ilimin da suka samu da kuma jari wajen juyawa domin su tsaya da kafar su.

Wakiliyar mu A’isha Ibrahim Abdul ta rawaito cewa, kimanin mata sama da dari hudu ne gidauniyar ta koyawa sana’o in, wanda suka hadar da zanen gado, rigunan abaya da kuma kwalliya, inda kuma a ranar Lahadin da ta gabata gidauniyar ta yaye su, daga ciki kuwa akwai marayu sama da hamsin.

Ilimi

Mun shirya yin aiki tare da masarautar Gaya – SEDSAC

Published

on

Kungiyar bunkasa ilimi da ci gaban demokradiya ta SEDSAC ta ce masarautar Gaya itace masarauta ta farko da kungiyar za ta yi hadin gwiwa da ita, domin ci gaba da samar da shirye-shirye da ya shafi rayuwar al’umma.

Sanarwar ta fito ne ta hannun daraktan kungiyar, Kwamrade Umar Hamisu Kofar Na’isa, ta na mai cewa, za ta yi hadin gwiwa da dukannin masauratu Biyar na Kano, domin bunkasa rayuwar al’umma tare da samar da ci gaba a kasa.

SEDSAC ta kuma yabawa gwamnan Kano, Dr Abdullahi Umar Ganduje da kuma ma su zaben sarki a Gaya, bisa nada Alhaji Ali Ibrahim Abdulkadir Gaya, a matsayin sabon sarkin Gaya, wanda kuma ya na daya daga cikin jigon iyaye na kungiyar SEDSAC.

Haka zalika SEDSAC ta kuma taya sabon sarkin murnar sarautar da ya samu tare da yi wa marigayi tsohon Sarkin Gaya, Alhaji Ibrahim Abdulkadir Gaya, addu’ar neman gafara a wajen Ubangiji.

Continue Reading

Labarai

Ba ma samun kulawa a wajen Gwamnati – Masu sana’ar Shuke-shuke

Published

on

Kungiyar masu Shuke-shuke ta kasa reshen jihar Kano ta koka dangane da rashin kulawa daga gwamnati wajen siyan tsirrai daga wurin su.

Shugaban kungiyar, Aliyu Shehu Kabara, ya bayyana hakan, yayin taron shekara da suka gudanar a jihar Kano a karshen makon da ya gabata.

Ya na mai cewar, “Yawancin lokuta gwamnati kan tashi masu sana’ar Shuke-shuke ba tare da samar musu da wasu wuraren ba”. Inji Aliyu Shehu Kabara.

A nasa jawabin, wani masani a kan harkokin tsirrai daga Jami’ar Bayero ta Kano, Malam Hassan Usaini, ya ce, “Akwai gudunmawa mai tarin yawa da masu lambuna ke bayarwa, a fannin muhalli da kuma ilimi, wanda suma mata akwai bukatar su shigo cikin harkar domin bayar da gudunmawa”.

Wakilin mu Abba Isah Muhammad ya ruwaito cewar, masu lambunan sun yi fatan gwamnati da sauran hukumomi, za su hada hannu da su, domin samar da ingantaccen muhalli.

Continue Reading

Labarai

Za mu hana shan Shisha a bainar Jama’a – Hukumar yawon bude ido

Published

on

Hukumar yawon bude ido ta jihar Kano ta ce, za ta hana shan Shisha a bainar Jama’a tare da hana kananan yara zuwa Otel da zarar gwamnati ta sanya wa dokar hannu.

Babban Manajan Daraktan hukumar, Yusuf Ibrahim Lajawa ne ya bayyana hakan,  a ganawar sa da gidan radiyon Dala a ranar Litinin.

Ya ce, “Tsofaffin wuraren da ake gudanar da Rini, dama wuraren da ake gudanar da Jima, na daya daga cikin ababen da mu ka sanya, a cikin  kasafin kudin hukumar a Bana”. A cewar Lajawa.

Wakilin mu Nasir Khalid Abubakar ya rawaito cewa, Yusuf Ibrahim Lajawa ya kuma ce, aikin hukumar ta su ya ta’allaka ne kadai wajen janyo ra’ayoyin al’umma, daga ko’ina domin zuwa jihar Kano domin yawon bude ido.

Continue Reading

Trending

error: Content is protected !!