Connect with us

Labarai

Covid-19: Matashi ya jawo kansa jangwam a shafin sa na Facebook

Published

on

Rundunar ‘Yansandan jihar Kano, ta kama wani matashi mai suna Sadam Sani Umar, da ta ke zargin ya yi rubutu a shafin sa na Facebook da ka iya tunzura al’umma.

Rundunar ta na zargin matashin ya shiga shafin sa na Facebook Inda ya rubuta cewar “ku na ganin mortar da a ka dauko tallafin Covid-19 na ‘yan Jama’iyar APC ku sa wawa babu abun da zai faru”. Inji matashin.

DSP Abdullahi Haruna, ya bayyana matakin da za su dauka tare da gargadin masu rubuta labarin karya ko batun da zai tunzura jama’a.

Wakilin mu Abba Isah Muhammad, ya rawaito cewa, rundunar ta kuma ce za ta cigaba da farautar masu yin kalamai ko rubutun da ya saba doka a shafukan sada zumunta domin tabbatar da dorewar zaman lafiya a Jihar Kano da kasa baki daya.

Labarai

Ma’aikatar Ruwa za ta ƙara wadata al’ummar Kano da kewaye da ruwa – Ali Haruna Makoɗa

Published

on

Kwamishinan albarkatun ruwa na jihar Kano Ali Haruna Makoɗa, ya sha alwashin farfaɗo da cibiyar tara ruwar nan mai lamba 6 wato River Inteake, dake Challawa, wadda tsohon gwamnan Kano Injiniya Rabi’u Musa Kwankwaso ya samar da ita a lokacin mulkin sa, domin wadata al’ummar birnin Kano da kewaye da ruwa.

Ali Haruna Makoɗa, ya bayyana hakan ne lokacin da ya kai ziyara gidan ruwa na Challawa dake ƙaramar hukumar Kumbotso a jiya Lahadi, domin ganewa idanunsa umarnin da yayi na gyaran manyan famfunan dake tunkuɗo ruwa a kwanakin baya, inda ya tarar an kammala gyaran kamar yadda ya buƙata.

Ta cikin wata sanarwar da mataimaki na musamman ga kwamishinan albarkatun ruwan na Kano kan kafafen sada zumunta Sharu Ahlan ya aikowa Dala FM Kano, Ali Makoɗa, ya kuma ce farfaɗo da matatun ruwan zai taimaka wajen wadata al’ummar jihar Kano, domin ci gaba da amfani da shi cikin nasara.

Sanarwar ta ƙara da cewa daga bisani dai kwamishinan albarkatun ruwan Ali Haruna Makoɗa, ya kuma kai ziyara cibiyar tara ruwan nan Mai lamba 6 wato “RIVER INTEAKE”, wadda tsohon Gwamna Rabi’u Musa ya Samar da ita tun a lokacin mulkin sa a jihar Kano.

Continue Reading

Labarai

Ku cire banbancin siyasa ko Addini wajen raba tallafin kayan abinci – Kantoman Dawakin Tofa

Published

on

Shugaban rikon karamar hukumar Dawakin Tofa a jihar Kano Kabiru Ibrahim Dan Guguwa, ya buƙaci ƴan Kwamitin da za su raba kayan abinci Buhu 1500, da Taliya katan 110, da su tabbatar da kayan sun je ga mabuƙatan da suka cancanta, ba tare da nuna banbancin siyasa ko Addini ba.

Kabiru Ibrahim Dan Guguwa, ya bayana hakan yayin da yake kaddamar da rabon kayan abincin a cibiyar harkokin Adinin Musulinci dake karamar hukumar a ranar Asabar.

Dan Guguwa, ya kuma kara da cewar, za’a raba tallafin a duk mazaɓun dake karamar hukumar ta Dawakin Tofa, dan ragewa mutane halin matsin rayuwar da ake ciki a yanzu.

Wakilinmu Abba Isah Muhammad ya rawaito shugabancin rikon na ƙaramar hukumar, ya kuma ce zai ci gaba da bin hanyoyin inganta rayuwar al’ummar ƙaramar hukumar tare da sauraron shawarwarin su wajen kawo ayyukan ci gaba a gare su.

Continue Reading

Labarai

Samar da magunguna da kula da marasa lafiya a ƙananan Asibitoci zai rage cinkoso a manyan Asibitoci – Mai unguwar Darma

Published

on

Mai unguwar Darma Malam Ashiru Hamza, ya ce samar da magunguna da kula da marasa lafiya a cikin ƙananan Asibitocin dake kusa da Al’umma, zai temaka wajen rage cinkoso a cikin manyan Asibitocin Jihar nan.

Malam Ashiru Hamza ya bayyana hakan ne a lokacin da Kungiyar Darma Zumunta, suka kai tallafin katin rubuta maganin karbar magani a karamin Asibiti dake unguwar Darma a mazabar Chedi a yau Laraba.

“Samar da katin bada magungunan a asibitoci zai taimakawa marasa lafiya, tare da rubuta musu magani a hukumance; muna buƙatar ƙungiyar ku ƙara ƙaimi wajen samar da hasken wutar Lantarki a Asibitoci domin ragewa al’umma wani raɗaɗin rayuwar da ya ke damun su, “in ji mai unguwar Darma”.

Da yake nasa jawabin shugaban ƙungiyar ta Darma Zumunta, Alhaji Ɗan Babannan Musa, wanda ya samu wakilcin Musa Ahmad Husaini, ya ce sun himmatu wajen taimakawa marasa lafiya, da ƙulla zumunci da Juna, wanda ta hakan ne suka dauki gaɓarar samar da katin a Asbitin.

A nasa ɓangaren likitan dake kula da Asibitin na unguwar Darma Musa Ibrahim Buhari, ya ce aikin da su keyi yana buƙatar taimakon Al’umma, musamman wajen karo musu kayan aikin, domin samun damar kula da lafiyar mutane a Asibitin.

A yayin kai kayan tallafin an samu halartar tsohon kansilan mazaɓar Chedi Usman Makel, wanda ta dalilinsa ne aka kai Asibitin unguwar Darma a lokacin da yake kan mukamin kansilan mazaɓar.

Continue Reading

Trending