Connect with us

Labarai

An sauyawa kwamishinoni wuraren aiki

Published

on

Gwamnan Kano Dr Abdullahi Umar Ganduje ya yi sauye-sauye a cikin kwamishinonin sa, a yayin da ya kuma tabbatar da ma’aikatar sabon kwamishina.

Ganduje wanda ya yi sauye-sauyen yayin zaman majalisar zartarwar. Ta cikin wata sanarwa mai kunshe da sa hannun sakataren yada labaran gwamnan, Abba Anwar ya fitar a yammacin Laraba.

Ta ce cikin wadanda a ka sauya wa ma’aikata sun hada da Mahmud Muhammad Dansantsi dake ma’aikatar ciniki, yanzu ya koma ma’aikatar gidaje da sufuri, sai kuma Barrister M A Lawan wanda yake a ma’aikatar gidaje da sufuri yanzu ya koma ma’aikatar Sharia, shi kuwa Barrister Ibrahim Mukhtar dake ma’aikatar Sharia a yanzu an mayar da shi ma’aikatar ciniki.

Sannan kuma sabon kwamishinan da a ka rantsar a yau, Idris Garba Unguwar Rimi an turashi ma’aikatar ayyuka.

Gwamna Ganduje ya kuma umarce su da su jajirce a ayyukan su da kuma ci gaba da kiyaye dokokin Corona a ma’aikatun su.

Hangen Dala

Yau shugaban kasa zai dawo daga Faransa

Published

on

Bayan ziyarar aiki ta kusan mako biyu Zuwa kasar Faransa a yau litinin ake saka ran shugaban kasa zai dawo gida Nigeria.

Cikin sanarwar da hadimin shugaban kasar kan harkokin yada labarai Bayo Onanuga ya fitar ya ce kowa ne lokaci daga yanzu shugaban kasa Asuwaju Bola Tinubu zai sauka a Nigeria domin cigaban da harkokin mulkin kasar.

Continue Reading

Labarai

Zan gina makarantun Islamiyya da ta Boko don tunawa da Mafarautan da aka kashe a Uromi – Rurum

Published

on

Ɗan majalisar Wakilai mai wakiltar ƙananan hukumomin Rano, da Kibiya da Bunkure Kabiru Alhassan Rurum, ya yi alƙawarin gina makarantu guda biyu na Islamiyya da na Boko, a garin Torankawa da ke ƙaramar hukumar Bunkure, don tunawa da mafarautan da aka kashe a garin Uromi ta Jihar Edo a kwanakin baya.

Hakan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da mataimakin ma musamman ga ɗan majalisar Fatihu Yusuf Bichi ya aikewa Dala FM Kano, Sanarwar ta ce hakan na zuwa ne yayin da Rurum, yake jajantawa al’ummar garuruwan da Iyalan mamatan 16 da aka kashe, a garin Uromi da ke ƙaramar hukumar Essan ta jihar Edo.

 

Rurum ya kuma buƙaci Mafarauta daga yankin Arewa da su dakatar da zuwa kudancin kasar da sunan Farauta, don su mutane ne dake yawo da kayan daji kuma akwai banbancin yare tsakani da hakan ke sanyawa ana yawan cin zarafin su da sunan matsalar tsaro.

 

Honarable Kabiru Alhassan Rurum, bayan addu’o’i na musamman da ya yi ga mamatan, ya kuma bai wa iyalai da ƴan uwan su haƙurin jure rashin, tare da bai wa iyalan waɗanda kisan gillar ya rutsa da su gudunmawar Naira Miliyan Biyar, domin a ɗan yi cefanen kayan abinci.

Continue Reading

Labarai

Za mu fara ɗaukar mataki akan masu zance a cikin Mota – Hukumar Hisbah

Published

on

Hukumar Hisbah ta jihar Kano ta ce ta shirya tsaf wajen ganin ta kawo ƙarshen zancen da wasu Masoya suke yi a cikin Motoci, domin daƙile ɓarnar da ke yaɗuwa ta hakan a wasu lokutan.

Mataimakin babban kwamandan hukumar Hisbah a Kano, Dr. Mujahideen Aminudden, ya bayyana hakan ne yayin zantawar sa da Dala FM Kano, a ranar Juma’a 18 ga watan Afrilun 2025.

 

“Ɗaukar wannan matakin ya zama dole kasancewar lamarin na neman ya zamar wa al’ummar jihar Kano alaƙakai, “in ji shi”.

Dakta Mujahidden ya kuma yi kira ga iyaye da su sanya idanu kan tarbiyyar ƴaƴan su, tare da rage buri wanda hakan ka iya kawo ƙarshen taɓarɓarewar tarbiyyar ƴaƴan nasu.

Continue Reading

Trending