Connect with us

Ilimi

Gwamnatin Kano ta kulla yarjejeniya da kasar Saudiyya a fannin ilimi

Published

on

Gwamnatin jihar Kano ta amince da wata yarjejeniya tsakanin Kano da Madina Academy da ke kasar Saudiyya, domin horar da malamai 5,000 a Madina.

Kwamishinan yada labarai, Muhammad Garba ne ya sanar da hakan a yayin ganawa da manema labarai kan sakamakon taron majalisar zartarwar jihar na jihar.

Gwamnatin za ta dauki nauyin bayar da tikitin dawowar jirgi da biza da alawus na horo ga rukunin farko na malamai 50 da za su halarci babban horo a Madina kafin watan Ramadan.

Gwamnatin ta kuma amince da fitar da Naira miliyan 94.9 domin saukaka matsugunin shagunan haya da gareji a kasar Saudiyya na shekarar 2020 da 2021.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a Reply

Ilimi

Ya kamata mu san tarihin yankunan mu – Dagacin Zawaciki

Published

on

Dagacin garin Zawaci dake yankin karamar hukumar Kumbosto, Mallam Abdulkadir Mu’azu, ya ce, kamata al’umma su kara himma wajen sanin tarihin garinsu, domin mahimmancin da hakan ya ke dashi.

Mallam Abdulkadir ya bayyana hakan ne a yayin taron kaddamar da littafin tarihin garin Zawaciki, wanda wani matashi mai suna Abubakar Yahuza Yakubu ya rubuta, wanda a ka gudanar cikin dakin taro na Islamic Center a ranar Asabar din nan.

Da ya ke nasa jawabin marubucin littafin Abubakar Yahuza Yakubu, bayyana dalilan da ya ce, ya rubuta littafin tarihin ne, domin mahimmancin da hakan yake dashi.

Wakilinmu Hassan Mamuda Ya’u da ya samu damar halartar taron ya rawaito mana cewar, alumma da dama ne suka samu damar halartar taron, kuma ciki har da tsohon shugaban karamar hukumar Kumbosto Kabiru Ado Panshekara.

Continue Reading

Ilimi

Karancin tallafawa makarantun Islamiyya ya kan haifar da matsala – Wakilin Arewa

Published

on

Wakilin Arewa dake cikin birnin Kano, Sayyadi Muhammad Yola ya ce, karancin rashin taimakon da masu hannu da shuni ke yi ga makarantun Islamiyya, yakan kawo tabarbarewar tarbiyar matasa a halin yanzu.

Sayyadi Muhammad ya yi wannan jawabin ne a yayin saukar karatun Al-kur’ani mai girma na makarantar, Subulussalam Kur’an Islamiyya ta gudanar cikin unguwar kofar ruwa na dalibai 204.

Da ya ke nasa jawabin shugaban makarantar Malam Anas Mahamud Madabo, ya ce, sau tari sukan fuskanci kalubale ta wajen iyayen dalibai, musamma ma wajen karancin biyan kudin makarantar, domin haka ya ke kira a garesu da su kara himma wajen biyan.

Wakiliyar mu, Aisha Ibrahim Abdul, ta rawaito cewar a cikin daliban da su ka yi saukar akwai matan aure guda Arba’in da Biyu.

Continue Reading

Ilimi

Ilimi: Mawadata ku tallafawa karatun matasa – Alhaji Ahmed Idris

Published

on

Gidauniyar Al’ihsan a jihar Kano, ta yi kira ga manyan ƙasar da masu hannu da shuni da su rinka tallafawa matasa tare da ɗaukar nauyin karatunsu a jami’o’i ma su zaman kansu.

Babban Akanta Janar na ƙasa, Alhaji Ahmed Idris ne ya bayyana hakan lokacin da ya ke baiwa matasa guda talatin takarda daukar nauyin karatunsu a wata jami’a mai zaman kanta wato Khadija Majiya da ke garin Majiya a jihar Jigawa.

Alhaji Ahmed Idris ya ce,”Samarwa da matasa da guraben karatu a makarantu ma su zaman kansu zai kawo ci gaba a cikin ƙasar nan domin samin saukin cunkoson da a ke samu a jami’o’in gwamnati”.

Haka zalika ya kuma ja hankalin ma su hali a ƙasar nan da su kalli halin da talakawa ke ciki ta yadda basa iya samun damar guraben karatu a jami’o’in ƙasar nan wani lokacin ma idan mutum ya samu kuɗin da zai biya, domin yin karatun yakan gagara dan haka ya kamata masu hannu da shunin su rinka ɗaukar nauyin ƴaƴan talakawa wajan karatu a ƙasar nan.
Alhaji Ahmed Idris ya kuma ce,”Ina fatan wannan ɗliban guda talatin da a ka baiwa gurbin karatun za su gudanar da karatun su yadda ya dace da kuma yin anfani da abin da su ka koya”.

Taron tallafawa matasan da guraben karatun ya sami halattar manyan malamai da dama daga nan Kano da ma wajanta har da shugaban makarantar mai zaman kanta inda matasan za su gudanar da karatun su.

Wakiliyar mu Aisha shehu Kabara ta rawaito cewa, Alhaji Ahmad Idris, ya kuma ce zai biyawa kowanne su sama da miliyan daya har su kammala karatun su tare da baiwa kowane dubu dari duk shekara, domin kula da hidimar karatun.

Continue Reading

Trending