Connect with us

Ƙasashen Ƙetare

Mutumin da ya bankawa majalisar dokokin Afrika ta Kudu ya gurfana a kotu

Published

on

Kasar Afrika ta Kudu na tuhumar mutumin da ya bankawa majalisar dokokin kasar wuta, a matsayin dan ta’adda.

A na tuhumar wanda a ke zargin a wata gobara da ta kone wasu sassan ginin majalisar dokokin kasar Afirka ta Kudu mai shekaru 138 da haihuwa.

Mutumin ya gurfana a gaban kotu kan karar da jami’an kasar su ka bayyana a matsayin wani hari ga dimokradiyyar kasar.

An tuhumar, Zandile Mafe mai shekaru 49 da laifin kona majalisar, sakamakon gobarar da ta tashi a ranar 2 ga watan Janairu, amma an kara tuhumar sa da laifin ta’addanci, saboda shima an kama shi da wani abu mai fashewa, in ji mai gabatar da kara.

Gobarar ta sa rufin sabon bangaren ginin ya ruguje, sannan kuma ya lalata tsohon ginin na Wing, tun a shekarar 1884, lokacin da  ke karkashin mulkin mallaka na Burtaniya.

An dage shari’ar har zuwa ranar 11 ga watan Fabrairu, kuma Mafe ya bayar da umarnin a tsare shi a cibiyar kula da masu tabin hankali, bayan rokon da majalisar tsaronsa ta yi masa na cewa yana fama da tabin hankali.

Ƙasashen Ƙetare

Sojoji Sun yi juyin Mulki a Gabon

Published

on

Sojoji sun bayyana a gidan talabijin na kasar Gabon tare da sanar da karbi mulki.

Sun ce sun soke sakamakon zaben da ka gudanar ranar Asabar, inda aka ayyana shugaba Ali Bongo a matsayin wanda ya lashe zaben.

Hukumar zaben ta ce Mr Bongo ya samu nasara ne da kasa da kashi biyu bisa uku na kuri’un da aka kada a zaben da ‘yan adawa suka ce an tafka magudi.

Sun Kuma ce Hambarar da shi zai kawo karshen mulkin shekaru 53 da iyalan gidansu ke yi a Gabon.

Sojoji 12 ne suka bayyana a gidan talabijin dake sanar da soke sakamakon zaben tare da rusa dukkan hukumomin kasar.

Daya daga cikin sojojin ya fada a tashar talabijin ta Gabon 24 cewa, “Mun yanke shawarar kare zaman lafiya ta hanyar kawo karshen mulkin da ake yi a yanzu.”

Mr Bongo ya hau karagar mulki lokacin da mahaifinsa Omar ya rasu a shekara ta 2009.

Continue Reading

Ƙasashen Ƙetare

Sojoji sunyi juyin Mulki a jamhuriyar Nijar

Published

on

Rahotanni daga jamhuriyar Nijar na cewa Sojojin Kasar sun yi juyin Mulki, tare da sanar da kawo karshen mulkin shugaba Muhammad Bazum.

Cikin sanarwar da suka bayar a gidan telebijin din Kasar, jagoran tawagar sojojin Kanal Amadu Abdramane yace “mun kawo karshen mulkin shugaba Muhammad Bazum tare da karbe dukkanin Wani Iko”.

Sojojin dai sun bayar da dalilin halin rashin tabbas da Kuma Matsin tattalin arziki a kasar.

Tuni dai sojojin suka garkame dukkanin iyakokin Kasar tare da Sanya dokar takaita zirga zirga daga karfe 10 na dare zuwa 6 na safe.

Tun a safiyar laraba ne dai aka wayi gari da fara wancan yunkuri, Wanda yanzu haka ta tabbata, Kasar Nijar na hannun sojoji, Wanda shi ne Karo na hudu ana gudanar da juyin mulkin a jamhuriyar Nijar.

Continue Reading

Ƙasashen Ƙetare

An tsaurara tsaro a fadar shugaban Kasar Nijar

Published

on

Rahotanni daga Jamhuriyar Nijar, na nuni da cewa dakarun da ke gadin fadar shugaban ƙasa sun rufe duk wata hanyar shiga fadar a wani lamari da ba a kai ga ganowa ba.

Sai dai rahotanni na cewa yanzu haka wasu daga cikin tsofaffin shugabannin ƙasar ta Nijar na tattaunawa da sojojin domin sasanta lamarin.

Karin bayani nan tafe….

Continue Reading

Trending