Connect with us

Siyasa

Barau Jibrin muke fata a 2023 –Sunusi Awuchi Gwammaja

Published

on

Wani dan siyasa a jihar Kano Sunusi Awuchi Gwammaja ya bayyana cewa babu wanda ya dace ya gaji kujerar gwamnan Kano Dakta Abdullahi Umar Ganduje 2023 kamar Sanata Barau I. Jibril Maliya

Yayin tattaunawar da Awuchi Gwammaja yayi da gidan rediyon Dala ta cikin shirin Hangen Dala na jiya Talata, ya bayyana cewa kaf Najeriya babu jihar da sukai dacen gwamna mai aiki kamar jihar Kano.

Haka kuma ya ce baya ga ayyukan da gwamna Ganduje keyi na alkhairi, to babu wanda ya dace ya gajeshi kamar Sanata Barau I. Jibril, saboda irin gudumawar da yake bayarwa a majalisa da babban kwamitin da ya rike na kasafin kudi.

A cewarsa sunyi hakan ne saboda kada ‘yan jam’iyyar hamayya su samar da wani yunkuri na wanda zai gaji gwamnatin jihar Kano.

Labarai masu alaka:

Mun siyo na’urar da zata rika gano mana masu laifi a duk inda suke –Ganduje

Saurari shirin Hangen Dala na ranar Juma’a 27 09 2019

Siyasa

Abinda ya sa muka kori Gudaji Kazaure -APC

Published

on

Jam’iyyar APC a jihar Jigawa ta kori fitaccen dan majalisar nan Muhammad Gudaji Kazaure daga jam’iyyar.

Cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun shugabannin jam’iyyar APC na mazabar Yamma a karamar hukumar Kazaure su goma sha tara, ta ce shuwagabannin mazabar sun amince da korar Gudajin daga jam’iyyar.

Sanarwar mai dauke da kwanan watan ranar Laraba ta ce dukkanin shuwagabannin mazabar sun amince da wannan mataki na korar dan majalisar.

Sanarwar ta ce an kori Gudaji Kazaure ne saboda rashin bin dokokin jam’iyyar.

Gudaji Kazaure dai shi ne dan majalisa mai wakiltar kananan hukumomin Kazaure, da Roni, da Gwiwa da kuma ‘Yan Kwashi.

Continue Reading

Labarai

Mustapha Jarfa ya kasa cika sharudan kotu

Published

on

Tun ranar Alhamis din nan ce, kotun majistrate mai lamba 47 dake zaman ta a unguwar Gyadi Gyadi a Kano ta sanya dan siyasa, Mustafa Jarfa a hannun beli, bisa wasu sharuda cewa, sai ya kawo mai mataki na 14 a aikin gwamnati ko a karamar hukuma ko jiha koma a tarayyar kasar Nijeriya, da kuma mutumin da ya biya haraji na shekara biyar sharadi na uku shi ne ba zai yi magana a wata kafar sadarwa ba, har sai an gama shari’ar, Idan kuma ya tesrewa kotu wadanda suka tsaya masa za su biya Naira dubu dari bibiyu kowannan su..

To sai dai kasancewar bai cika sharudan ba, an kuma kama shi tare da kai shi gidan ajiya da gyaran hali, inda a ka damka shi a hannun jami’in gidan, Babangida Sani da masu taimaka masa Nasir Ado da Mubarak Sani Karkarna.

Baki shi ke yanka wuya inji masu iya Magana, domin kuwa tun da fari a na zargin Mustapha Jarfa da ta da hargitsi a cikin al’umma da barazana ga rayuwar mataimakin gwamnan, Kano Nasir Yusuf Gawuna da kuma bata masa suna, wanda kuma tun a baya ya musanta zarge-zargen.

A cikin tuhumar da a ke yi masa a baya akwai zagi da cin mutumcin mataimakin gwamnan na Kano, ya kuma amsa laifin inda waccan kotun majistrate mai lamba 34 ta yi masa hukuncin daurin shekara guda a gidan ajiya da gyaran hali ba kuma tare da zabin biyan tara ba.

A baya dai an gurfanar da shi ne a gaban kotun majistrate, mai lamba 34, dake zaman ta a Rijiyar zaki, inda yanzu kuma a ka canja masa kotun, kamar yadda wakilin mu Abubakar sabo ya rawaito.

Continue Reading

Labarai

An bada belin Mustapha Jarfa  

Published

on

A Alhamis din nan ne 20-02- 2020, kotun majistrate mai lamba 47 dake zaman ta a unguwar Gyadi-Gyadi ta sanya dan siyasan nan Mustapha Jarfa a hannun beli, bisa sharadin cewa sai ya kawo mai mataki na 14 a aikin gwamnati ko a karamar hukumar ko jiha ko kuma a tarayya tare da mutumin da ya biya haraji na shekara biyar, sharadi na uku shi ne ba zai yi magana a wata kafar sadarwa ba har sai an gama shari’ar. Idan kuma ya tserewa kotu wadanda suka tsaya masa za su biya naira dubu dari bibiyu.

Sai dai kasancewar bai cika sharudan ba, an sake mai da shi gidan ajiya da gyaran hali, inda a ka damka shi a hannun jami’in gidan, Babangida Sani da masu taimaka masa Nasir Ado da Mubarak Sani Karkarna.

Tun da fari dai a na zargin sa ne da tayar da hargitsi a cikin al’umma da barazana ga rayuwar mataimakin gwamnan Kano, Nasir Yusuf Gawuna da kuma bata masa suna harda zagi da cin mutuncin mataimakin gwamnan, ya kuma amsa laifin inda waccan lokutan majistrate mai lamba 34 ta yi masa hukuncin daurin shekara guda a gidan ajiya da gyaran hali ba kuma tare da zabin biyan tara ba.

A baya dai an gurfanar da shi ne a gaban kotun majistrate, mai lamba 34, dake zaman ta a Rijiyar zaki, inda yanzu kuma a ka canja masa kotun. Kamar yadda wakilin mu Abubakar sabo ya rawaito.

 

Continue Reading

Trending

error: Content is protected !!
en_USEnglish
en_USEnglish