Connect with us

Labarai

Covid-19: Yadda kasuwar Singa ta kasance a ranar da za a killace al’umma

Published

on

Dimbin al’umma ne su ka rinka kwararowa daga sassan cikin jihar Kano da kewaye domin siyayyan kayayyakin masarufi saboda kulle da za a yi a fadin Kano baki daya.

Cikin kasuwar Singa nan ne inda a ke gudanar da hada-hadar siyar da kayan masarufi wanda ta yi shahara wajen diban al’umma.

Cinkoso da a ka hada a kan titin Ibrahim Taiwo Road daf da kasuwar Singa

Cikin kasuwar dai ta kasance babu masaka tsinke sakamakon manyan motoci ciki harda Tirela da sauran motocin daukar kaya, saboda cushewa da ta yi duka dai a kokarin kowa ya dauke kayayyakin da ya siya.

Wasu sun gwammace su yi tafiyar kafa maimakon su shafe awanni a tsaye su na jiran abun hawa

Su kuwa a nasu bangaren wadanda su ke yin dako a cikin kasuwar tun daga kurar daukar kaya da wanda su ke dauka da kan su ko kuma goya kayan a bayan su kasuwar su ce ta bude.

haka zalika tutunan da suke kewaye da kasuwar ya kasance a cike da al’umma yayin da wasu ke ta jiran ababan hawa saboda cinkoson al’umma.

Labarai

An sanya ranar fara ɗibar Maniyyata aikin Hajjin 2025, daga Kano zuwa ƙasar Saudiyya

Published

on

Yayin da aikin hajjin bana ke ƙara gabatowa a ƙasa mai Tsarki, hukumar jin daɗin Alhazai ta Jihar Kano, ta shayar da ranar 13 ga watan Mayun 2025, a matsayin ranar farko da za’a fara ɗibar Maniyyata aikin hajjin bana, daga jihar Kano zuwa ƙasar Saudiyya.

Cikin sanarwar da jami’in yaɗa labaran shukumar Sulaiman Abdullahi Dederi ya fitar, ta ce Darakta Janar na hukumar Alhaji Lamin Rabi’u Danbappa, ne ya bayyana hakan ranar Asabar, a yayin wata ziyara da ya kai cibiyoyin karatun koyon Aikin Hajj na kananan hukumomin Ungogo da Bichi, a wani bangare na shirin Hajjin shekarar 2025.

 

“Bisa ga jadawalin da Hukumar kula da Aikin Hajji ta Ƙasa (NAHCON) ta fitar, cewa Jihar Kano za ta fara jigilar maniyyatan mu zuwa Saudiyya, tare da kamfanin jirgin sama na Max Air a ranar 13 ga Mayu, 2025, “in ji Lamin”.

Ɗanbaffa, ya ƙara da cewa Hukumar ta kammala dukkanin shirye-shiryen da suka kamata tun da wuri, domin tabbatar da cewa an gudanar da jigilar maniyyatan cikin nasara da tsari mai kyau.

 

Da yake nasa jawabin, Shugaban Hukumar, Alhaji Yusif Lawan, ya ja hankalin maniyyata masu niyyar tafiya aikin hajjin, da su rika halartar karatun koyon Aikin Hajjin a kai a kai domin amfanin kansu.

 

Haka kuma, ya gargade su da su kiyaye bin dokoki da ka’idojin na hukumomin Najeriya, da kuma waɗanda Saudiyya suka shimfiɗa domin tafiyar da aikin Hajjin na 2025.

Continue Reading

Labarai

Ba mu san Hamisu Breaker ya saki waƙar Amanata ba – Hukumar tace fina-finai

Published

on

Hukumar tace Fina-finai da Ɗab’i ta jihar Kano ta ce yanzu haka tana kan bincike don gano yadda akai mawakin nan Hamisu Breaker, ya saki sabuwar wakarsa mai suna “Amanata” ba tare da an tantance ta ba.

Mai magana da yawun hukumar Abdullahi Sani Sulaiman, shi ne ya bayyana hakan a wani sakon murya da ya aikowa Dala FM Kano, a ranar Alhamis 24 ga watan Afrilun 2025.

Ya kuma ce aikin dakatar da wakar ba na hukumar Hisbah ba ne na hukumar tace fina-finai ne, amma ba laifi ba ne kasancewar duk hukumomi ne na Gwamnati, a don haka idan hukumar ta Hisbah ta magantu akai babu laifi, domin dama suna aiki kafaɗa da kafaɗa.

A game da wakar ta Hamisu Beraker, mai suna “Amanata”, Abdullahi Sani, ya ce su har yanzu ba su san ta ina wakar ta fita ba tare da an tantance ta ba, amma tuni shugaban hukumar Abba Al-mustapha ya bada umarnin gudanar da bincike akan ta.

Hukumar Hisbah ta Jihar Kano ce dai ta hannun mataimakiyar babban kwamandan ta a ɓangaren mata Dakta Khadijah Sagir Sulaiman, ta yi Allah wa-dai da wakar Hausar mai taken “Amana ta” da mawaki Hamisu Breaker ya rera, inda ta shawarci matasa da su guji sauraren wakar, bisa yadda take ɗauke da abubuwan da ke ƙarfafa aikata alfasha, da kuma amfani da kalmomin batsa a cikin bidiyon ta.

Continue Reading

Hangen Dala

Rashin wuta: Muna cikin mawuyacin hali – al’ummar Kano, Katsina da Jigawa

Published

on

Al’ummar jihohin Kano, katsina da Jigawa na fuskantar yanayi mara dadi, Sakamakon karancin samun wutar lantarki daga hukumar KEDCO.

Al’ummar jihohin sun ce iya sa’o’i uku kacal suke samun wutar, wanda hakan ke haifar musu da nakasu a harkokin kasuwancin su.

Wani bincike da jaridar Daily Trust tayi ta ambato yadda masu kananan masana’antu irin su Walda, Cajin Waya, Kankara da masu sana’ar dinki da dai sauran kananan sana’o’i dake amfani da wutar lantarki sun shiga mawuyacin hali.

Kazalika rashin wutar ya shafi hatta bangaren ruwan sha, dama masu sana’ar sayar da Ruwa a irin yankunan Hotoro da sauran irin wuraren dake sayen ruwa, Inda yanzu haka ruwan yayi tashin gwauron zabi a kowace jarka.

Koda dai ana ta bangaren hukumar rarraba hasken wutar lantarkin me kula da shiyyar Kano, Katsina da Jigawa KEDCO sun nemi afuwar al’umma.

Idan za’a tuna dai a makon jiya ne Ministan Wutar lantarki yace ‘yan Nigeria Miliyan 150 na samun wadatacciyar wutar lantarki.

Sai dai kuma a jihohi irin su Kano, Katsina da Jigawa na bayyana damuwa kan karancin Wutar, Inda suka ce bata wuce ta sa’o’i uku suke samu a kowa ce rana.

Continue Reading

Trending