Baba Suda
Saurari shirin Baba Suda na ranar Litinin 30/09/2019
A cikin shirin Baba Suda na jiya Litinin kunji cewar wani boka ya tsinci Talatar sa a Laraba saboda ana zargin yana tsare ‘yan mata a gidan sa suyi kwana da kwanaki, wai yana basu maganin farin jinin samun mazaje.
Sannan kunji cewa ana zargin jami’an Road Safety sun hada kai da jami’an Civil Defence sun yi wa wani matashi dukan kawo wuka.
Haka zalika mun baku labarin cewa al’ummar unguwar Tudun Rubudi sun wayi gari da ganin gawar wata mata yashe cikin jini sannan kuma aka tsinci gawar ‘yarta a rijiya.
Ayi Sauraro Lafiya
Baba Suda
Matashi ya shiga hannu bisa zargin sa da yin baɗala da Akuya
Jami’an tsaron jihar Ogun na Amotekun, ta kama wani matashi mai suna Ibrahim Ismaila, bisa zargin laifin yin lalata da wata Akuya.
An kama Ismaila mai shekaru 18 a garin Ilu-Tuntun Olorunsogo, Ajowa, cikin karamar hukumar Ifo ta jihar.
Kwamandan Amotekun na jihar, David Akinremi, wanda ya bayyana hakan a ranar Talata ya ce, kama matashin ya biyo bayan karar da wani Jimoh Opeyemi ne ya yi, wanda ya ga Ismaila a lokacin da yake yin lalata da Akuyar.
Jimoh Opeyemi, ya je wajen wani gini sai ya hangi wanda ake zargin ya na amfani Akuyar.
Akinremi ya ce, Opeyemi ya ƙwarma ihu, inda ya jawo hankalin jama’a a yankin ciki har da wani jami’in Amotekun Corps, wanda ya samu nasarar cafke wanda ake zargin.
Baba Suda
Toro: Namijin Agwagwa ya shafe tsawon shekaru 13 a raye – Umaru Tunkuli
Wani matashi mai suna Umaru Yahaya mazaunin layin Kuka Sani Mai Nage (A), a jihar Kano, ya tabbatar mana da cewa Namijin Agwagwar (Toro) da ya ke kiwao ya shafe tsawon shekaru 13 ya na raye a wajen shi ba tare da ya gudu ba.
Matashin Umaru Tunkuli, ya ce a yanzu haka bay a sha’awar ya yanka wannan Toro, hasali ma ya kai shekaru 20 ya na kiwon Agwagi.
Ga tattaunawar su da wakilin mu Tijjani Alfindiki.
Baba Suda
Rahoto: Zan bayar da kudin fansa domin a dawo da Kyanwa ta – Matashi
Wani matashi a yankin unguwar Farawa dake karamar hukumar Kumbotso, Kawu Rufa’I, ya ce a kan Magen da ya ke zargin an yi masa garkuwa da an raba shi da abar kaunar shi, sakamakon yadda suka shaku da juna.
Kawu Rufa’I yacce zai dauki matakin shari’a mudum ya yi artabu da mutum da ya yi garkuwa da Magen, wanda ya bayyana cewa tun a baya sai da a ka dauke ta duk da furucin da a ka yi masa cewa za a dauke ta.
Wakilin mu Tijjani Adamu wanda ya tattauna da matashin ya aiko mana rahoto.
-
Nishadi5 years ago
Ina neman mijin aure – Rayya
-
Labarai4 years ago
Hamisu Breaker ya kai kan sa wajen ‘yan sanda
-
Nishadi5 years ago
Mansura Isah ta yi kaca-kaca da Sadiya Haruna
-
Manyan Labarai5 years ago
KAROTA: An baiwa Baffa Babba wa’adin kwanaki bakwai
-
Labarai5 years ago
Auren dan Panshekara da ba Amurkiya ya samu cikas
-
Lafiya2 years ago
Rahoto: An gano wani gida da ake gini da takardun Kur’ani da Alluna
-
Manyan Labarai5 years ago
Sabuwar damfarar da ta fito a Kano
-
Nishadi5 years ago
An gano daliban da Adam Zango ya dauki nauyin karatun su