Connect with us

Labarai

Masarautar Ringim ta yi kira a karfafa zumunci

Published

on

Boran Dan Ruwatan Ringim, Alhaji Muhammad Aminu Isah, ya nemi al’ummar musulmai da su kara himmatuwa wajen sada zumunci domin rabauta da rahamar Allah (S.W.T)

Alhaji Muhammad Aminu Isah, ya yi wannan kiran ne a yayin da iyalan Mallam Alhassan Lasan, suka shirya taron sada zumunci, wanda ya gudana a unguwar Sani mai Nagge dake yankin karamar hukumar Gwale a Kano.

Ya ce “Sada zumuncin a tsakanin juna abu ne da yakan kara karfafa zumunta a cikin al’umma baki daya kuma hakan yakan kara dankon zumunci ga ‘yan uwa da abokan arziki”.

Shi kuwa Shugaban hada taron, Mallam Abubakar Sabo Isah, ya ce”Suna hada taron ne domin karfafa  zumunci a tsakanin su musamman ma ta yadda dangin su za s uke shaida ‘yan uwan su a duk inda suke a fadin duniya”.

Hakazalika itama a nata jawabin shugaba a bangaren mata, Hajiya Saude Zakariyya, ta ce” Iyaye da su rinka gudanar da auren zumunci a tsakanin dangi domin hakan zai karfafa zumunci a tsakanin juna da kuma bunkasa zuri’a sakamkon a zamanin yanzu ba’a fiye samun damar yin hakan ba”.

Wakilin mu Hassan Mamuda Ya’u ya rawaito cewa, ‘yan uwa daga cikin ahalin Mallam Alhassan Lasan ne suka halarci taron sada zumuncin wadanda suka zo daga jihohi daban daban daga fadin cikin kasar Nijeriya.

Labarai

Ba mu san Hamisu Breaker ya saki waƙar Amanata ba – Hukumar tace fina-finai

Published

on

Hukumar tace Fina-finai da Ɗab’i ta jihar Kano ta ce yanzu haka tana kan bincike don gano yadda akai mawakin nan Hamisu Breaker, ya saki sabuwar wakarsa mai suna “Amanata” ba tare da an tantance ta ba.

Mai magana da yawun hukumar Abdullahi Sani Sulaiman, shi ne ya bayyana hakan a wani sakon murya da ya aikowa Dala FM Kano, a ranar Alhamis 24 ga watan Afrilun 2025.

Ya kuma ce aikin dakatar da wakar ba na hukumar Hisbah ba ne na hukumar tace fina-finai ne, amma ba laifi ba ne kasancewar duk hukumomi ne na Gwamnati, a don haka idan hukumar ta Hisbah ta magantu akai babu laifi, domin dama suna aiki kafaɗa da kafaɗa.

A game da wakar ta Hamisu Beraker, mai suna “Amanata”, Abdullahi Sani, ya ce su har yanzu ba su san ta ina wakar ta fita ba tare da an tantance ta ba, amma tuni shugaban hukumar Abba Al-mustapha ya bada umarnin gudanar da bincike akan ta.

Hukumar Hisbah ta Jihar Kano ce dai ta hannun mataimakiyar babban kwamandan ta a ɓangaren mata Dakta Khadijah Sagir Sulaiman, ta yi Allah wa-dai da wakar Hausar mai taken “Amana ta” da mawaki Hamisu Breaker ya rera, inda ta shawarci matasa da su guji sauraren wakar, bisa yadda take ɗauke da abubuwan da ke ƙarfafa aikata alfasha, da kuma amfani da kalmomin batsa a cikin bidiyon ta.

Continue Reading

Hangen Dala

Rashin wuta: Muna cikin mawuyacin hali – al’ummar Kano, Katsina da Jigawa

Published

on

Al’ummar jihohin Kano, katsina da Jigawa na fuskantar yanayi mara dadi, Sakamakon karancin samun wutar lantarki daga hukumar KEDCO.

Al’ummar jihohin sun ce iya sa’o’i uku kacal suke samun wutar, wanda hakan ke haifar musu da nakasu a harkokin kasuwancin su.

Wani bincike da jaridar Daily Trust tayi ta ambato yadda masu kananan masana’antu irin su Walda, Cajin Waya, Kankara da masu sana’ar dinki da dai sauran kananan sana’o’i dake amfani da wutar lantarki sun shiga mawuyacin hali.

Kazalika rashin wutar ya shafi hatta bangaren ruwan sha, dama masu sana’ar sayar da Ruwa a irin yankunan Hotoro da sauran irin wuraren dake sayen ruwa, Inda yanzu haka ruwan yayi tashin gwauron zabi a kowace jarka.

Koda dai ana ta bangaren hukumar rarraba hasken wutar lantarkin me kula da shiyyar Kano, Katsina da Jigawa KEDCO sun nemi afuwar al’umma.

Idan za’a tuna dai a makon jiya ne Ministan Wutar lantarki yace ‘yan Nigeria Miliyan 150 na samun wadatacciyar wutar lantarki.

Sai dai kuma a jihohi irin su Kano, Katsina da Jigawa na bayyana damuwa kan karancin Wutar, Inda suka ce bata wuce ta sa’o’i uku suke samu a kowa ce rana.

Continue Reading

Hangen Dala

Rashin wuta:- Muna cikin mawuyacin hali – al’ummar Kano, Katsina da Jigawa

Trending