Connect with us

Siyasa

Ban taba karbar biliyan 1 daga hannun kowa ba -Shugaban Jam’iyyar PDP

Published

on

Shugaban jam’iyyar PDP na kasa, Sanata Iyorchia Ayu ya musanta karbar Naira biliyan 1 daga hannun kowa kamar yadda gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike ya yi ikirari, yana mai gargadin wadanda suka fusata da su bar iyalansa daga cikin rigimar.

Ayu ya karyata ikirarin Wike yayin da yake amsa tambayoyi game da zargin da ake masa sannan ya kuma yi alkawarin cewa za a gabatar da bayanin asusun jam’iyyar ga mambobin jam’iyyar nan ba da jimawa ba.

Shugaban PDP na kasa ya ce a matsayinsa na uban jam’iyyar ya yanke shawarar yin shiru domin zaman lafiya ya yi mulki.

Ayu ya kuma yi kira ga daukacin ‘ya’yan jam’iyyar da su bar iyalansa da cewa. “Na ga ya kamata in karfafa sulhu. Amma inda ya shafi mutuncina, wanda har ’yan uwana ake kawo su cikin wasa.

“Ina kira ga mutanen da suka fusata su daina yunkurin bata min suna ko shigar da iyalina cikin harkokin jam’iyya.

” Ban taba karbar biliyan 1 daga hannun kowa ba. Kuma miliyan 100 da daya daga cikin gwamnonin ya bayar, an yi amfani da shi bisa ga adalci wajen abin da aka bayar”.

Hangen Dala

Lauyoyin gwamnatin Kano sun bukaci a kamo Ganduje

Published

on

Babbar kotun jaha mai lamba 7 karkashin jagorancin mai sharia Amina Adamu ta sanya karfe biyu da rabi na ranar yau dan bayyana matsayarta akan batun gurfanar da tsohon gwamnan kano Dr Abdullahi Umar Ganduje da mai dakinsa da wasu mutane.

A zaman kotun na yau lauyoyin gwamnatin jaha sun bayyana wa kotun cewa an sadar da sammace ga wadanda ake kara ta hanyar kafafen yada labarai kamar yadda kotun ta yi umarni tun a baya amma wadanda ake kara basu samu damar halartar kotun ba dan haka ya roki ko dai a kamo su ko kuma kotun ta ci gaba duk da cewar basa gaban kotun.

Sai dai lauyan wanda ake kara na 6 barrister Nuraini Jimo SAN ya yi suka inda ya bayyana cewar kotun ta dakata tun da sun daukaka kara ya kuma bayyana cewar kotun bata da hurumi sannan kunshin tuhume-tuhumen yana dauke ta kura-kurai.

Kotun zata bayyana matsayarta a yau da rana.

Tun da farko gwamnatin kano ta yi karar Ganduje da mutane 6 bisa zargin almundahana akan kudi sama da Naira Biliyan 4 da aka yi zargin sun sayarda wasu filaye sun raba kudin.

Continue Reading

Labarai

Da Dumi Dumi:- EL Rufai ya kai karar majalisar dokoki

Published

on

Tsohon Gwamna jahar Kaduna Mal. Nasir elrufai ya Maka majalisar Dokokin jahar Kaduna a gaban Kotu a bisa bata Masa Suna da majalisar tayi na cewa Gwamnatin sa ta sace kudaden jahar da Suka naura naira miliyan dubu Dari Hudu.

Tsohon Gwamna ya shigar da karar ce, a Gaban babbar kotun taraiyya dake NDA Kaduna a safiyar Laraban nan 26 ga watan Yuni 2024.

Inda ya bukaci Kotun data tursasa majalisar ta bashi hakuri a bainar jama’a, sakamakon Kazafin da Yan majalisan Suka yi masa da mukarraban Gwamnatinsa data gabata.

 

Karin bayani na nan tafe….

Continue Reading

Siyasa

Zauren jam’iyyun haɗin kan kasa IPAC sun cire shugaban jam’iyyar LP na Kano Abdullahi Raji daga cikin tafiyar su 

Published

on

Sakataren zauren jam’iyyun haɗin kan kasar nan, IPAC na ƙasa reshen jihar Kano, kuma shugaban jam’iyyar APM na Kano Honarable Nuhu Idris, ya ce sun cire shugaban jam’iyyar LP na jihar Kano Abdullahi Raji daga cikin tafiyar su ta IPAC, baki ɗaya.

Sakataren na IPAC, Nuhu Idris ya ce sun dauki wannan mataki ne bisa yadda Rajin ke amfani da kungiyar CUPP, da rusassun jam’iyyun kasar nan suka samar a baya, a dan haka, duk wata jam’iyyar dake da rijista a yanzu na ƙarƙashin IPAC.

Ya kuma ce dokar da ta kafa IPAC, ba ta bai wa ɗan kowacce jam’iyya damar shiga hurumin wata jam’iyyar ba kamar yadda Rajin ke ƙoƙarin yi a rikicin dake faruwa a jam’iyyar APC a nan jihar Kano.

Shugaban jam’iyyar APM, ɗin Honarable Nuhu Idris, ya ce sun cire Rajin daga tafiyar ta IPAC ne, sakamakon wata sanarwa da ya fitar, ya ce, ka da hukumar zaɓe INEC, ta yi watsi da shugaban mazaɓar Ganduje, wanda hakan ba dai-dai ba ne a dokance, dan haka, suka fitar da shi daga cikin tafiyar tare da sanar da shugabancin jam’iyyar sa na kasa.

Continue Reading

Trending