Connect with us

Wasanni

Covid-19: a baiwa Liverpool kofin Premier -Shugaban hukumar kwallon kafan turai

Published

on

Shugaban hukumar kwallon kafa na nahiyar turai, Aleksander Ceferuin, ya ce a baiwa kungiyar kwallon kafa ta Liverpool kofin Premier.

Ceferin na wannan kalaman ne biyo bayan kara dage gasar Premier da a ka yi ba tare da saka ranar dawo ba saboda annobar cutar Corona.

Ya ce” Ni banga wata hanya hanya ba da za a hana Liverpool wannan gasar”.

“mu na tattaunawa a kan wannan batun yanzu haka kawai su mu ke jira, saboda mu na son kawo karshen kamala duk wata gasa , saboda ba za mu kai har watan Satumba ba ko kuma Oktoba a na gasar nahiyar turai, saboda gasar cin kofin zakarun nahiyar turai da ta Europa dole mu dakatar da su har idan an bamu umarnin dakatarwa”. Inji Ceferin.

Wasanni biyu kawai Liverpool za ta ci ta lashe gasar Preimer a bana tun cikin shekaru 30 da ba ta lashe gasar ba.

Tuni dai kasar Belgium da Scotland su ka mikawa wanda yake a kan teburi kofi sakamakon tsayawa cak da a ka yi a harkokin kwallon kafa a duniya saboda CoronaVIRUS.

 

Wasanni

Kocin Munich: Ina taya Klopp murnar daukan Thiago

Published

on

Mai horas da kungiyar Bayern Muncih Hansi Flick ya taya Kocin Liverpool, Jurgen Klopp murnar daukan dan wasa Thiago Alcantara.

Tuni dan wasan, Thiago Alcantara ya yi bankwana da kungiyar sa ta Bayern Munich da kuma abokan karawar sa, sakamakon barin kungiyar da zai yi zuwa Liverpool.

Thiago mai shekaru 29, ya cimma yarjejeniya da Liverpool, inda za ta biya kudin sa a kan kudi Fam miliyan 25 kwatankwacin Yuro miliyan 27.5.

Kocin ya ce“Thiago dan wasa ne wanda ya banbanta da sauran ‘yan wasa, ya shafe tsawon shekaru 7 tare da mu, kwararre ne a harkar kwallon kafa, mu dai duk jikin mu ya yi sanyi yau dinnan, saboda ya yi sallama da mu, kawai dai zan yi masa fatan alheri, kuma ina yabawa Jurgen Klopp sakamakon daukan dan wasan da ya yi, mu kuma mun yi rashin dan wasa mai nagarta”. Inji Flick.

Continue Reading

Wasanni

Kasar Sin: Za su fara kallon gasar Firimiya a Talabijin

Published

on

Hukumar gasar Firimiya ta kasar Ingila, ta cimma yarjejeniya da kasar Sin, domin haskaka gasar Firimiya a kasar na kakar 2020 da 2021.

Hukumar ta cimma yarjejeniyar da kamfanin Tencent Sports, bayan da hukumar gasar Firimiya ta kwace kwantiragi na Fam miliyan 564 da talabijin na PPTV a cikin farkon wannan watan.

Masu kallon gasar Firimiya a kasar Sin za su fara kallon wasannin da za a fafata a wannan makon mai zuwa.

Continue Reading

Wasanni

Gareth Bale: Ungulu za ta koma gidan ta na tsamiya

Published

on

A ranar Juma’a mai zuwa ne dan wasan gaban kungiyar Real Madrid, Gareth Bale, zai koma tsohuwar kungiyar sa ta Tottenham Hotspur a matsayin aro.

Bale dan kasar Wales mai shekaru 31, wanda har yanzu a na ci gaba da tattaunawa domin samun masalaha a tsakanin kungiyoyin biyu, domin komawar sa Tottenham.

Har idan a ka kammala tattaunawar dan wasa Bale zai tattaki har zuwa birnin London, domin ya rattaba kwantiragi a tsohuwar kungiyar sa.

A ranar Alhamis ne a ka hangi Bale ya ware kan sa ya na daukar horo shi kadai a kungiyar sa ta Real Madrid.

A shekarar 2007 ne dan wasa Bale ya koma Tottenham daga kungiyar Southampton, daga nan kuma ya komaReal Madrid a shekarar 2013 wanda ya fi kowane dan wasa tsada a lokacin a kan kudi Fam miliyan 85.

Haka zalika ya zura kwallo, 100 a Real Madrid, sannan ya lashe gasar cin kofin zakarun kungiyoyin nahiyar Turai guda hudu.

Continue Reading

Trending

error: Content is protected !!