Connect with us

Labarai

Gwamnatin tarayya: Ba za a bude makarantu ba a Nijeriya

Published

on

Gwamnatin tarraya ta ce ba za ta bude makarantu ba a fadin kasar nan ba, har sai an bullo da sabbin tsare-tsare na kare dalibai daga kamuwa da cutar Corona.

Karamin ministan Ilimi, Chukwuemeka Nwajiuba ne ya bayyana hakan yayin zantawa da manema labarai, jim kadan bayan kammala taron majalisar zartasawa ta kasa a jiya Labara.

A cewar sa, duk da majalisar wakilai ta bukaci da a bude makarantun kasar nan sannan a baiwa daliban ‘yan ajin karshen na sakandire damar rubuta jarrabawar kammala sakandire ta yammcin Afirka WAEC, ba daidai bane a bude makarantu ko ba wa daliban rubuta jarrabawar, ba tare da an bullo da tsare- tasren kare su daga kamuwa ko yada cutar ba.

Karamin ministan ilimin ya kuma ce,” Ma’aikatar ilimi ta lura da cewa, akwai hadari babba idan har a ka bar dalibai su ka koma makarantu tsaka da wannan cuta mai hadarin gaske. A yanzu haka ma su ruwa da tsaki na tsaka da tattaunawa kan yi wuwar bude makarantu ko baiwa dalibai ‘yan ajin karshe damar rubuta jarrabawa.

Hangen Dala

Rashin wuta: Muna cikin mawuyacin hali – al’ummar Kano, Katsina da Jigawa

Published

on

Al’ummar jihohin Kano, katsina da Jigawa na fuskantar yanayi mara dadi, Sakamakon karancin samun wutar lantarki daga hukumar KEDCO.

Al’ummar jihohin sun ce iya sa’o’i uku kacal suke samun wutar, wanda hakan ke haifar musu da nakasu a harkokin kasuwancin su.

Wani bincike da jaridar Daily Trust tayi ta ambato yadda masu kananan masana’antu irin su Walda, Cajin Waya, Kankara da masu sana’ar dinki da dai sauran kananan sana’o’i dake amfani da wutar lantarki sun shiga mawuyacin hali.

Kazalika rashin wutar ya shafi hatta bangaren ruwan sha, dama masu sana’ar sayar da Ruwa a irin yankunan Hotoro da sauran irin wuraren dake sayen ruwa, Inda yanzu haka ruwan yayi tashin gwauron zabi a kowace jarka.

Koda dai ana ta bangaren hukumar rarraba hasken wutar lantarkin me kula da shiyyar Kano, Katsina da Jigawa KEDCO sun nemi afuwar al’umma.

Idan za’a tuna dai a makon jiya ne Ministan Wutar lantarki yace ‘yan Nigeria Miliyan 150 na samun wadatacciyar wutar lantarki.

Sai dai kuma a jihohi irin su Kano, Katsina da Jigawa na bayyana damuwa kan karancin Wutar, Inda suka ce bata wuce ta sa’o’i uku suke samu a kowa ce rana.

Continue Reading

Hangen Dala

Rashin wuta:- Muna cikin mawuyacin hali – al’ummar Kano, Katsina da Jigawa

Ci gaba ba ya zuwa sai an samu haɗin kan al’umma – Dagacin Ja’en

Published

on

Dagacin garin Ja’en da ke ƙaramar hukumar Gwale a jihar Kano, Alhaji Isma’il Sa’ad Usman, ya ce hadin kai ne kaɗai zai kawo ci gaba ga kowa ce irin al’umma.

Dagacin ya bayyana hakan ne Jim kaɗan bayan wani taron masu Ruwa da tsaki na Garin Ja’en, wanda Hakimin Gundumar Ɗorayi Barde Kerarriya Alhaji Shehu Kabir Bayero ya shirya, aka gudanar a yankin Ja’en a ƙarshen makon da ya gabata.

“Dukkanin wani ci gaba ba ya zuwa har sai an samu haɗin kan kowa ne bangare na al’umma, “in ji Dagacin”.

Wakilin Dala FM Kano, Ahmad Rabi’u Ja’en ya ruwaito cewa, taron ya samu halartar dukkanin bangarori, na unguwannin Ja’en, da suka haɗar da kungiyar mafarauta da maharba dabma kungiyar malaman makaranta.

Continue Reading

Trending