Connect with us

Nishadi

Jarumi Shah Rukh Khan ya cika shekaru 54 a duniya

Published

on

Shah Rukh Khan mashahurin jarumi ne hakazalika fitacce a duniyar fina-finan India baki daya, baya ga haka “Furodusa” ne, wato mai shirya fina-finai.

Jarumi Sharukhan Ba za’a kirashi da Dogo ba, Hakazalika ba’a Kirashi da gajere ba, an haifi jarumin a ranar 2 ga watan Nuwamba na shekarar 1965 a babban birnin kasar India wato New Delhi.

Jarumin ya fara karatunsa ne a makarantar St. Columba’s School daga nan ya tafi makarantar Hansraj College, University of Delhi, Jarumin ya kammala karatun digirin sa na farko a jami’ar Millia Islamia University a bangaren tsimi da tanadi.

Ya zuwa yanzu dai jarumin yana da shekaru 54 a duniya.

A yayin da Shah Rukh khan ke murnar bikin cika shekaru 54 a duniya al’umma da dama daga sassa daban-daban na duniya sun aike masa da sakon taya murna.

Shima jarumin ya wallafa sakon godiyarsa ga daukacin masoyansa kamar yadda kuke gani a kasa.

Rubutu Masu Alaka:

Jarumi Madagwal na fama da rashin lafiya

Jarumi Akshay Kumar ya dagawa jarumi Salman Khan kafa

Labarai

Ta sanadiyar sada zumunci a shafin Whatsapp na samu matar aure – Mudansur Usman

Published

on

Kungiyar sada zumunci a shafin Whatsap mai suna, Birnin Masoya, ta ce hadin kai da sada zumunci da su ke yi a shafin Whatsapp, ya sanya har ta kai wasu daga cikin su za su auri junan su.

Shugaban kungiyar, Mudansur M Usman, ya bayyana hakan yayin taron cikar kungiyar na shekara biyu da kafuwa, ya kuma ce, sada zumunci da su ke yi a cikin shafin tsakanin maza da mata ya sanya wasu daga cikin su za su auri junan su ta bangaren samari mata da maza.

Wakilin mu Tijjani Adamu ya turo mana da rahoton sa daga wajen taron da kungiyar ta aiwatar.

Continue Reading

Addini

Rundunar Yan sandan Kano ta gargadi mutane a kan bikin Kirsimeti da sabuwar shekara

Published

on

Rundunar ‘yan sandan Kano ta ce za ta bayar da cikakken tsaro, domin ganin an gudanar da bukukuwan Kirsimeti da na sabuwar shekara cikin kwanciyar hankali da lumana.

Jami’in hulda da jama’a na rundunar, DSP Abdullahi Haruna Kiyawa ne ya bayyana hakan ga manema labarai a ranar Juma’a.

Ya ce”Rundunar mu a shirye ta ke tsaf wajen haramta harba knockout tare da masu kona tayoyi, saboda haka kowa ya tabbata ya bamu gudunmawa wajen ganin komai ya tafi lafiya, iyaye su jawa ‘ya’yan su kunne”. Inji DSP Kiyawa.

Rundunar ta kuma gargadi masu yin gudun ganganci da mota da su kiyaye doka tare da ganin bas u yi wasan tseren mota ba, musamman ma a murnar sabuwar shekara ta 2022.

Continue Reading

Labarai

‘Yan mata ku guji samarin Shaho – ‘Yan Sanda

Published

on

Rundunar ƴan sandan jihar Kano ta kara samun ƙorafi daga wata budurwa a kan matashin da rundunar ta kama a baya, wanda ya ke yi wa ƴan mata dabaru ya ke guduwa da wayoyin su da kuma abinda ya sawwaƙa.

Mai magana da yawun rundunar, DSP Abdullahi Haruna Kiyawa ne ya bayyana hakan ga manema labarai a daren Talata, inda ya ce”Matashin mai suna Saifullahi Muhammad, duk da an kaishi kotu za mu ƙara faɗaɗa bincike a kai, domin ƙara ɗaukar matakin da ya dace a kansa”.

Wakilin mu Hassan Mamuda Ya’u ya rawaito mana cewar, daga bisani kuma rundunar ta gargaɗi ƴan mata da su ƙara kulawa da irin samarin da su ke nuna suna son su, domin kaucewa faɗawa komar ɓata garin samari.

Continue Reading

Trending