Connect with us

Labarai

Mu na son gwamnatin Kano ta dakatar da ƙarin farashin dutse – Direbobin Tifa

Published

on

Ƙungiyar Direbobin Tifa ta kasa reshen jihar Kano ta bukaci gwamnatin Kano da ta dakatar da ƙarin ƙudin dutse da wasu kamfanonin ƙasar Sin da ke sarrafa duwatsu su ka yi musu da kusan kaso arba’in cikin ɗari ba tare da sun sanar da ƙungiyar ba.

Shugaban ƙungiyar Direbobin Tifa ta jihar Kano Kwamared Mamuni Ibrahim Takai ne ya bayyana hakan lokacin da yake zantawa da manema labarai kan batun ƙarin ƙudin da kamfanonin su ka yi wa masu siyan dutsen domin sanar da gwamnatin Kano.

Ya ce, Wannan ƙarin da kamfanonin su ka yi wa dutsen babu makawa zai haddasa tashin farashin dutsen a yanzu baya ga tsada da kwangila da za ta kara saboda ƙarin ƙudin, domin kuwa shima talaka gini zai gagareshi”.

Ya kuma ce, “Abun takaicin shi ne yadda al’ummar Kano su ke tarawa wadannan kamfanoni miliyoyin kuɗaɗen kuma duwatsun da su ke sarrafawa suna siyarwa da jama’a na ‘yan Kano ne kuma ’yan Kano ne su ke siya domin su yi amfani da shi”. A cewar Kwamared Mamuni Ibrahim Takai

Wakilin mu Abdulkarim Muhammad Tukuntawa ya rawaito cewar, shugaban kungiyar ya kuma yi ga gwamnati da ‘yan majalisar Kano harma da hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa ta jihar Kano da su takawa yunkurin kamfanonin birki domin mutane na cikin mawuyacin hali a yanzu.

 

 

 

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Labarai

Rahoto: Saurayi ya kai iyayen budurwar sa kotu kan zargin cinye masa kudade

Published

on

Wani matashi ya yi zargin iyayen budurwar sa sun karbi kudaden aure har da sadaki a hannun sa, bayan ya rage kwanaki uku a daura aure, iyayen budurwar su ka kawar da maganar auren kuma tsawon watanni ba zancen aure ko kuma dawo masa da kudaden da ya bayar.

Sai dai iyayen budurwar sun yi da’awar cewar, an je gwaji ne kafin aure saurayin ya gudu, inda shi kuma ya mayar da martanin cewar, a ranar da a ka je gwajin bai je da isassun kudi ba, shi yasa ya tafi, kuma washe gari ko da yaje gidan budurwar bijiro da zancen ta fasa auren, yanzu tsohon saurayin ta za ta aura, hakan ta sanya ya garzaya kotun shari’ar musulunci domin a bi masa hakkin sa.

Domin jin cikakken rahoton saurari wannan.

Continue Reading

Labarai

Rahoto: Mai sayen filaye ya kai karar abokin cinikin sa kotu bayan shekaru 3

Published

on

Kotun shari’ar musulunci da ke zamanta a unguwar Goran dutse, karkashin mai shari’a Isma’il Garba Kofar Na’isa, wani mutum mai suna Ibrahim Ishaq, ya yi karar wani mai suna Ibrahim Abba, kan cinikin wani filaye da su ka yi shekaru uku da su ka gabata.

Ibrahim Abba ya bai wa Ibrahim Ishaq motoci guda biyu shi kuma ya bashi filaye guda tara, daga bisani takaddama ta barke a tsakanin su, Ibrahiim Ishaq ya na zargin an cuce shi a cinikin, hakan ya sanya shi garzaya wa kotu.

Domin jin cikakken rahoton saurari wannan.

 

 

Continue Reading

Labarai

Rahoto: NAFDAC ta kama magungunan dabbobi na jabu a Kano

Published

on

Hukumar lura da ingancin abincin da magunguna ta kasa reshen jihar Kano NAFDAC, ta kai sumame wani gida a karamar hukumar Bichi, ta ka kama  wani mutum Muhammad Jamilu Sani, wanda aka samu yana hada magungunan dabbobi da allurai da ta ke zargin na jabu ne.

Shugaban hukumar Malam Shaba Muhammad ne ya bayyana hakan a ranar Laraba yayin zantawar sa da gidan rediyon Dala.

Domin jin cikakken rahoton saurari wannan.

Continue Reading

Trending

error: Content is protected !!