Connect with us

Siyasa

Ba za mu goyi bayan kafa kwamiti a jam’iyyar APC ba – Aminu Black

Published

on

Guda daga cikin magoya bayan jam’iyyar APC Gandujiyya a jihar Kano, S.A Aminu Black Gwale ya kalubalanci sabon tsarin da mataimaki na musamman ga gwamnan Kano, Shehu Isa Direba ya fito da shi na fitar da wa su kwamitoci a cikin jam’iyyar.

Aminu Black wanda ya bayyana hakan ta cikin Shirin siyasa na Hangen Dala, inda ya ce”Kafa kwamiti a cikin jam’iyyar, tamkar haifar da wani rabuwar kai ne a tsakanin magoya baya, matukar ba a gyara tsarin ba, to babu shakka sai sun fuskanci kalubale”.

Aminu Black ya kuma ce ba sa goyon bayan ware wa su ‘Yan jam’iyyar, su rinka zuwa ofisoshin kwamishinonin jihar.

Labarai

Buhari ya sake nada Farfesa Yakubu a matsayin shugaban INEC

Published

on

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya sake gabatar da sunan Farfesa Mahmood Yakubu, a majalisar dokokin kasar, domin sake ci gaba da jagorantar hukumar zabe mai zaman kanta wato INEC a wa’adi na biyu.

Shugaba Buhari ya tabbatar da sake naɗa Farfesa Yakubu ne a cikin wata wasika da ya aika wa shugaban majalisar dattiajai Sanata Ahmed Lawan.

Wata sanarwa mai dauke da sa hannun mai magana da yawun shugaban, Femi Adesina, ta ce bisa tanadin sashi na 154 (1) na kundin tsarin mulkin Najeriya na 1999 da aka yiwa gyaran fuska, “Ina farin cikin gabatar da Farfesa Mahmood Yakubu ga majalisa domin tabbatar da shi a matsayin Shugaban, Hukumar zabe mai zaman kanta ta Kasa (INEC) a karo na biyu kuma wa’adi na karshe.

Farfesa Yakubu shi ya jagoranci babban zaben shekarar 2019, da kuma na gwamnoni da ake gudanarwa lokaci daban da babban zaɓe.

Duk da cewa yawancin zabukan da ya jagoranta sun sha suka daga masu sanya ido daga cikin gida da kuma wajen kasar, kan matsaloli da zargin magudi, amma kuma an yaba masa a zaben gwamnoni da ya jagoranta a baya-baya nan a jihohin Edo inda dan takarar jam’iyyar PDP mai hamayya ya lashe da kuma Ondo da dan takarar jam’iyyar APC ya yi nasara.

A watan Oktoba 2015 ne Shugaba Buhari ya naɗa Farfesa Yakubu a matsayin shugaban hukumar INEC, wanda ya maye gurbin Farfesa Attahiru Jega.

Continue Reading

Labarai

Babu wanda ya cancanci shan romon dumukradiya sai talaka – Farfesa Kamilu Fagge

Published

on

Masanin kimiyyar siyasa a Jami’ar Bayero da ke jihar Kano Farfesa Kamilu Sani Fagge, ya ce, babu wanda ya cancanci ya sha romon dumukradiya kamar talaka, duba da su ke jefawa shugabanni kuri’a har su samu su dare kujerar mulki.

Farfesa Kamilu Sani Fagge, ya bayyana hakan ne a zantawar sa da gidan rediyon Dala a ranar Alhamis

Haka zalika, shima wani masanin tattalin arziki a Jami’ar Yusuf Maitama sule da ke jihar Kano Dr. Yusuf Ibrahim Kofar Mata ya ce, “Idan har gwamnatin kasar nan na san shawo kan matsalar halin matsin rayuwa da a ke ciki, babu shakka sai ta tuntubi shawararin masana kan harkokin tattalin arzikin”. Inji Dakta Yusuf Ibrahim Kofar Mata

Wakiliyar mu Shamsiyya Farouk Bello ta rawaito cewa, a yayin da Najeriya za ta cika shekarun 60 da samun ‘yan cin kai a tafarkin dumukradiya, amma masana na ganin har dan Najeriya bai ci ribar dumukradiyar ba.

 

Continue Reading

Labarai

Biden ya soki yadda shugaba Trump ke tunkarar annobar Covid-19

Published

on

Dan takarar shugabancin Amurka, Joe Biden ya ce abokin adawarsa wato Shugaba Donald Trump ya dasa fargaba da kuma rarrabuwar kawuna a tsakanin Amurkawa.

Joe Biden wanda ya tsaya takarar shugabancin kasar karkashin jam’iyyar Democrat ya kuma bayyana irin matakan da zai dauka idan har al’ummar kasar su ka zabe shi a watan Nuwambar bana.

Kanfanin dillancin labarai na Reuters ya rawaito cewa, tsohon mataimakin shugaban Amurka na wancan lokaci Barrack Obama, ya bayyana hakan a ranar babban taron jam’iyyar na karshe, inda ya caccaki yadda shugaban Amurka Donald Trump ke tafiyar da shirin dakile cutar Covid-19, ko da yake ya ce idan Amurkawa su ka bashi dama akwai matakan da ya tanada, domin kawo karshen cutar a kasar.

Continue Reading

Trending

error: Content is protected !!