Connect with us

Labarai

Iyayen yaran nan da aka sace sun zargi gwamnatin Kano da kin daukar mataki

Published

on

Shekara guda kenan, da jami’an ‘yan sanda suka gano matsalar batan yaran da ake fama da su a jihar Kano da ke arewacin Najeriya, inda ake zuwa da su kudancin kasar.

Ana dai zargin cewa yaran da ake sacewa zuwa kudancin kasar, ana sauya musu suna da kuma addini.

Daga lokacin da aka gano batan yaran ne gwamnatin jihar ta kafa wani kwamiti na musamman da zai gudanar da binciken zargin batan yaran.

To sai dai kwatsam, iyayen yaran da aka sace sun bayyana takaicin su kan yadda gwamnati ta nuna halin ko in kula da halin da suke ciki.

Iyayen dai na zargin gwamnatin jihar da rashin daukar matakan da suka dace wajen binciko inda yaransu suke, duk da cewa akwai sama da guda dari da har yanzu ba a san inda suke ba.

“Gaskiya, mun fara yanke kauna da matakan gwamnatin, saboda ‘yayan talakawa ne ya sanya gwamnatin ta yi biris da batun ‘yayanmu.” In ji Zainab Giginyu

Wadannan magidanta da suka yi tattaki mazan su da matan su zuwa Dala FM, sun bayyana cewar akwai sauran yayansu sama da guda dari a yankin kudancin kasar da aka sace, amma da yawan wadanda aka zarga da satar ma an bayar da belisu suna cigaba da rayuwar su cikin farin ciki yayin da wata ma da aka bayar da belin ta ta arce.

“Muna cikin mawuyacin hali, muna rokon gwamnati ta taimaka ta binciko mana yaranmu idan har don mu take aiki, mu ‘yayanmu muke nema ba wani abu muke roko gwamnati ta yi mana ba.” In ji mahaifiyar wata yarinya

A baya dai kungiyar iyayen yaran da suka bata ta ce kwamitin da aka kafa be tuntube su ba, don haka basu da masaniya kan yadda kwamitin yake aikinsa.

Kungiyar ta ce kwamitin bincike da aka kafa tun farko be neme su ba ta yadda za su iya gabatar da bahasin yadda yaransu suka bata.

Malam Salihu Isma’il shine mai magana da yawun iyayen yaran, ya ce suna takaicin yadda gwamnati ta gaza daukar mataki, bayan tsawon shekara guda da batan yaransu.

“Yau tun da aka dawo da yaran nan shekara daya, wasu daga cikin yaran da aka dawo da su, sun ce sun ga ‘yayanmu, wasu ma ajinsu daya. tsawon shekara daya, kwamitin da aka nada har yanzu ko yaro guda daya be dawo mana da shi ba.”

Malam Salihu ya ce wasu daga cikin iyayen yara, yanzu haka suna fama da ciwon mutuwar barin jiki, wasun su kuma sun mutu saboda takaicin batan yaran nasu.

A baya-bayan nan ne kwamitin ya gabatar da rahoton bincikensa, duk da cewa kungiyar iyayen yaran ta ce babu wani tuntuba da suka same daga bangaren gwamnati kan wannan batu.

Labarai

Ƴan kasuwa ku tsaftace magudanan ruwa bisa gabatowar Damuna – Ƙungiyar Amata ta kasuwar Singa

Published

on

An buƙaci ƴan kasuwa da su rinƙa tsaftace tare da gyara magudanan ruwa a cikin kasuwannin su, bisa yadda damuna ke ƙara gabatowa.

Shugaban ƙungiyar Amata reshen kasuwar Singa Alhaji Musa Ibrahim Ɗan gaske, ne ya bukacin hakan a zantawar sa da manema labarai, yayin kaddamar da tsaftace kasuwar da kuma gyara mugudanun ruwan kasuwar.

Alhaji Musa, ya kuma ce ta hanyar tsaftace magudanan ruwan ne za a gujewa kowacce irin ambaliyar ruwa a cikin kasuwanni.

Continue Reading

Hangen Dala

Yau za’a fara Shari’ar Ganduje da gwamnatin Kano

Published

on

A yau ne babbar kotun jaha mai lamba 4 zata fara sauraron wata sharia wadda gwamnatin kano ta ahigar.

 

Gwamnatin jahar kano dai ta shigar da karar tsohon gwamnan jahar kano Dr Abdullahi Umar Ganduje da mai dakinsa Hafsat Umar Ganduje da kuma dansu Umar Abdullahi Ganduje da kuma wani kamfani mai suna Lamash da kuma Dr Jibrilla Muhammad.

 

Gwamnatin jahar kano dai tana zargin Ganduje da wadanna mutane da laifin hada baki da barnatar da dukiyoyin gwamnati.

 

 

Cikin zarge-zargen da ake yiwa su Ganduje akwai batun sun sayar da wasu filotai ba bisa ka’ida ba.

 

 

Da kuma batun zargin da akewa Ganduje na badakalar karbar dala tun a shekarar 2019.

 

 

Yanzu haka an girke jami,an tsaro a harabar sakateriyar Audu Bako inda kuma daga yanzu zuwa kowane lokaci kotun zata fara sauraron korafin kamar yadda wakilinmu Yusuf Nadabo Ismail ya rawaito

Continue Reading

Labarai

Ku tallafawa mazauna gidajen gyaran halin dan rage musu raɗaɗin rayuwa – Mallam Ibrahim Bunkure

Published

on

Limamin masallacin Salafussaleh dake unguwar Ɗorayi ƙarama a jihar Kano, Mallam Ibrahim Abdullahi Bunkure, ya shawarci al’umma da su ƙara dagewa wajen tallafawa mazauna gidajen ajiya da gyaran hali, da masu buƙata ta musamman, domin rage musu wani raɗaɗin rayuwa na yau da kullum.

Mallam Ibrahim Abdullahi Bunkure, ya bayyana hakan ne yayin da suka tallafawa mazauna gidan gyaran hali na Goron Dutse, da kayayyakin Abinci, da kuma na gidan yara, a wani ɓangare na taya su bikin ƙaramar Sallah, wajen ganin sun samu farin ciki a bukukuwan ƙaramar sallar da aka gudanar.

Ya ce matuƙar masu hali za su rinƙa tallafawa mazauna gidan gyaran halin da abubuwan da suka sawwaƙa, babu makawa za’a rage musu wata damuwa ta yau da kullum.

Wakilinmu Yakubu Ibrahim Dogarai ya rawaito cewa, Mallam Ibrahim Abdullahi Bunkure, ya ce daga cikin kayan abincin da suka kai wa mazauna gidajen akwai Tuwon Sallah, da garin Kwakwaki, da kuma sinadarin Ɗanɗano, da Sukari, domin ragewa mazaunan gidajen wani raɗaɗin rayuwa.

Continue Reading

Trending