Connect with us

Siyasa

Masu kukan na zabo musulmi mataimaki ni ‘ya’ya na da mata ta Kiristoci ne – Tinubu

Published

on

Ɗan takarar shugaban kasa a jam’iyyar APC, Bola Ahmed Tinubu, ya shaidawa shugabannin ƙungiyar Kiristoci ta kasa CAN cewa, ba zai saka batun addini a mulkinsa ba, muddin ya yi nasara a zaɓen 2023.

Tinubu ya ce, shi Musulmi ne sai dai matarsa da ‘ya’yansa duk Kiristoci ne.

Tsohon gwamnan na Legas ya faɗawa kungiyar ta CAN wadannan maganganun ne a Abuja, a kokarin nuna musu cewa, ya na tare da su kuma bambanci addini ba zai yi tasiri a shugabancinsa ba.

Batun zaɓin da Tinubu ya yi na Kashim Shettima a matsayin mataimakinsa, ya ja hankali da haifar da ce-ce-ku-ce tsakanin ‘yan kasa musamman Kiristoci da ke ganin an yi musu rashin adalci.

Sai dai Tinubu ya ce, shi burinsa shi ne kafa gwamnati mai nagarta, ba wai bisa addini ko kabilanci ko wani abin da mutum ya yarda da shi ba.

Tinubu ya ce,“Ni mutum ne da ke neman kawo sauyi a Najeriya, shi yasa na ke neman haɗin-kan kowa ba tare da nuna bambamci na addini ba, wajen kai kasar ga nasara”.

Tinubu ya yi alkawarin cewa Kiristoci za su more a mulkinsa.

Hangen Dala

Yau shugaban kasa zai dawo daga Faransa

Published

on

Bayan ziyarar aiki ta kusan mako biyu Zuwa kasar Faransa a yau litinin ake saka ran shugaban kasa zai dawo gida Nigeria.

Cikin sanarwar da hadimin shugaban kasar kan harkokin yada labarai Bayo Onanuga ya fitar ya ce kowa ne lokaci daga yanzu shugaban kasa Asuwaju Bola Tinubu zai sauka a Nigeria domin cigaban da harkokin mulkin kasar.

Continue Reading

Hangen Dala

Kofar APC a bude take ga masu shiga – Abdullahi Abbas

Published

on

Jamiyyar APC a Jihar Kano tace Kofar ta a bude take ga dukkanin masu son shigowa jamiyyar.

 

Shugaban jamiyyar na Kano Hon Abdullahi Abbas ne ya bayyana hakan yayin wani taron manema labarai.

 

Abbas yace labarin dake yawo cewa akwai wadanda ke Shirin shigowa jamiyyar, su sani Kofar APCn a bude take tare da maraba ga dukkanin wadanda zasu shigo.

 

Koda dai Abdullahi Abbas yace shigowa APC ba zai hana tuhuma kan zargin cin hanci da rashawa ba, koma kaucewa hukumar EFCC da ICPC.

 

A baya bayan nan ne dai aka rinka yada cewa mabiya jamiyyar NNPP kwankwasiyya na Shirin shiga jamiyyar APC tare da madugun ta Sanata Rabiu Musa Kwankwaso.

Continue Reading

Hangen Dala

Gwamnoni sun bukaci a kawo karshen matasalar Filato

Published

on

Ƙungiyar Gwamnonin kasar nan (NGF) ta buƙaci jagororin jihar Plateau su haɗa kan al’ummar jihar mai yawan al’adu da ƙabilu domin dakatar da kashe-kashen mutane da ake yawan samu a jihar.

 

Shugaban ƙungiyar, wanda kuma shi ne gwamnan jihar Kwara – Abdulrahman Abdulrazaq, ne ya bayyana haka ranar Alhamis lokacin da ya kai ziyarar jaje.

 

“Muna kira da jagorori da masu faɗa a ji a duka garuruwan jihar da sauran fannoni da su haɗa hannu da gwamnan jihar wajen haɗa kan al’ummar jihar tare da dawo da zaman lafiya mai ɗorewa”, in ji shugaban ƙungiyar ta NGF.

 

“Ya kamata shugabannin matasan al’umomin jihar su fito su haɗa kai wajen yin Allah wadai da tashin hankalin da ake samu a jihar, muna kira da a riƙa sasanta duka matsalolin da suka taso ta hanyar tattaunawa da lalama tare da girmama juna,” a cewar Abdulrahman Abdulrazaq.

 

Fiye da mutum 100 ne aka kashe cikin mako biyu da suka gabata, lokacin da wasu mahara suka kai hari a wasu garuruwan ƙananan hukumomin Bokkos da Bassa a jihar.

 

A ranar Talata ne babban sifeton ƴansandan ƙasar, Kayode Egbetokun ya ziyarci jihar inda ya sha alwashin kamo waɗanda suka ƙaddamar da kashe-kashen, da ya bayyana da na rashin imani, domin hukunta su.

Continue Reading

Trending