Connect with us

Labarai

Mahaifiyar mai horas da kasar Italiya ta tuhume shi a kan kin kiran Balotelli

Published

on

Mahaifiyar mai horas da kasar Italiya, Roberto Mancini ta tuhumi mai horaswar bisa kin kiran dan wasa Mario Balotelli, wanda hakan ta ke ganin shi ne musababbin hana kasar Italiya zuwa gasar cin kofin duniya wanda za a yi a kasar Qatar a shekarar nan.

Da take magana a gidan rediyon Rai 1 a ranar Juma’a, Marianna Puolo, ta ce, da ya kirawo Balotelli da Mancini zai ci gajiyar ikon sa, kuma shigarsa zai iya hana abin da ya faru a Palermo, inda Italiya ta sha kashi a hannun Arewacin Macedonia da ci 1-0.

Balotelli, matashin da ya taba zama abin mamaki wanda a yanzu ya na taka leda a Adana Demirspor a gasar Super Lig ta Turkiyya, ya dade ya na sha’awar Mancini, tun daga zamansu na dan wasa da koci a Inter da Manchester City.

Yanzu mai shekaru 31, Balotelli ya samu kiran zuwa sansanin atisayen Italiya a farkon wannan shekarar. Italiya dai ba ta buga wasa ba tun bayan da babban kociyan kungiyar Mancini ya buga masa wasa sau uku a shekarar 2018, wanda hakan ya biyo bayan rashin halartar tawagar kasar na tsawon shekaru hudu.

“Mu ke da rike da wasan a hannunmu, amma harin bai yi kyau ba, wanda ya janyo a ka zura mana kwallo,” in ji mahaifiyar Mancini.

Hangen Dala

Rashin wuta: Muna cikin mawuyacin hali – al’ummar Kano, Katsina da Jigawa

Published

on

Al’ummar jihohin Kano, katsina da Jigawa na fuskantar yanayi mara dadi, Sakamakon karancin samun wutar lantarki daga hukumar KEDCO.

Al’ummar jihohin sun ce iya sa’o’i uku kacal suke samun wutar, wanda hakan ke haifar musu da nakasu a harkokin kasuwancin su.

Wani bincike da jaridar Daily Trust tayi ta ambato yadda masu kananan masana’antu irin su Walda, Cajin Waya, Kankara da masu sana’ar dinki da dai sauran kananan sana’o’i dake amfani da wutar lantarki sun shiga mawuyacin hali.

Kazalika rashin wutar ya shafi hatta bangaren ruwan sha, dama masu sana’ar sayar da Ruwa a irin yankunan Hotoro da sauran irin wuraren dake sayen ruwa, Inda yanzu haka ruwan yayi tashin gwauron zabi a kowace jarka.

Koda dai ana ta bangaren hukumar rarraba hasken wutar lantarkin me kula da shiyyar Kano, Katsina da Jigawa KEDCO sun nemi afuwar al’umma.

Idan za’a tuna dai a makon jiya ne Ministan Wutar lantarki yace ‘yan Nigeria Miliyan 150 na samun wadatacciyar wutar lantarki.

Sai dai kuma a jihohi irin su Kano, Katsina da Jigawa na bayyana damuwa kan karancin Wutar, Inda suka ce bata wuce ta sa’o’i uku suke samu a kowa ce rana.

Continue Reading

Hangen Dala

Rashin wuta:- Muna cikin mawuyacin hali – al’ummar Kano, Katsina da Jigawa

Ci gaba ba ya zuwa sai an samu haɗin kan al’umma – Dagacin Ja’en

Published

on

Dagacin garin Ja’en da ke ƙaramar hukumar Gwale a jihar Kano, Alhaji Isma’il Sa’ad Usman, ya ce hadin kai ne kaɗai zai kawo ci gaba ga kowa ce irin al’umma.

Dagacin ya bayyana hakan ne Jim kaɗan bayan wani taron masu Ruwa da tsaki na Garin Ja’en, wanda Hakimin Gundumar Ɗorayi Barde Kerarriya Alhaji Shehu Kabir Bayero ya shirya, aka gudanar a yankin Ja’en a ƙarshen makon da ya gabata.

“Dukkanin wani ci gaba ba ya zuwa har sai an samu haɗin kan kowa ne bangare na al’umma, “in ji Dagacin”.

Wakilin Dala FM Kano, Ahmad Rabi’u Ja’en ya ruwaito cewa, taron ya samu halartar dukkanin bangarori, na unguwannin Ja’en, da suka haɗar da kungiyar mafarauta da maharba dabma kungiyar malaman makaranta.

Continue Reading

Trending