Connect with us

Labarai

Rauni: Ɗan wasan Arsenal ba zai buga sauran kakar wasa ta bana ba

Published

on

Ana sa ran Kieran Tierney ba zai buga sauran kakar wasa ta bana ba, bayan da Arsenal ta tabbatar da cewa, dan wasan bayan na bukatar tiyata a gwiwa.

Tierney bai buga wasan ranar litinin, bayan da Crystal Palace ta doke ta da ci 3-0.

Dan wasan baya na Scotland ya ji ciwo a gwiwarsa ta hagu bayan atisaye a ranar Alhamis din da ta gabata, kuma kociyan kungiyar Mikel Arteta, ya amince bayan rashin nasarar da Gunners ta yi a Selhurst Park cewa raunin “bai yi kyau ba”.

Labarai

Za mu fara ɗaukar mataki akan masu zance a cikin Mota – Hukumar Hisbah

Published

on

Hukumar Hisbah ta jihar Kano ta ce ta shirya tsaf wajen ganin ta kawo ƙarshen zancen da wasu Masoya suke yi a cikin Motoci, domin daƙile ɓarnar da ke yaɗuwa ta hakan a wasu lokutan.

Mataimakin babban kwamandan hukumar Hisbah a Kano, Dr. Mujahideen Aminudden, ya bayyana hakan ne yayin zantawar sa da Dala FM Kano, a ranar Juma’a 18 ga watan Afrilun 2025.

 

“Ɗaukar wannan matakin ya zama dole kasancewar lamarin na neman ya zamar wa al’ummar jihar Kano alaƙakai, “in ji shi”.

Dakta Mujahidden ya kuma yi kira ga iyaye da su sanya idanu kan tarbiyyar ƴaƴan su, tare da rage buri wanda hakan ka iya kawo ƙarshen taɓarɓarewar tarbiyyar ƴaƴan nasu.



Continue Reading

Hangen Dala

Kofar APC a bude take ga masu shiga – Abdullahi Abbas

Published

on

Jamiyyar APC a Jihar Kano tace Kofar ta a bude take ga dukkanin masu son shigowa jamiyyar.

 

Shugaban jamiyyar na Kano Hon Abdullahi Abbas ne ya bayyana hakan yayin wani taron manema labarai.

 

Abbas yace labarin dake yawo cewa akwai wadanda ke Shirin shigowa jamiyyar, su sani Kofar APCn a bude take tare da maraba ga dukkanin wadanda zasu shigo.

 

Koda dai Abdullahi Abbas yace shigowa APC ba zai hana tuhuma kan zargin cin hanci da rashawa ba, koma kaucewa hukumar EFCC da ICPC.

 

A baya bayan nan ne dai aka rinka yada cewa mabiya jamiyyar NNPP kwankwasiyya na Shirin shiga jamiyyar APC tare da madugun ta Sanata Rabiu Musa Kwankwaso.



Continue Reading

Hangen Dala

Gwamnoni sun bukaci a kawo karshen matasalar Filato

Published

on

Ƙungiyar Gwamnonin kasar nan (NGF) ta buƙaci jagororin jihar Plateau su haɗa kan al’ummar jihar mai yawan al’adu da ƙabilu domin dakatar da kashe-kashen mutane da ake yawan samu a jihar.

 

Shugaban ƙungiyar, wanda kuma shi ne gwamnan jihar Kwara – Abdulrahman Abdulrazaq, ne ya bayyana haka ranar Alhamis lokacin da ya kai ziyarar jaje.

 

“Muna kira da jagorori da masu faɗa a ji a duka garuruwan jihar da sauran fannoni da su haɗa hannu da gwamnan jihar wajen haɗa kan al’ummar jihar tare da dawo da zaman lafiya mai ɗorewa”, in ji shugaban ƙungiyar ta NGF.

 

“Ya kamata shugabannin matasan al’umomin jihar su fito su haɗa kai wajen yin Allah wadai da tashin hankalin da ake samu a jihar, muna kira da a riƙa sasanta duka matsalolin da suka taso ta hanyar tattaunawa da lalama tare da girmama juna,” a cewar Abdulrahman Abdulrazaq.

 

Fiye da mutum 100 ne aka kashe cikin mako biyu da suka gabata, lokacin da wasu mahara suka kai hari a wasu garuruwan ƙananan hukumomin Bokkos da Bassa a jihar.

 

A ranar Talata ne babban sifeton ƴansandan ƙasar, Kayode Egbetokun ya ziyarci jihar inda ya sha alwashin kamo waɗanda suka ƙaddamar da kashe-kashen, da ya bayyana da na rashin imani, domin hukunta su.



Continue Reading

Trending