Connect with us

Labarai

Gwamnatin Kano ta gurfanar da likita a kotu

Published

on

Gwamnatin jihar Kano ta gurfanar da wani likita a gaban mai shari’a, Usman Na Abba a babbar kotun jihar mai lamba 8.

Likitan mai suna, Dr Ayinde A A, a na dai zargin sa da lefin kisan kai ta hanyar ganganci a wajen aiki, laifin da ya saba da sashi na 222 (7) na kundin Penal code.

Kunshin zargin ya bayyana cewar Dr Ayinde yayiwa wani mutum mai suna, Lawan Ado, tiyata a kafa lamarin da ya kai har ya datse kafar mutumin nan take kuma ya rasu.

Sai dai likitan wanda yake aiki a wani asibiti mai zaman kansa ya musanta zargin.

Ya kuma roki kotun da ta ba shi dama domin tuntubar iyalan marigayin ko a yi sulhu.

Sai dai lauyan gwamnati, Lamido Soron Dinki, ya bayyanawa kotun cewar shi an turo shi ne ya tuhumi mutumin a gaban kotu, domin haka shi babu ruwan sa da batun sulhu.

Wakilin mu, Yusuf Nadabo Ismail, ya rawaito cewar an sanya litinin mai zuwa domin jin ra’ayin kotun dangane da rokon beli.

Labarai

Mai horas da kungiyar Southampton ya kara rattaba sabon kwantiragi

Published

on

Mai horas da kungiyar kwallon kafa ta Southampton, Ralph Hasenhuttl ya kara rattaba sabon kwantiragi a kungiyar ta Southampton.

Ralph Hasenhuttl mai shekaru 52 dan kasar Austrian ya karbi kungiyar ne tun a watan Disamba na shekarar 2018 wanda ya tsallake da su fadawa zuwa ajin ‘yan dagaji.

Mai horaswar ya dai rattaba sabon kwantiragi na tsawon shekaru hudu wanda zai ci gaba da zama a kungiyar har zuwa shekarar 2024.

Southampton dai ita ce kungiya da ta taba kwasar kashin ta a hannu har tsawon kwallaye tara da a ka zura mata a raga a gasar wanda Leicester City ta lallasa ta.

Continue Reading

Labarai

Naji dadi matuka da za a dawo gasar Premier -Mai horas da Liverpool

Published

on

Mai horas da kungiyar kwallon kafa ta Liverpool Jurgen Klopp ya ce ya ji dadi sakamakon dawowa da za a yi gasar Firimiya a ranar 17 ga watan Yunin nan.

Klopp ya tabbatar da hakan ne ayayin tattaunawar sa da gidan rediyon BBC ya na mai cewa ya yi kewar wasan sakamakon hutun da a ka tafi na dakatar da wasan a ranar 13 ga watan Maris.

Ya ce” Na yi rashi sosai wannan abun mamaki ne domin kuwa abu ne mai amfani a rayuwa ta kuma wanda nake so, fatan kawai mutane za su dafawa abun domin ganin an kai ga gaci”. A cewar Klopp.

Liverpool ita ce dai a kan gaba da maki 25 wanda idan ta lashe gasar wannan dai shi ne karo na farko tun cikin shekaru 30 ba ta lashe gasar ba.

Continue Reading

Labarai

Covid-19: Za a ci kasuwanni a ranar da a ka bude Kano

Published

on

Gwamnatin jihar Kano ta bada dama ga ‘yan kasuwar jihar Kano da su bude dukannin kasuwannin su a ranakun da a ka bude jihar Kano.

Kwamishin yada labarai na jihar, Kwamrade Muhammad Garba ne ya tabbatar da hakan cewa tuni gwamnati ta baiwa ‘yan kasuwar dama bayan ganawa da su ka yi da gwamnati.

‘Yan kasuwar za su bude kasuwannin na su ne tun bayan cikin tsawon kwanaki sama da 50 a rufe sakamakon bullar cutar Corona a jihar Kano.

Da dama dai wasu daga cikin ‘yan kasuwan sun ci kasuwar su a bayan fage musamman ma wasu daga cikin ‘yan kasuwar Kantin Kwari yadda su ka rinka yin kasuwanci irin samfurin tafi da gidan ka.

Continue Reading

Trending

error: Content is protected !!
en_USEnglish
en_USEnglish