Labarai
An kama dan sandan da ya takurawa wata budurwa a Kano

Wata mata da ke unguwar Hotoro bayan Depot ta kai korafin wani jami’in Dan sanda a shelkwatar rundunar ‘yan sandan jihar Kano bisa zargin takurawa rayuwar ta da kuma cin zarafin ta da ya ke yi.
Matar ta kai korafin jami’in Dan sandan ne mai aiki a unguwar ta Hotoro ranar Alhamis domin a yi mata iyaka da shi.
Ta ce, “Akwai wani Dan sanda da a ke cewa Dan masani, to ya takurawa rayuwa ta, bayan an kai kara ta ya kamani a kan laifin da ba a bincike ni ba, ba’ a yi min komai ba, bayan na dawo gida kullum ya na bibiya ta ya na takurawa rayuwa ta. Ya taba zuwa ya same ni ba da kwakwkwaran sutura a jiki na ba, ya ce lallai sai na hau mota mun tafi, mutanen unguwa su ka fito su na ba shi hakuri ya ce, zai hada da su. Ni ba matar aure ba ce. Yanzu abubuwan sun yawa sai na kira dakin korafi na ‘yan sanda, kuma na zo na ga adalci karara, na gode wa Allah an taimaka min, kuma an kamo shi. Ba wani abu da yake kawo shi kawai in ya zo ya ce, in hau mota, ko kuma akwai kanne na mata guda biyu ya ce, suma lalle sai ya tafi da su”.
Ta kara da cewa, “Ya kamani ina jinin al’ada, na yi na yi ya barni in gyara jiki na, karshe ma’aikatan su ka ce ya barni in gyara jiki na ya ce a’a, har ya kasance su na kora ta saboda ina bata mu su wuri da jini, shi ne dalilin ya sa na kawo karar shi, ya na nan an kamo shi. Ni abun da na gani an taimake ni, kuma an gurfanar da shi a gaban manyan sa, kuma an yi adalci daidai gwargwado. Matakin da na ke so a dauka a raba ni da shi babu ni babu shi. Iya sanina abun da ya taba hada ni da shi ya taba cewa in bashi hadin kai naki”. A cewar matar.
Audio PlayerA nasa bangaren Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Kano DSP Abdullahi Haruna Kiyawa ya ce, “Kwamishinan ‘yan sandan jihar Kano, ya sa an kamo wannan Dan sanda kuma ya bada umarnin a yi binciken kwakwaf, duk wanda ya ke da gaskiya a ciki, za ta bayyana kuma za a yi adalci. Kai tsaye kowanne lokaci mu na bada lambar ofishin mu, ko kuma a zo kai tsaye, ko a je ofishin mu da ke kusa a sanar da D.P.O, shi kuma ya turo mutane zuwa ofishin na mu”. Inji DSP Kiyawa.
Audio PlayerWakilin mu Abba Isah Muhammad ya rawaito cewa, DSP Abdullahi Haruna Kiyawa ya kuma ja hankalin sauran jami’an ‘yan sanda da su yi aiki da gaskiya da rikon amana kamar yadda doka ta tanadar.

Labarai
Ba mu san Hamisu Breaker ya saki waƙar Amanata ba – Hukumar tace fina-finai

Hukumar tace Fina-finai da Ɗab’i ta jihar Kano ta ce yanzu haka tana kan bincike don gano yadda akai mawakin nan Hamisu Breaker, ya saki sabuwar wakarsa mai suna “Amanata” ba tare da an tantance ta ba.
Mai magana da yawun hukumar Abdullahi Sani Sulaiman, shi ne ya bayyana hakan a wani sakon murya da ya aikowa Dala FM Kano, a ranar Alhamis 24 ga watan Afrilun 2025.
Ya kuma ce aikin dakatar da wakar ba na hukumar Hisbah ba ne na hukumar tace fina-finai ne, amma ba laifi ba ne kasancewar duk hukumomi ne na Gwamnati, a don haka idan hukumar ta Hisbah ta magantu akai babu laifi, domin dama suna aiki kafaɗa da kafaɗa.
A game da wakar ta Hamisu Beraker, mai suna “Amanata”, Abdullahi Sani, ya ce su har yanzu ba su san ta ina wakar ta fita ba tare da an tantance ta ba, amma tuni shugaban hukumar Abba Al-mustapha ya bada umarnin gudanar da bincike akan ta.
Hukumar Hisbah ta Jihar Kano ce dai ta hannun mataimakiyar babban kwamandan ta a ɓangaren mata Dakta Khadijah Sagir Sulaiman, ta yi Allah wa-dai da wakar Hausar mai taken “Amana ta” da mawaki Hamisu Breaker ya rera, inda ta shawarci matasa da su guji sauraren wakar, bisa yadda take ɗauke da abubuwan da ke ƙarfafa aikata alfasha, da kuma amfani da kalmomin batsa a cikin bidiyon ta.

Hangen Dala
Rashin wuta: Muna cikin mawuyacin hali – al’ummar Kano, Katsina da Jigawa

Al’ummar jihohin Kano, katsina da Jigawa na fuskantar yanayi mara dadi, Sakamakon karancin samun wutar lantarki daga hukumar KEDCO.
Al’ummar jihohin sun ce iya sa’o’i uku kacal suke samun wutar, wanda hakan ke haifar musu da nakasu a harkokin kasuwancin su.
Wani bincike da jaridar Daily Trust tayi ta ambato yadda masu kananan masana’antu irin su Walda, Cajin Waya, Kankara da masu sana’ar dinki da dai sauran kananan sana’o’i dake amfani da wutar lantarki sun shiga mawuyacin hali.
Kazalika rashin wutar ya shafi hatta bangaren ruwan sha, dama masu sana’ar sayar da Ruwa a irin yankunan Hotoro da sauran irin wuraren dake sayen ruwa, Inda yanzu haka ruwan yayi tashin gwauron zabi a kowace jarka.
Koda dai ana ta bangaren hukumar rarraba hasken wutar lantarkin me kula da shiyyar Kano, Katsina da Jigawa KEDCO sun nemi afuwar al’umma.
Idan za’a tuna dai a makon jiya ne Ministan Wutar lantarki yace ‘yan Nigeria Miliyan 150 na samun wadatacciyar wutar lantarki.
Sai dai kuma a jihohi irin su Kano, Katsina da Jigawa na bayyana damuwa kan karancin Wutar, Inda suka ce bata wuce ta sa’o’i uku suke samu a kowa ce rana.

Hangen Dala
Rashin wuta:- Muna cikin mawuyacin hali – al’ummar Kano, Katsina da Jigawa

-
Nishadi5 years ago
Ina neman mijin aure – Rayya
-
Labarai5 years ago
Hamisu Breaker ya kai kan sa wajen ‘yan sanda
-
Nishadi6 years ago
Mansura Isah ta yi kaca-kaca da Sadiya Haruna
-
Manyan Labarai5 years ago
KAROTA: An baiwa Baffa Babba wa’adin kwanaki bakwai
-
Labarai5 years ago
Auren dan Panshekara da ba Amurkiya ya samu cikas
-
Lafiya3 years ago
Rahoto: An gano wani gida da ake gini da takardun Kur’ani da Alluna
-
Manyan Labarai5 years ago
Sabuwar damfarar da ta fito a Kano
-
Nishadi6 years ago
An gano daliban da Adam Zango ya dauki nauyin karatun su