Connect with us

Siyasa

Yanzu ne Buhari ya fara bin dokar kasa –Kwamaret Hamisu K/Na’isa

Published

on

Wani manazarci kan al’amuran yau da kullum kuma shugaban kungiyar cigaban ilimi da cigaban dimokradiyya a Kano Kwamaret Umar Hamisu Kofar Na’isa ya bayyana cewa a yanzu gwamnatin tarayya ta fara bin tsarin dokokin kasa, ba kamar lokutan baya ba inda gwamnatin ke yin fatali da umarni da kotunan kasar nan ke bayarwa.

Idan muka kalli batun Sambo dasuki lokutan baya ana tuhumar sa da laifin barnatar da kudade tare da laifin mallakar makamai ba bisa ka’ida ba, kuma kotuna daban-daban sun bada belinsa har sau tara amma gwamnatin tarayya tayi biris da umarnin a cewar Hamisu Umar.

Kazalika wannan mataki na rashin bin doka ya sanya wasu daga cikin gwamnatocin jihohi sunyi koyi da ita wajen kin bin umarnin kotunan.

Amma matakin da Buhari ya dauka a yanzu na sakin Sambo Dasuki da Omeyele Sowore ya fara nunawa duniya cewa gwamnatin Najeriya ta fara bin doka, kuma muna fatan a dore da haka, domin tabbatar da adalci a kasar mu.

Labarai masu alaka:

Alakar shugaban kasa Buhari da Tunubu zai haifar da ‘yan kallo a shekarar 2023

Don mu bunkasa tattalin arzikin kasa da tsaro yasa muka rufe boda – Buhari

Siyasa

Abinda ya sa muka kori Gudaji Kazaure -APC

Published

on

Jam’iyyar APC a jihar Jigawa ta kori fitaccen dan majalisar nan Muhammad Gudaji Kazaure daga jam’iyyar.

Cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun shugabannin jam’iyyar APC na mazabar Yamma a karamar hukumar Kazaure su goma sha tara, ta ce shuwagabannin mazabar sun amince da korar Gudajin daga jam’iyyar.

Sanarwar mai dauke da kwanan watan ranar Laraba ta ce dukkanin shuwagabannin mazabar sun amince da wannan mataki na korar dan majalisar.

Sanarwar ta ce an kori Gudaji Kazaure ne saboda rashin bin dokokin jam’iyyar.

Gudaji Kazaure dai shi ne dan majalisa mai wakiltar kananan hukumomin Kazaure, da Roni, da Gwiwa da kuma ‘Yan Kwashi.

Continue Reading

Labarai

Mustapha Jarfa ya kasa cika sharudan kotu

Published

on

Tun ranar Alhamis din nan ce, kotun majistrate mai lamba 47 dake zaman ta a unguwar Gyadi Gyadi a Kano ta sanya dan siyasa, Mustafa Jarfa a hannun beli, bisa wasu sharuda cewa, sai ya kawo mai mataki na 14 a aikin gwamnati ko a karamar hukuma ko jiha koma a tarayyar kasar Nijeriya, da kuma mutumin da ya biya haraji na shekara biyar sharadi na uku shi ne ba zai yi magana a wata kafar sadarwa ba, har sai an gama shari’ar, Idan kuma ya tesrewa kotu wadanda suka tsaya masa za su biya Naira dubu dari bibiyu kowannan su..

To sai dai kasancewar bai cika sharudan ba, an kuma kama shi tare da kai shi gidan ajiya da gyaran hali, inda a ka damka shi a hannun jami’in gidan, Babangida Sani da masu taimaka masa Nasir Ado da Mubarak Sani Karkarna.

Baki shi ke yanka wuya inji masu iya Magana, domin kuwa tun da fari a na zargin Mustapha Jarfa da ta da hargitsi a cikin al’umma da barazana ga rayuwar mataimakin gwamnan, Kano Nasir Yusuf Gawuna da kuma bata masa suna, wanda kuma tun a baya ya musanta zarge-zargen.

A cikin tuhumar da a ke yi masa a baya akwai zagi da cin mutumcin mataimakin gwamnan na Kano, ya kuma amsa laifin inda waccan kotun majistrate mai lamba 34 ta yi masa hukuncin daurin shekara guda a gidan ajiya da gyaran hali ba kuma tare da zabin biyan tara ba.

A baya dai an gurfanar da shi ne a gaban kotun majistrate, mai lamba 34, dake zaman ta a Rijiyar zaki, inda yanzu kuma a ka canja masa kotun, kamar yadda wakilin mu Abubakar sabo ya rawaito.

Continue Reading

Labarai

An bada belin Mustapha Jarfa  

Published

on

A Alhamis din nan ne 20-02- 2020, kotun majistrate mai lamba 47 dake zaman ta a unguwar Gyadi-Gyadi ta sanya dan siyasan nan Mustapha Jarfa a hannun beli, bisa sharadin cewa sai ya kawo mai mataki na 14 a aikin gwamnati ko a karamar hukumar ko jiha ko kuma a tarayya tare da mutumin da ya biya haraji na shekara biyar, sharadi na uku shi ne ba zai yi magana a wata kafar sadarwa ba har sai an gama shari’ar. Idan kuma ya tserewa kotu wadanda suka tsaya masa za su biya naira dubu dari bibiyu.

Sai dai kasancewar bai cika sharudan ba, an sake mai da shi gidan ajiya da gyaran hali, inda a ka damka shi a hannun jami’in gidan, Babangida Sani da masu taimaka masa Nasir Ado da Mubarak Sani Karkarna.

Tun da fari dai a na zargin sa ne da tayar da hargitsi a cikin al’umma da barazana ga rayuwar mataimakin gwamnan Kano, Nasir Yusuf Gawuna da kuma bata masa suna harda zagi da cin mutuncin mataimakin gwamnan, ya kuma amsa laifin inda waccan lokutan majistrate mai lamba 34 ta yi masa hukuncin daurin shekara guda a gidan ajiya da gyaran hali ba kuma tare da zabin biyan tara ba.

A baya dai an gurfanar da shi ne a gaban kotun majistrate, mai lamba 34, dake zaman ta a Rijiyar zaki, inda yanzu kuma a ka canja masa kotun. Kamar yadda wakilin mu Abubakar sabo ya rawaito.

 

Continue Reading

Trending

error: Content is protected !!
en_USEnglish
en_USEnglish