Connect with us

Wasanni

Jaddawalin zagaye na biyu na gasar kofin M.A Lawal

Published

on

Wasan zagaye na biyu na gasar cin kofin Barrista M.A Lawal.

Za a yi wasan ne a ranar Laraba 8/3/2020

1 White Hart vs FC Sheshe

2 Mariri United vs Golden S Fagge

3 Kano Lion vs Yar Maggi Mandawari

4 Tarauni United vs Dakata United

5 Sky Limit vs Tarauni Babies

6 Samba Limawa vs High Landers

7 FC Man Blue vs Golden Gate

8 Zage United vs Hatoro United

9 Daurawa United vs All Star U/Uku

10 Dakata Emirate vs FC Sharlam

11 New Generation vs Esteem Boys

12 Etihad FC vs KMC Feeders

13 Dorayi Warriors vs Jogana United

14 FC Bawo vs C.P Boys

15 Fancy Fagge vs Karkasara United

16 Golden Star Sharada vs Brilliant Boys ko Civil Defence FC.

Labarai

Mai horas da kungiyar Southampton ya kara rattaba sabon kwantiragi

Published

on

Mai horas da kungiyar kwallon kafa ta Southampton, Ralph Hasenhuttl ya kara rattaba sabon kwantiragi a kungiyar ta Southampton.

Ralph Hasenhuttl mai shekaru 52 dan kasar Austrian ya karbi kungiyar ne tun a watan Disamba na shekarar 2018 wanda ya tsallake da su fadawa zuwa ajin ‘yan dagaji.

Mai horaswar ya dai rattaba sabon kwantiragi na tsawon shekaru hudu wanda zai ci gaba da zama a kungiyar har zuwa shekarar 2024.

Southampton dai ita ce kungiya da ta taba kwasar kashin ta a hannu har tsawon kwallaye tara da a ka zura mata a raga a gasar wanda Leicester City ta lallasa ta.

Continue Reading

Labarai

Naji dadi matuka da za a dawo gasar Premier -Mai horas da Liverpool

Published

on

Mai horas da kungiyar kwallon kafa ta Liverpool Jurgen Klopp ya ce ya ji dadi sakamakon dawowa da za a yi gasar Firimiya a ranar 17 ga watan Yunin nan.

Klopp ya tabbatar da hakan ne ayayin tattaunawar sa da gidan rediyon BBC ya na mai cewa ya yi kewar wasan sakamakon hutun da a ka tafi na dakatar da wasan a ranar 13 ga watan Maris.

Ya ce” Na yi rashi sosai wannan abun mamaki ne domin kuwa abu ne mai amfani a rayuwa ta kuma wanda nake so, fatan kawai mutane za su dafawa abun domin ganin an kai ga gaci”. A cewar Klopp.

Liverpool ita ce dai a kan gaba da maki 25 wanda idan ta lashe gasar wannan dai shi ne karo na farko tun cikin shekaru 30 ba ta lashe gasar ba.

Continue Reading

Labarai

Barcelona za ta yi karon batta da Real Mallorca

Published

on

Kungiyar kwallon kafa ta Barcelona za ta tunkari takwararta ta Real Mallorca a wasan farko da za ta yi tun bayan tafiya hutun Coronavirus.

Yanzu haka dai kungiyar za ta fafata ne a ranar 13 ga watan Yunin nan a yayin da kungiyar Sevilla za ta kece raini da Real Betis da karfe 9 na dare dukannin su a cikin ranar.

Bacerlona ita ce jag aba a teburin Laliga inda ta baiwa Real Madrid maki biyu a Tsakani bayan wasannin mako na 27 da su ka fafata. Sai Eibar za ta kara da Real Madrin a ranar 14 ga watan nan da mu ke ciki.

Continue Reading

Trending

error: Content is protected !!
en_USEnglish
en_USEnglish