Connect with us

Siyasa

Wike ya tuhumi shugaban jam’iyyar PDP da karbar Naira Biliyan 100 a hannun Gwamna

Published

on

Gwamna Nyesom Wike na jihar Ribas, ya sake yin wani sabon zarge-zarge a kan jam’iyyar PDP da kuma shugaban jam’iyyar Iyorchia Ayu na kasa.

Wike ya zargi Ayu da karbar Naira miliyan 100 da Naira biliyan 1 daga hannun wani gwamna.

A wata tattaunawa da ya yi da manema labarai a ranar Juma’a, gwamnan ya kalubalanci shugaban jam’iyyar PDP na kasa da ya karyata zargin cin hanci da ake yi masa.

A cewar Wike, “Ba wai kawai na fito na yi magana ba, bari Ayu ya fito ya ce bai karbi Naira biliyan 1 ba. Bari in gaya muku Ayu ya karbi Naira miliyan 100 daga hannun wani gwamna.

“Idan ba don soyayyar wannan jam’iyyar ba, idan muka saki abin da muke da shi, ‘ya’yan Ayu za su je wurinsa su ƙaryata shi.”

Wike ya kuma yi alƙawarin zubar da ƙarin zarge-zarge idan “an tura mu bango.”

Gwamnan ne ke jagorantar ‘yan PDP na neman a tsige Ayu.

Sau da yawa, Wike ya zargi Ayu da ayyukan zamba.

Ya kuma jaddada kiran sa kan cewa dan takarar shugaban kasa na PDP shugaban kasa ba zai iya fitowa daga yanki daya ba.

Hangen Dala

Take hakki:- Matakin Amnesty game da kama wasu ‘yan jarida a Kano

Published

on

Ƙungiyar kare haƙƙin ɗan adam ta Amnesty International, ta yi ala-wadai da cin zarafin ‘yan jarida biyu a Kano, wato mawallafin jaridar kano Times, Buhari Abba da kuma Isma’il Auwal.

Cikin sanarwar sa Ƙungiyar ta wallafa a shafin ta na facebook,
ta ce babu shakka abin da rundunar ‘Yansandan jihar Kano ta yi bisa umarnin Kwamishinan yaɗa labaran jihar, Ibrahim Waiya abin takaici ne.

Rundunar ‘Yansandan jihar Kano dai ta gayyaci Buhari Abba zuwa sashin binciken manyan laifuka (CID) ne, harma kuma ta tsare shi na tsawon awanni.

Kuma dai ana tuhumar mutanen biyun ne da zargin ɓata sunan kwamishinan, ta hanyar wani ra’ayi da jaridar ta wallafa wanda Isma’il Auwal ya rubuta.

Kungiyar ta Amnesty ta ce duk ba zata lamunci duk wani yunƙuri na takewa waɗannan ‘Yan jarida haƙƙinsu ba.

A ƙarshe ƙungiyar taja hankalin gwamantin kano da kuma rundunar ‘Yansandan jihar, da su guji yunƙurin daƙile ‘yancin faɗin albarkacin baki.

Continue Reading

Baba Suda

Gwamnatin Kano ta musanta labarin da ke cewa za ta saka kafar Wando daya da Sojojin Baka

Published

on

Gwamnatin jihar Kano ta musanta labarin da ke yawo na cewa za ta saka kafar wando daya da Sojojin Baka.

 

Kwamishinan yada labaran jihar Kwamred Ibrahim Waiya shi ne ya bayyana hakan lokacin wani taron karawa juna sani da hukumar kula da kafafen yada labarai NBC ta shirya a yau Alhamis.

 

Yace gwamnatin Kano za ta hada kai da Yan siyasa masu magana a Rediyo da aka fi Sani da Sojojin Baka, domin tsaftace harkokin siyasar Kano.

 

Haka kuma kwamishinan ya musanta labarin da ke cewa Gwamnatin Kano za ta saka kafar wando daya da Sojojin Baka.

 

Kwamishina Waiya ya kuma ce za su hada kai da kafafen yada labarai domin Kara kawo tsafta a harkokin siyasar Kano.

Continue Reading

Labarai

Tsohon shugaban majalisar Dattawa Ahmad Lawan ya ƙaryata ficewar sa daga APC zuwa SDP

Published

on

Tsohon shugaban majalisar Dattawa Ahmad Lawan, ya musanta wata jita-jita da ake yaɗawa kan cewar ya fice daga cikin jam’iyyar APC mai mulki a ƙasa, zuwa SDP, al’amarin da ya ce bashi da tushe ballantana makama.

A cikin wata sanarwar da mashawarci na musamman ga tsohon Sanatan a kafafen yaɗa labarai Ezrel Tabiowo, ya fitar a jiya Lahadi, ta ce jita-jitar da ake yaɗawa na cewar Ahmad Lawan ya fice daga jam’iyyar ta APC, ƙarya ce tsagwaronta.

Jaridar Daily trust ta ruwaito cewar, sanarwar ta kuma ce, har yanzu Ahmad Lawan ɗan Jam’iyyar APC ne, kuma yana biyayya ga jam’iyyar, wadda yake alfahari da ita.

Continue Reading

Trending