Connect with us

Siyasa

APC ce za ta lashe zaben 2023 – Buhari

Published

on

Shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya bayyana cewa, jam’iyyar All Progressives Congress (APC) za ta lashe zaben shugaban kasa a 2023.

Buhari ya ce, APC ta yi sa’ar samun Tinubu a matsayin dan takararta na shugaban kasa.

Ya yi magana ne a kasar Birtaniya yayin da ya ke mayar da martani kan yiwuwar APC ta lashe zaben shugaban kasa a 2023.

Da aka tambaye shi kan yiwuwar APC na rashin yin nasara a 2023, Buhari ya ce: “Mene ne damar jam’iyyata ba za ta ci zabe ba? Za mu ci zabe.

“Tinubu, dan takarar shugaban kasa, sanannen dan siyasa a kasar nan, ya kasance gwamna na wa’adi biyu a jihar Legas, jihar da ta fi kowa arziki kuma jihar da aka fi ziyarta.

“Don haka, ina ganin jam’iyyar ta yi sa’ar samun shi ya zama dan takara.”

A watan Yuni, Tinubu ya zama dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC, bayan ya doke mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo; Shugaban majalisar dattawa Ahmad Lawan da tsohon ministan sufuri, Rotimi Amaechi.

Tsohon gwamnan jihar Legas ya samu kuri’u 1,271, inda ya doke abokin hamayyarsa Amaechi wanda ya samu kuri’u 316.

Baba Suda

Gwamnatin Kano ta musanta labarin da ke cewa za ta saka kafar Wando daya da Sojojin Baka

Published

on

Gwamnatin jihar Kano ta musanta labarin da ke yawo na cewa za ta saka kafar wando daya da Sojojin Baka.

 

Kwamishinan yada labaran jihar Kwamred Ibrahim Waiya shi ne ya bayyana hakan lokacin wani taron karawa juna sani da hukumar kula da kafafen yada labarai NBC ta shirya a yau Alhamis.

 

Yace gwamnatin Kano za ta hada kai da Yan siyasa masu magana a Rediyo da aka fi Sani da Sojojin Baka, domin tsaftace harkokin siyasar Kano.

 

Haka kuma kwamishinan ya musanta labarin da ke cewa Gwamnatin Kano za ta saka kafar wando daya da Sojojin Baka.

 

Kwamishina Waiya ya kuma ce za su hada kai da kafafen yada labarai domin Kara kawo tsafta a harkokin siyasar Kano.

Continue Reading

Labarai

Tsohon shugaban majalisar Dattawa Ahmad Lawan ya ƙaryata ficewar sa daga APC zuwa SDP

Published

on

Tsohon shugaban majalisar Dattawa Ahmad Lawan, ya musanta wata jita-jita da ake yaɗawa kan cewar ya fice daga cikin jam’iyyar APC mai mulki a ƙasa, zuwa SDP, al’amarin da ya ce bashi da tushe ballantana makama.

A cikin wata sanarwar da mashawarci na musamman ga tsohon Sanatan a kafafen yaɗa labarai Ezrel Tabiowo, ya fitar a jiya Lahadi, ta ce jita-jitar da ake yaɗawa na cewar Ahmad Lawan ya fice daga jam’iyyar ta APC, ƙarya ce tsagwaronta.

Jaridar Daily trust ta ruwaito cewar, sanarwar ta kuma ce, har yanzu Ahmad Lawan ɗan Jam’iyyar APC ne, kuma yana biyayya ga jam’iyyar, wadda yake alfahari da ita.

Continue Reading

Hangen Dala

Lauyoyin gwamnatin Kano sun bukaci a kamo Ganduje

Published

on

Babbar kotun jaha mai lamba 7 karkashin jagorancin mai sharia Amina Adamu ta sanya karfe biyu da rabi na ranar yau dan bayyana matsayarta akan batun gurfanar da tsohon gwamnan kano Dr Abdullahi Umar Ganduje da mai dakinsa da wasu mutane.

A zaman kotun na yau lauyoyin gwamnatin jaha sun bayyana wa kotun cewa an sadar da sammace ga wadanda ake kara ta hanyar kafafen yada labarai kamar yadda kotun ta yi umarni tun a baya amma wadanda ake kara basu samu damar halartar kotun ba dan haka ya roki ko dai a kamo su ko kuma kotun ta ci gaba duk da cewar basa gaban kotun.

Sai dai lauyan wanda ake kara na 6 barrister Nuraini Jimo SAN ya yi suka inda ya bayyana cewar kotun ta dakata tun da sun daukaka kara ya kuma bayyana cewar kotun bata da hurumi sannan kunshin tuhume-tuhumen yana dauke ta kura-kurai.

Kotun zata bayyana matsayarta a yau da rana.

Tun da farko gwamnatin kano ta yi karar Ganduje da mutane 6 bisa zargin almundahana akan kudi sama da Naira Biliyan 4 da aka yi zargin sun sayarda wasu filaye sun raba kudin.

Continue Reading

Trending