Connect with us

Wasanni

Mutum 103 sun kamu da Korona a gasar Premier

Published

on

A kalla ‘yan wasan Premier 103 da ma’aikatan su da a ka gwada a cikin kwanaki bakwai har zuwa 26 ga watan Dismab sun kamu da Korona.

Alkaluman tantancewar na mako-mako da ya gabata an samu 90, wanda a ka sanar mako daya da ya gabata.

An gudanar da gwaje-gwaje yan wasa da ma’aikatan su 15,186 tsakanin 20 zuwa 26 ga Disamba, yayin da mahukuntan gasar Premier ta sake dawo da gwajin ‘yan wasa da ma’aikata a kullum.

Ya zuwa yanzu an dakatar da wasannin sama da goma sha biyar a Ingila a cikin watan Disamba, saboda kamuwa da cutar Korona.

Manyan Labarai

Karya doka: ‘Yan sandan Birtaniya sun fara bincikar Boris Johnson

Published

on

‘Yan sandan Biritaniya sun ce, sun fara gudanar da wani bincike a kan matakan kariya na COVID-19 da Firayiminista, Boris Johnson ya karya a Downing Street, bayan sun sami shaida daga binciken gwamnatin cikin gida kan jerin tarurrukan da ya gudanar.

Johnson ya bayyana da’awar cewa, shi da ma’aikatansa sun yi taro a tsakiyar Birtaniyya domin, keta dokokin da suka kafa na yakar cutar ta COVID-19, wanda tun a baya ya bayar da hakuri.

Kimar Johnson ta zube a idanun ‘yan majalisar Birtaniya da kuma ‘yan kasar, sakamakon taron da ya halarta a na tsaka da gudanar da kullen lockdown a Downing Street.

ITV ya rawaito a ranar Litinin cewa, Johnson ya halarci wani bikin ba-zata a ranar haihuwarsa a shekarar 2020. Kimanin mutane 30 ne suka halarci taron a dakin taro na majalisar ministoci mai lamba 10 Downing Street, ofishinsa da mazauninsa, in ji majiyar Reuters.

Continue Reading

Manyan Labarai

Najeriya ta dawo gida bayan cire ta daga gasar AFCON

Published

on

Tawagar ‘yan wasan Najeriya na Super Eagles sun dawo gida Najeriya, bayan cire su daga daga gasar cin kofin nahiyar Afirka (AFCON) da ke gudana a kasar Kamaru na shekarar 2021.

Kamfanin dillancin labarai na Najeriya (NAN) ya rawaito cewa, tawagar ‘yan wasan da jami’an, sun dawo ne ta jirgin haya daga Garoua inda suka buga wasanni hudu a gasar.

Super Eagles sun sauka ne da karfe 1:10 na cikin daren Talata a filin jirgin saman Nnamdi Azikwe da ke Abuja, inda jami’an hukumar kwallon kafar Najeriya NFF suka tarbe su.

Jami’an NFF sun samu jagorancin babban sakataren su Mohammed Sanusi, tare da rakiyar mambobin kwamitin zartarwa na tarayya Yusuf Ahmed da Shehu Dikko.

Continue Reading

Manyan Labarai

Buhari ya bukaci Super Eagles su lashe gasar AFCON

Published

on

Shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya karfafawa tawagar ‘yan wasan Super Eagles, kwarin gwiwa tare da ganin sun kawo kofin AFCON na 2021 zuwa Najeriya.

Shugaba Buhari, a cewar wata sanarwa da mai magana da yawunsa, Femi Adesina, ya fitar, ya yaba wa ministan wasanni da ci gaban matasa, Sunday Dare bisa kyakkyawan aikin da ya ke yi.

Buhari na wannan kalaman ne gabanin wasan da Najeriya za ta kara da kasar Tunisia a gasar cin kofin nahiyar Afrika da aka shirya gudanarwa a daren yau Lahadi a kasar Kamaru.

Da ya ke magana ta hanyar Zoom daga fadar shugaban kasa ta Villa, Abuja, shugaban ya tattauna da mai horas da Najeriya Augustine Eguavoen, da kyaftin Ahmed Musa da Amaju Pinnick, shugaban hukumar kwallon kafa ta Najeriya (NFF), da sauran su tawagar ‘yan wasan da ke kasar Kamaru.

Lokacin da tawagar Super Eagles ke ganawa shugaba Buhari.

Shugaba Buhari da ya ambaci sunayen biyu daga cikin ‘yan wasan, Kelechi Iheanacho da Moses Simon, ya bukaci Super Eagles da su ci gaba da faranta wa ‘yan Najeriya rai, ba wai kawai ta lashe wasan zagaye na biyu ba, amma a karshe su dauke kofin.

Shugaban ya ce: “Ku na yi wa Najeriya alfahari. Ku na cin nasara. Da fatan za a ci gaba da yin nasara. Gwamnatin Tarayya ta na ba ku goyon baya, kuma na ce na gode wa dukkan ma’aikata da ’yan wasa..Da fatan za a ci gaba da yi wa kasa alfahari.” In ji Buhari.

Continue Reading

Trending