Connect with us

Labarai

Tsoron zagi ya sanya ba ma shiga harkokin al’ummar Arewa – Ali Nuhu

Published

on

Fitaccen jarumin fina-finan Hausa a masana’antar Kannywood Ali Nuhu ya ce, tsoron yin shishshigi ko kuma zagi a dandalin sada zumunta ya sanya ba sa shiga cikin wani al’amari da ya shafi al’umma.

Ali Nuhu ya bayyana hakan ne a zantawar sa da gidan rediyon Dala a yau Juma’a.

Ya na mai cewa, “Mu na son shiga cikin al’amuran amma duba da gudun wulakanci mu ke kauda kai, kuma abubuwa da yawa na taimakon al’umma ‘yan Kannywood suna shiga domin bayar da tallafin su”. A cewar Ali Nuhu.

Ƴan wasan kwaikwayo da mawaƙa a yankin kudancin ƙasar nan dai ana ganin sun taka muhimmiyar rawa yayin zanga-zangar neman rusa rundunar ƴan sandan SARS, kuma wannan ba shi ne farau ba da in al’amuran al’umma sun tashi a yankin, mawaƙa da ƴan Film kan taka rawa wajen kawo sauyi ba.

Sai dai kuma a yankin mu na Arewa ba kasafai, mawaƙa ke shiga a dama da su kan al’amuran jama’a ba.

Itama dai jarumar fina-finan Kaddywood Saratu Gidado Daso ta ce, “Kyamar ‘yan fina-finan Hausa ya sanya ba ma shiga cikin al’amuran da suka shafi al’umma, mu da ba’a damu ba ta yaya za mu fito wata zanga-zanga”. Inji Saratu Gidado Daso.

 

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Labarai

Harin ‘yan bindiga ya yi sanadiyar mutuwar mutane 20 a Zamfara

Published

on

Yan bindiga sun hallaka mutane 20 a wani har da suka kai garin Tungar Kwana da ke karamar hukumar Mafara a jihar ta Zamfara, bayan sun saci wasu dabbobin da jami’an tsaro suka kwato.

Kakakin ‘yan sandan jihar SP Shehu Muhammad ya bayyana hakan a zantawar sa da  wakilin mu Yusuf Ibrahim Jargaba.

Ya ce, “Tuni suka baza jami’an tsaro domin gano wadanda su ka yi kisan su fuskanci hukunci”. A cewar SP Shehu Muhammad

 

Continue Reading

Labarai

Rahoto: Tarbiyya na taka muhimmiyar rawa wajen samun zaman lafiya – Liman

Published

on

Babban limamin masallacin juma’a na Umar Bin Khaddab da ke Dangi, Dr Yahaya Tanko ya ce, addinin musulunci addini ne na zaman lafiya, saboda haka al’umma su kiyayi tayar da husuma.

Dr Yahaya Tanko ya bayyana hakan ne a zantawar sa da wakilin mu Tijjani Adamu.

Domin jin cikakken rahoton saurari wannan.

Continue Reading

Labarai

Rahoto: Matashin da ake zargi da kashe matar sa ya sake gurfana a kotu

Published

on

Gwamnatin jihar Kano ta ci gurfanar da mutumin nan da ake zargin ya kashe matar sa, a gaban babbar kotun jihar Kano mai lamba 7, karkashin mai shari’a Usman Na Abba.

Tun a ranar 2 ga watan Afirilu na shekarar da ta gaba aka yi zargin Aminu Inuwa ya yi amfani da wuka ya kashe matar sa mai suna Safara’u Muhammadu, kuma binne ta a cikin gidan sa, a unguwar Gwazaye Dorayi Karama da ke karamar hukumar Gwale.

Domin jin cikakken rahoton saurari wannan.

Continue Reading

Trending

error: Content is protected !!