Connect with us

Manyan Labarai

Masu cin Beraye sun bayyana a Kano

Published

on

A yayin da masana lafiya ke gargadin mu’amala da Beraye domin gujewa kamuwa da cutar Lassa sakamakon cutar an gano cewa Beraye ne ke hadda sa cutar ga bil Adama.

Sai gas hi wasu mutane da suka mayar da Beraye naman cimakar su a cikin abincin sun a yau da kulum.

Mutanen wanda suka ya da zango a cikin garin Rogo dake karamar hukumar sun ce cikin Berayen da suke ci babu wanda ya taba samun wata matsala ga lafiyar su, duk da cewa cutar Lassa ta samo asali ne ga Beraye.

Michel Joseph da shi da iyalai da ‘yan uwansa wanda suka sami masauki a cikin garin Rogo ya ce” Mu masu kama Beraye ne kuma ba mu san irin Berayen ba kuma bamu samu matsala da sub a, domin kuwa abincin mu ne Bera muna kama su kuma muna cin su, duk cikin mu babu wani wanda ya samu wata cuta gamunan garau muna zaune har kwado muna ci”.

Likitoci suna cewa a jikin Beraye a ke samun cutar Lassa, ba kwajin tsoron cutar Lassa?

“Berayen da a ka ce suna kawo cutar mu a yankin mu babu wani Bera mai cutar, mu da muke ci har yanzu ba mu samu wata matsalaba, mu (27) wanda muke cin Berayen mu yi miya da su mu zuba a abincin mu har yanzu babu wata matsala da muka fuskanta”.

Yanzu in na kawo muku Bera za ku siya?

“Ba ma siya muna amfani da tarkon mu kama, ko ka kawo ma nan aka ba za mu siya ba, wanda muke kamawa shi muke ci muke kaoshi”.

Wane irin tarko ku ke amfani ku kama Berayen?

“Mun hada tarko mu saka a kan hanyar Berayen ba tare da wata matsala ba, ka gam un zo garin Rogo mun zauna mun samu abun da muke bukata yanzu muna saka tarko sai ka gam un kama Beraye da yaw aba tare da wata matsala ba, kuma mu gyara mu ci ko ciwon kai ba ma yi”.

A na baku hadin kai yayin kama Berayen?

“ Eh bamu da wata matsala domin mahukunta sun san da zaman mu kuma in zamu shiga cikin gona mu kama zamu shiga ba tare da wata matsala ba, in kuwa k ace mu fita daga gonar Raken ka sai mu fita tunda har yau ba wanda ya ce mun yi masa satar rake a cikin gonar sa”. Inji Michel Joseph a cikin tattaunawar mu da shi”.

Ga cikaken hirara tamu da shi.

Duk da annobar cutar Lassa sai gashi wasu mutane da sun bayyana a Kano suna shan dabgen Beraye.

Ilimi

Mun shirya yin aiki tare da masarautar Gaya – SEDSAC

Published

on

Kungiyar bunkasa ilimi da ci gaban demokradiya ta SEDSAC ta ce masarautar Gaya itace masarauta ta farko da kungiyar za ta yi hadin gwiwa da ita, domin ci gaba da samar da shirye-shirye da ya shafi rayuwar al’umma.

Sanarwar ta fito ne ta hannun daraktan kungiyar, Kwamrade Umar Hamisu Kofar Na’isa, ta na mai cewa, za ta yi hadin gwiwa da dukannin masauratu Biyar na Kano, domin bunkasa rayuwar al’umma tare da samar da ci gaba a kasa.

SEDSAC ta kuma yabawa gwamnan Kano, Dr Abdullahi Umar Ganduje da kuma ma su zaben sarki a Gaya, bisa nada Alhaji Ali Ibrahim Abdulkadir Gaya, a matsayin sabon sarkin Gaya, wanda kuma ya na daya daga cikin jigon iyaye na kungiyar SEDSAC.

Haka zalika SEDSAC ta kuma taya sabon sarkin murnar sarautar da ya samu tare da yi wa marigayi tsohon Sarkin Gaya, Alhaji Ibrahim Abdulkadir Gaya, addu’ar neman gafara a wajen Ubangiji.

Continue Reading

Labarai

Ba ma samun kulawa a wajen Gwamnati – Masu sana’ar Shuke-shuke

Published

on

Kungiyar masu Shuke-shuke ta kasa reshen jihar Kano ta koka dangane da rashin kulawa daga gwamnati wajen siyan tsirrai daga wurin su.

Shugaban kungiyar, Aliyu Shehu Kabara, ya bayyana hakan, yayin taron shekara da suka gudanar a jihar Kano a karshen makon da ya gabata.

Ya na mai cewar, “Yawancin lokuta gwamnati kan tashi masu sana’ar Shuke-shuke ba tare da samar musu da wasu wuraren ba”. Inji Aliyu Shehu Kabara.

A nasa jawabin, wani masani a kan harkokin tsirrai daga Jami’ar Bayero ta Kano, Malam Hassan Usaini, ya ce, “Akwai gudunmawa mai tarin yawa da masu lambuna ke bayarwa, a fannin muhalli da kuma ilimi, wanda suma mata akwai bukatar su shigo cikin harkar domin bayar da gudunmawa”.

Wakilin mu Abba Isah Muhammad ya ruwaito cewar, masu lambunan sun yi fatan gwamnati da sauran hukumomi, za su hada hannu da su, domin samar da ingantaccen muhalli.

Continue Reading

Labarai

Za mu hana shan Shisha a bainar Jama’a – Hukumar yawon bude ido

Published

on

Hukumar yawon bude ido ta jihar Kano ta ce, za ta hana shan Shisha a bainar Jama’a tare da hana kananan yara zuwa Otel da zarar gwamnati ta sanya wa dokar hannu.

Babban Manajan Daraktan hukumar, Yusuf Ibrahim Lajawa ne ya bayyana hakan,  a ganawar sa da gidan radiyon Dala a ranar Litinin.

Ya ce, “Tsofaffin wuraren da ake gudanar da Rini, dama wuraren da ake gudanar da Jima, na daya daga cikin ababen da mu ka sanya, a cikin  kasafin kudin hukumar a Bana”. A cewar Lajawa.

Wakilin mu Nasir Khalid Abubakar ya rawaito cewa, Yusuf Ibrahim Lajawa ya kuma ce, aikin hukumar ta su ya ta’allaka ne kadai wajen janyo ra’ayoyin al’umma, daga ko’ina domin zuwa jihar Kano domin yawon bude ido.

Continue Reading

Trending

error: Content is protected !!