Connect with us

Wasanni

Mahaifiyar Kocin Manchester City ta mutu saboda Coronavirus

Published

on

Mahaifiyar mai horas da kungiyar kwallon kafa ta Manchester City, Pep Guardiola ta mutu sakamakon cutar Coronavirus da ta kama ta.

Mahaifiyar ta sa mai suna Dolors Sala Carrio, mai shekaru 82 ta mutu ne a birnin Barcelona bayan fama da cutar da ta yi.

Tuni dai kungiyar Manchester City da sauran kungiyoyi su ka mika sakon ta’aziyar su ga mai horas da Manchester City Pep Guardiola sakamakon rashin mahaifiyar sa da ya yi.

Guardiola mai shekaru 49, a kwanakin baya ya dai bada tallafin gudunmawar Yuro miliyan daya kwatankwacin Fam miliyan dubu dari tara da ashirin domin a yaki cutar Covid-19.

 

Wasanni

Kocin Munich: Ina taya Klopp murnar daukan Thiago

Published

on

Mai horas da kungiyar Bayern Muncih Hansi Flick ya taya Kocin Liverpool, Jurgen Klopp murnar daukan dan wasa Thiago Alcantara.

Tuni dan wasan, Thiago Alcantara ya yi bankwana da kungiyar sa ta Bayern Munich da kuma abokan karawar sa, sakamakon barin kungiyar da zai yi zuwa Liverpool.

Thiago mai shekaru 29, ya cimma yarjejeniya da Liverpool, inda za ta biya kudin sa a kan kudi Fam miliyan 25 kwatankwacin Yuro miliyan 27.5.

Kocin ya ce“Thiago dan wasa ne wanda ya banbanta da sauran ‘yan wasa, ya shafe tsawon shekaru 7 tare da mu, kwararre ne a harkar kwallon kafa, mu dai duk jikin mu ya yi sanyi yau dinnan, saboda ya yi sallama da mu, kawai dai zan yi masa fatan alheri, kuma ina yabawa Jurgen Klopp sakamakon daukan dan wasan da ya yi, mu kuma mun yi rashin dan wasa mai nagarta”. Inji Flick.

Continue Reading

Wasanni

Kasar Sin: Za su fara kallon gasar Firimiya a Talabijin

Published

on

Hukumar gasar Firimiya ta kasar Ingila, ta cimma yarjejeniya da kasar Sin, domin haskaka gasar Firimiya a kasar na kakar 2020 da 2021.

Hukumar ta cimma yarjejeniyar da kamfanin Tencent Sports, bayan da hukumar gasar Firimiya ta kwace kwantiragi na Fam miliyan 564 da talabijin na PPTV a cikin farkon wannan watan.

Masu kallon gasar Firimiya a kasar Sin za su fara kallon wasannin da za a fafata a wannan makon mai zuwa.

Continue Reading

Wasanni

Gareth Bale: Ungulu za ta koma gidan ta na tsamiya

Published

on

A ranar Juma’a mai zuwa ne dan wasan gaban kungiyar Real Madrid, Gareth Bale, zai koma tsohuwar kungiyar sa ta Tottenham Hotspur a matsayin aro.

Bale dan kasar Wales mai shekaru 31, wanda har yanzu a na ci gaba da tattaunawa domin samun masalaha a tsakanin kungiyoyin biyu, domin komawar sa Tottenham.

Har idan a ka kammala tattaunawar dan wasa Bale zai tattaki har zuwa birnin London, domin ya rattaba kwantiragi a tsohuwar kungiyar sa.

A ranar Alhamis ne a ka hangi Bale ya ware kan sa ya na daukar horo shi kadai a kungiyar sa ta Real Madrid.

A shekarar 2007 ne dan wasa Bale ya koma Tottenham daga kungiyar Southampton, daga nan kuma ya komaReal Madrid a shekarar 2013 wanda ya fi kowane dan wasa tsada a lokacin a kan kudi Fam miliyan 85.

Haka zalika ya zura kwallo, 100 a Real Madrid, sannan ya lashe gasar cin kofin zakarun kungiyoyin nahiyar Turai guda hudu.

Continue Reading

Trending

error: Content is protected !!