Connect with us

Labarai

Yadda a ke yanka rakumi

Published

on

Jami’in hulda da jama’a na kasuwar sayar da dabbobi da ke Kofar Na’isa, Kwamared Umar Hamisu Kofar Na’isa ya ce, rashin iya sarrafa naman rakumi wajen dafawa kan sanya shi yin tauri.

Kwamared Umar Hamisu Kofar Na’isa ya bayyana hakan ne a zantawar sa da gidan gidan rediyon Dala ranar Talata.

Ya ce, “Mu nan jihar Kano ba mu saba da yanka rakumi a matsayin abun layya ba, za ka ga idan a ka ce, gida za’a yanka rakumi abun ya zama abun kallo, za’a cika yara da manya an zo kallon yanka rakumi, amma lokaci na tafiya, da ya ke an ce zamani canjawa yake, kusan daga shekaru uku zuwa mutane sun fara fahimtar yanka rakumi, kuma mu na nan mu na bincike a kan batun shin tsakanin rakumi da sa wanne yafi nama? Kamar mu yanzu idan kwastoma ya zo mu na wasa kasuwar mu da cewar, rakumin dubu dari da hamsin zai iya baka naman sa na dubu dari da tamanin”.

Kwamared Umar, ya kuma ce, “Rashin fahimta ne, a na yawan cewa naman rakumi yafi tauri, tunda an fi sabawa da yanka sa, ta bangaren sarrafawa ne idan har uwar gida, ko kuma wadanda za su sarrafa naman sun goge da yadda za su iya sarrafa naman rakumi, to ba za ka iya banbance naman rakumi da naman sa ba, domin za ka iya zuwa kasuwa ka sayi naman rakumin ba kasan shi ba ne ba”.

Ya kara da cewa, “Rakumi ba kayar da shi a ke yi kamar sa ba, a kan dan yi masa ‘yan dabaru ya kwanta, idan ma bai kwanta ba za’a sa igiyoyi a kafafunsa guda biyu a ja su, a rike kafafun sa guda biyu na gaba sai a hade su a sa igiya a daure tsakanin gwiwar hannun, sai kafafun ya kwanta, shi ba sai an kwantar da shi ya yi rigingine ba, shi zaman rakumi tankwashe kafa ya ke yi, kafafun da ya tankwashe sai a sa igiya, wannan dogon wuyan na sa sai a jawo igiya kan ya lakwanshe ya hadu da gangar jiki sai a daure kan”.

Kazalika, ya kuma ce, “Yadda ake yanka rakumi ba yadda ake yanka sa ba ne, shi ba tsakiyar wuyan sa a ke yanka wa ba, shi kuma rakumi a na yanka shi ta tsakanin wuyan na sa da gangar jiki, akwai wani rami da ake sa mun wuka mai tsini sai a caka a jata gefe da gefe, daga nan rakumi ya yanku, sai kuma fida, shi kuma rakumi ta baya ake fede shi”. A cewar Kwamared Umar Kofar Na’isa

Wakilin mu Tijjani Adamu ya rawaito cewar, Kwamared Hamisu ya kuma ce, babban rakumi wanda a ka saba da hawan sa, yafi saukin yankawa a kan matashin rakumi wanda yanka shi ya ke bayar da wahala.

 

Hangen Dala

Yau shugaban kasa zai dawo daga Faransa

Published

on

Bayan ziyarar aiki ta kusan mako biyu Zuwa kasar Faransa a yau litinin ake saka ran shugaban kasa zai dawo gida Nigeria.

Cikin sanarwar da hadimin shugaban kasar kan harkokin yada labarai Bayo Onanuga ya fitar ya ce kowa ne lokaci daga yanzu shugaban kasa Asuwaju Bola Tinubu zai sauka a Nigeria domin cigaban da harkokin mulkin kasar.

Continue Reading

Labarai

Zan gina makarantun Islamiyya da ta Boko don tunawa da Mafarautan da aka kashe a Uromi – Rurum

Published

on

Ɗan majalisar Wakilai mai wakiltar ƙananan hukumomin Rano, da Kibiya da Bunkure Kabiru Alhassan Rurum, ya yi alƙawarin gina makarantu guda biyu na Islamiyya da na Boko, a garin Torankawa da ke ƙaramar hukumar Bunkure, don tunawa da mafarautan da aka kashe a garin Uromi ta Jihar Edo a kwanakin baya.

Hakan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da mataimakin ma musamman ga ɗan majalisar Fatihu Yusuf Bichi ya aikewa Dala FM Kano, Sanarwar ta ce hakan na zuwa ne yayin da Rurum, yake jajantawa al’ummar garuruwan da Iyalan mamatan 16 da aka kashe, a garin Uromi da ke ƙaramar hukumar Essan ta jihar Edo.

 

Rurum ya kuma buƙaci Mafarauta daga yankin Arewa da su dakatar da zuwa kudancin kasar da sunan Farauta, don su mutane ne dake yawo da kayan daji kuma akwai banbancin yare tsakani da hakan ke sanyawa ana yawan cin zarafin su da sunan matsalar tsaro.

 

Honarable Kabiru Alhassan Rurum, bayan addu’o’i na musamman da ya yi ga mamatan, ya kuma bai wa iyalai da ƴan uwan su haƙurin jure rashin, tare da bai wa iyalan waɗanda kisan gillar ya rutsa da su gudunmawar Naira Miliyan Biyar, domin a ɗan yi cefanen kayan abinci.

Continue Reading

Labarai

Za mu fara ɗaukar mataki akan masu zance a cikin Mota – Hukumar Hisbah

Published

on

Hukumar Hisbah ta jihar Kano ta ce ta shirya tsaf wajen ganin ta kawo ƙarshen zancen da wasu Masoya suke yi a cikin Motoci, domin daƙile ɓarnar da ke yaɗuwa ta hakan a wasu lokutan.

Mataimakin babban kwamandan hukumar Hisbah a Kano, Dr. Mujahideen Aminudden, ya bayyana hakan ne yayin zantawar sa da Dala FM Kano, a ranar Juma’a 18 ga watan Afrilun 2025.

 

“Ɗaukar wannan matakin ya zama dole kasancewar lamarin na neman ya zamar wa al’ummar jihar Kano alaƙakai, “in ji shi”.

Dakta Mujahidden ya kuma yi kira ga iyaye da su sanya idanu kan tarbiyyar ƴaƴan su, tare da rage buri wanda hakan ka iya kawo ƙarshen taɓarɓarewar tarbiyyar ƴaƴan nasu.

Continue Reading

Trending