Connect with us

Labarai

‘Yan kasuwa za su amfana da bashin CBN – Prof Dandago

Published

on

Masanin tattalin arziki kuma tsohon kwamishinan kudi na jihar Kano Farfesa Isah Dandago ya ce, bashin da Babban bankin kasa CBN zai baiwa kananan ‘yan kasuwa zai taimaka wajen bunkasa tattalin arzikin kasar nan musamman a yanzu da annobar Corona ta lalata harkar kasuwanci a kasar nan.

Farfesa Isah Dandago ya bayyana hakan ne ta cikin shirin a zantawar sa da gidan rediyon Dala a ranar Alhamis.

Ya ce, “Bashin wanda bankin CBN ya yi yarjejeniya da bankunan kasar nan kan rashin sanya kudin ruwa a yayin da ‘yan kasuwa za su dawo da kudaden bayan juya su ta bangaren kasuwanci, akwai damar sauran jahohin kasar nan su shiga tsarin wanda kawo yanzu jahohi bakwai ne kawai suka karbi tsarin”.

A nasa bangaren tsohon Kwamishinan ciniki da kasuwanci a jihar Kano Alhaji Danburan Abubakar Nuhu ya ce, “Matukar gwamnati za ta bada  bashin bisa tsari to kuwa zai taimaka wa ‘yan kasuwa wajen farfado da kasuwancin su”.

Bakin biyu sun yi kira ga ‘yan kasuwa da su yi amfani da bashin ta hanyar da ta dace da nufin farfado da kasuwanci da tattalin arzikin kasar nan.

Hangen Dala

Rashin wuta: Muna cikin mawuyacin hali – al’ummar Kano, Katsina da Jigawa

Published

on

Al’ummar jihohin Kano, katsina da Jigawa na fuskantar yanayi mara dadi, Sakamakon karancin samun wutar lantarki daga hukumar KEDCO.

Al’ummar jihohin sun ce iya sa’o’i uku kacal suke samun wutar, wanda hakan ke haifar musu da nakasu a harkokin kasuwancin su.

Wani bincike da jaridar Daily Trust tayi ta ambato yadda masu kananan masana’antu irin su Walda, Cajin Waya, Kankara da masu sana’ar dinki da dai sauran kananan sana’o’i dake amfani da wutar lantarki sun shiga mawuyacin hali.

Kazalika rashin wutar ya shafi hatta bangaren ruwan sha, dama masu sana’ar sayar da Ruwa a irin yankunan Hotoro da sauran irin wuraren dake sayen ruwa, Inda yanzu haka ruwan yayi tashin gwauron zabi a kowace jarka.

Koda dai ana ta bangaren hukumar rarraba hasken wutar lantarkin me kula da shiyyar Kano, Katsina da Jigawa KEDCO sun nemi afuwar al’umma.

Idan za’a tuna dai a makon jiya ne Ministan Wutar lantarki yace ‘yan Nigeria Miliyan 150 na samun wadatacciyar wutar lantarki.

Sai dai kuma a jihohi irin su Kano, Katsina da Jigawa na bayyana damuwa kan karancin Wutar, Inda suka ce bata wuce ta sa’o’i uku suke samu a kowa ce rana.

Continue Reading

Hangen Dala

Rashin wuta:- Muna cikin mawuyacin hali – al’ummar Kano, Katsina da Jigawa

Ci gaba ba ya zuwa sai an samu haɗin kan al’umma – Dagacin Ja’en

Published

on

Dagacin garin Ja’en da ke ƙaramar hukumar Gwale a jihar Kano, Alhaji Isma’il Sa’ad Usman, ya ce hadin kai ne kaɗai zai kawo ci gaba ga kowa ce irin al’umma.

Dagacin ya bayyana hakan ne Jim kaɗan bayan wani taron masu Ruwa da tsaki na Garin Ja’en, wanda Hakimin Gundumar Ɗorayi Barde Kerarriya Alhaji Shehu Kabir Bayero ya shirya, aka gudanar a yankin Ja’en a ƙarshen makon da ya gabata.

“Dukkanin wani ci gaba ba ya zuwa har sai an samu haɗin kan kowa ne bangare na al’umma, “in ji Dagacin”.

Wakilin Dala FM Kano, Ahmad Rabi’u Ja’en ya ruwaito cewa, taron ya samu halartar dukkanin bangarori, na unguwannin Ja’en, da suka haɗar da kungiyar mafarauta da maharba dabma kungiyar malaman makaranta.

Continue Reading

Trending