Connect with us

Wasanni

Gasar cin kofin Musa Dan Mama 2020 Wudil

Published

on

Za a fara wasannin kamar haka.

Wasan farko  20/4/2020.

Kwallon Bakan Dala 88.5 Whatsapp Group

VS

  1. Porto Wudil

A filin wasa na Wudil Utd

Karfe 4:30pm

Ranar 21/4/2020

Sheva Academic

VS

Golden Ster Sumail

Filin wasa na Kust Wudil

Karfe 4:30pm

Ranar 22/4/2020

Red Fire Wudil

VS

Valencia Wudil

Filin wasa na Techanical wudil

Karfe 4:30pm

Ranar 23/4/2020

AS Roma Wudil.

VS

Man City Wudil

Fili na Technical Wudil

Karfe 4:30pm

Ranar 28/4/2020

 

Fansy Utd Wudil

VS

Wudil Pillars

Fili na Wudil Utd

Karfe 4:30pm

Ranar 29/4/2020

Civil defences Wudil

VS

Everton Wudil

Fili na Wudil Utd

Karfe 4:30pm

Ranar 4/5/2020

FC Magic Wudil

VS

Liverpool Wudil

Fili na Wudil Utd

Karfe 4:30pm

Shugaban gasar Musam Dan Mama Wudil ya tabbatar da cewa akwai manyan baki da za su kasance a gasar Tijjani Adamu da Abba Haruna Idris na rediyon Dala.

Wasanni

COVID 19: SWAN ta dakatar da taron ta a Kano

Published

on

Kungiyar marubuta labarin wasanni ta kasa reshen jihar Kano, SWAN ta dakatar da taron ganawa da dake yi da masu ruwa da tsaki a cikin kungiyar sakamakon cutar Coronavirus.

Shugabann kungiyar, Musbahu Bala Chediya ‘Yan Gurasa, ne ya tabbatar da hakan cewa ba za su samu damar zaman kungiyar wanda za su gudanar a ranar 26 ga watam Maris sakamakon kaucewa cutar ta Covid-19.

Ya kuma bukaci dukannin mambobin kungiyar da su ci gaba da bada kulawa domin kare lafiyar su, sannan za kuma su sanar da lokacin da za a gudanar da taron a nan gaba bada jimawa ba.

Taron dai wanda kungiyar za ta yi da masu ruwa da tsaki da ‘ya’yan ta ciki hada maganar shaidar kati na kungiyar wato ID Card da maganar kalandar kungiyar da kuma wasannin kasa na shekarar 2020 da dai sauran su. Wanda dole ya sanya kungiyar SWAN ta dage taron na ta na wannan lokacin sakamakon cutar Coronavirus da ake ta kokarin magance faruwar ta a fadin jihar Kano baki daya.

 

Continue Reading

Wasanni

Ighalo: Daga aro zai zama dan wasan din din din

Published

on

Kungiyar kwallon kafa ta Manchester United ta tabbatar da cewa za ta sayi dan wasan gabanta Odion Ighalo na kwantiragin din din din daga kungiyar sa.

Manchester United wadda ta taya dan wasan a kan kudi fam miliyan 15 domin ganin an siyar mata da dan wasan gaban wanda yake a kungiyar a matsayin aro.

Mai horas da kungiyar ta Manchester United, Ole Gunnar Solskjaer, ya dai baiwa Odhion Ighalo, dama domin ganin ya amince da tayin da aka yi masa na ganin ko zai zauna a kungiyar ko kuwa.

Ighalo dai ya zo kungiyar ne a matsayin aro daga kungiyar sa ta Shanghai Greenland Shenhua dake kasar China.

 

 

 

Continue Reading

Wasanni

Covid-19: An dakatar da gasar kofin M.A Lawal a Kano

Published

on

Shugabanin masu gudanar da wasa na gasar cin kofin Barrisat M.A Lawal sun dakatar da gasar sakamakon cutar coronavirus.

Sanarwar mai kunshe da sa hannun sakataren tsare-tsaren gasar Abdullahi Sharada, ya tabbatar da hakan cewa sakamakon dakatar da kowane wasa a Nijeriya su ma suka dauki wannan matakin gudun kada a samu yaduwar cutar.

Continue Reading

Trending

error: Content is protected !!
en_USEnglish
en_USEnglish