Manyan Labarai
Rikici ya barke a tsakanin Malaman Islmaiyya da ‘yan kwamiti

Hukumar Shari’a ta Jihar Kano ta ce ta samar da sulhu a tsakanin ‘yan kwamitin makaranatar Tarbiyatul Auwlad da kuma malaman makarantar dake unguwar Chirancin a karamar hukumar kumbotso.
Mai rikon mukamin shugabancin hukumar, Malam Bashir Ibrahim, ya bayyana hakan ne a wata takarda mai dauke da sa hannun jami’in hulda da jama’a na hukumar, Sani Muhammad Sadiq, ya sanyawa hannu.
Ya na mai cewa” An samu cimma daidaiton ne bayan kiran bangarorin biyu da mu ka yi tare da sauraron su a hukumar ta shari’a kuma a ka samu fahimtar juna”.
Haka kuma anyi adu’o’in samun dorewar zaman lafiya a makarantar da jihar Kano dama Kasa baki daya.
Tun dai a baya ne Malaman makarantar suka yi yajin aiki a kan sauyawa makarantar suna zuwa Mahadi maimakon sunan ta na baya, Tarbiyatul Auwlad wanda idan malaman sun dauki mataki a kan dalibai dazarar sun aikata laifi, sai mai makarantar ya yi watsi tare da nuna bacin ran sa.
Haka zalika wannan matakin da malaman suka dauka wasu daga cikin iyayen daliban suka fito tare da nuna bacin ran su kan hukuncin dai na koyar da daliban a makarantar, wanda ta kai har sai da a ka tafi gaban hakimin Kumbotso domin ya samar da sulhu a tsakanin su.

Hangen Dala
Yau shugaban kasa zai dawo daga Faransa

Bayan ziyarar aiki ta kusan mako biyu Zuwa kasar Faransa a yau litinin ake saka ran shugaban kasa zai dawo gida Nigeria.
Cikin sanarwar da hadimin shugaban kasar kan harkokin yada labarai Bayo Onanuga ya fitar ya ce kowa ne lokaci daga yanzu shugaban kasa Asuwaju Bola Tinubu zai sauka a Nigeria domin cigaban da harkokin mulkin kasar.

Manyan Labarai
Gobara ta ƙone tarin shaguna a kasuwar Kurmi da ke Kano – ACFO Saminu Yusuf

Hukumar kashe Gobara ta jihar Kano, ƙarƙashin jagorancin babban daraktan ta Alhaji Sani Anas, ta tabbatar da ƙonewar shaguna guda shida ƙurmus a kasuwar Kurmi Jakara Ƴan Jagwal da ke jihar, sakamakon tashin Gobara.
Jami’in hulɗa da jama’a na hukumar ACFO Saminu Yusuf Abdullahi, shi ne ya bayyana hakan ta cikin wata sanarwa da ya aikowa tashar Dala FM Kano, a ranar Juma’a 18 ga watan Afrilun 2025.
“Sashin mu na karɓar kiraye-kirayen gaggawa ya karɓi kiran gaggawa daga baturen Ƴan Sandan Jakara, wanda ya sanar da tashin gobarar a safiyar Juma’ar nan; ko da jami’an mu suka je wurin sun tarar wutar ta ƙone shaguna 6 ƙurmusu, da kuma wasu shaguna biyar da wani ɓangaren su ya ƙone, “in ji Saminu”.
Kazalika, Hukumar kashe Gobarar ta jihar Kano, ta ce jami’anta sun yi nasarar kashe wutar ba tare da ta tsallaka zuwa Maƙota ba, tare da ƙoƙarin tseratar da Miliyoyin Naira a lokacin.
ACFO Saminu Yusuf, ya kuma ce hukumar za ta yi duk mai yiyuwa domin ganon musabbin tashin gobarar, kasancewar ko a baya ma kimanin sati biyu da suka gabata, sun samu makamancin tashin wutar, ko da dai ya ce babu rasa rai ko kuma jikkata a tashin gobarar.

Hangen Dala
Kofar APC a bude take ga masu shiga – Abdullahi Abbas

Jamiyyar APC a Jihar Kano tace Kofar ta a bude take ga dukkanin masu son shigowa jamiyyar.
Shugaban jamiyyar na Kano Hon Abdullahi Abbas ne ya bayyana hakan yayin wani taron manema labarai.
Abbas yace labarin dake yawo cewa akwai wadanda ke Shirin shigowa jamiyyar, su sani Kofar APCn a bude take tare da maraba ga dukkanin wadanda zasu shigo.
Koda dai Abdullahi Abbas yace shigowa APC ba zai hana tuhuma kan zargin cin hanci da rashawa ba, koma kaucewa hukumar EFCC da ICPC.
A baya bayan nan ne dai aka rinka yada cewa mabiya jamiyyar NNPP kwankwasiyya na Shirin shiga jamiyyar APC tare da madugun ta Sanata Rabiu Musa Kwankwaso.

-
Nishadi5 years ago
Ina neman mijin aure – Rayya
-
Labarai5 years ago
Hamisu Breaker ya kai kan sa wajen ‘yan sanda
-
Nishadi6 years ago
Mansura Isah ta yi kaca-kaca da Sadiya Haruna
-
Manyan Labarai5 years ago
KAROTA: An baiwa Baffa Babba wa’adin kwanaki bakwai
-
Labarai5 years ago
Auren dan Panshekara da ba Amurkiya ya samu cikas
-
Lafiya3 years ago
Rahoto: An gano wani gida da ake gini da takardun Kur’ani da Alluna
-
Manyan Labarai5 years ago
Sabuwar damfarar da ta fito a Kano
-
Nishadi5 years ago
An gano daliban da Adam Zango ya dauki nauyin karatun su