Connect with us

Wasanni

Dan wasan Manchester City Zinchenko ya koma Arsenal

Published

on

Arsenal ta kammala daukar dan wasan tsakiya na kasar Ukraine, Oleksandr Zinchenko, daga Manchester City.

Zinchenko wanda ya buga wasanni da dama, ya buga wasanni 15 a kakar da a ka kammala a Firemiriyar kasar Ingila.

Zinchenko mai shekara 25 ya koma Arsenal ne daga Manchester City, bayan da kungiyar ta je kasar Amurka, wanda yarjejeniyar da ta kai fan miliyan 30.

Shi ne dan wasa na biyu da ya koma Arsenal daga Manchester City a bazarar nan. In ji BBC.

Tuni Gabriel Jesus ya koma Emirates kan fan miliyan 45, inda har ma ya ci mata ƙwallo wasan sada zumunta.

Manyan Labarai

Ƴan Manchester United basu cancanci a basu albashin mako-mako ba – Rio Ferdinand

Published

on

Tsohon dan wasan kungiyar kwallon kafa ta Manchester United, Rio Ferdinand ya ce, ‘yan wasan kungiyar, ba su cancanci albashin mako-mako da suke samu daga kungiyar ba.

Ya ce ‘yan wasan sun riga sun rasa kwarin gwiwa a kan sabon koci Erik ten Hag.

Wannan rashin nasara na nufin Manchester United ta yi rashin nasara a wasanni biyu na farko a gasar Premier bayan da ta doke Brighton da ci 2-1 a ranar farko ta gida.

Kalaman Ferdinand na zuwa ne a lokacin da Josh Dasilva da Mathias Jensen da Ben Mee da Bryan Mbeumo suka ci Manchester United ta girgiza ta a filin wasa na Community.

Continue Reading

Manyan Labarai

Cucurella ya koma Chelsea daga Brighton

Published

on

Ɗan wasan gefe na baya, Marc Cucurella, ya sauya sheka daga Brighton zuwa Chelsea a kan kudi fama miliyan 65.

Bayan kammala sauya sheka, Cucurella ya ce: “Na yi farin ciki kwarai da gaske. Wannan babbar dama ce a gare ni na shiga daya daga cikin kungiyoyi mafi kyau a duniya kuma zan yi aiki tukuru don jin dadi a nan kuma in taimaka wa kungiyar.”

Sabon shugaban Chelsea, Todd Boehly, ya yi farin cikin samun matsaya akan ɗan wasan.

Ya kara da cewa: “Marc fitaccen dan wasan baya ne mai inganci a gasar Premier kuma yana kara karfafa ‘yan wasanmu da za su shiga sabuwar kakar wasa.”

“Muna ci gaba da aiki a ciki da wajen filin wasa, kuma muna farin cikin cewa, Marc zai kasance wani bangare na yanzu da kuma nan gaba a Chelsea.

Cucurella, mai shekaru 24, ya kasance tauraro, tun zuwansa daga Getafe watanni 12 da suka gabata, inda ya lashe kyautar gwarzon dan wasan kungiyar.

Continue Reading

Labarai

Kwamishinan Matasa da Wasanni ya rasu a wani hatsari daga Yobe zuwa Kano

Published

on

Rahotanni sun bayyana cewa, Kwamishinan matasa da wasanni na jihar Yobe, Hon. Goni Bukar ya rasu a wani hatsarin mota da ya rutsa da su a hanyar Damaturu zuwa Kano.

Marigayin wanda aka fi sani da Bugon, kamar yadda wata majiya mai tushe ta bayyana, ya rasu ne a daren ranar Talata a hanyarsa ta zuwa jihar Kano.

Tun da farko dai Marigayi Kwamishinan, ya halarci sallar jana’izar daya daga cikin mukarrabansa da aka yi a Damaturu babban birnin jihar Yobe kafin ya wuce Kano. In ji Daily Post.

Marigayi Goni Bukar ya kasance tsohon dan majalisar wakilai mai wakiltar Bursari/Geidam/Yunusari a jihar Yobe.

An shirya gudanar da sallar jana’izar kwamishinan wasanni da ya rasu ranar Laraba da misalin karfe 11:30 na safe a masallacin Yobe na Islamic Center dake Damaturu.

Sakon karshe na Bugon akan matsayin sa na WhatsApp da karfe 11:03 na safe, da ya wallafa a Talata:

“Wannan rayuwa da duk abin da ke cikinta, na ɗan lokaci ne”.

Continue Reading

Trending