Labarai
Kano: Yarinya ‘yar shekara biyu ta shiga kangin tallace-tallace
Da safiyar yau Alhamis ne wasu matasa Sulaiman Abdullahi Bala da Amina Salisu su ka ga wata karamar yarinya dake unguwar Kwanar Jaba a Jihar Kano, ‘yar kimanin shekaru biyu ta na sayar da wainar filawa.
Matasan sun kawo yarinyar gidan rediyon Dala inda su ka bayyana takaicin su kan yadda yarinyar da sanyin safiya ta fito talla ko magana ba ta iya yi sosai.
Sulaiman Abdullahi ya ce, “Ina kan hanya ne, zan je in sayi wani abu a garin kwanar Jaba, sai naga an taru ina zuwa sai naga yarinya ce an zagaye ta ga kuma robar wainar filawa a hannunta da kuma kudi, na tambaya sai a ke ce min wannan yarinyar talla take, sai na ga wannan ma idan ka bata kudi ba za ta iya irgawa ba, ya za a yi mutum ya sayi abu kuma ta bashi canji? sanyi ma zai iya kama ta, nima abun ya ba ni tausayi”.
Naji kayi maganar sanyi wacce irin shiga ce a jikinta?
“Hijabi ne a jikinta, sai wata ‘yar riga sai dan takalmi. Naga kudi a hannunta kusan Naira Dari Biyu. Ni fatana a duba a gani wannan yarinyar ai ta yi karama. Akwai wadanda a wajen ma sun san ta, domin ta na kawo talla wajen su.” Inji Sulaiman
Ya kuma kara da cewa, “Iyayen ta su tsaya su duba, wannan ai, abun dubawa ne, yaro kamar wannan karama ce sosai cin zarafin yara ne”.
A nata bayanin Amina Salisu ta ce, “Mun kai yara makaranta, sai mu ka yi magana da wata zan karbi wani abu a hannun ta, muna zuwa sai muka ga taro ana ta korafi, wata yariyna ce karama take ta zuwa ta na kawo talla a cikin gida, shi ne abun ya ba ni tausayi na tsaya na ce gaskiya bai dace yarinya karama kamar wannan an bar ta tana talla, saboda haka na ce ya dace in kai ta inda za a tallafa mata”.
To kun nemi iyayen ta, ko kuji wane hali a ke ciki?
“Gaskiya bamu nema ba, abun da ya sa bamu nema ba saboda ance yarinyar in tayi laifi har a turken dabbobi a ke daure ta a dake ta. Ka ga ma hannun ta shaida ce karaya ce aka yi mata, kuma jikin ta in ka duba shaidar duka ne.” Inji Amina.
Wakilin mu Aliyu Wali, ya zanta da yarinyar ta na mai cewa, “Waina nake sayarwa, biyu Naira biyar, babarmu ta na gida, sunan ta Rabi, baban mu sunan sa Sani, ni kadai ce ba ni da kani, da safe nake fitowa talla, ina zuwa islamiyya, ba na zuwa boko”.
Naga ciwo a hannunki me ya ji miki ciwo?
“(Kuka) Wani yaro ne yaji min ciwo a unguwar mu ba abun da na yi masa”.
Mutanen da su ka tsince ta a unguwar ta Jaba sun kuma ce, za su mayar da ita gida ne sun kawo ta gidan rediyo ne domin a tallafa mata domin yara irin ta su ne wadanda a ke cutarwa a yi musu fyade, tare da sace su a sauya masu suna.
Wakilin mu Aliyu Wali da Abba Isah Muhammad, sun garzaya zuwa hukumar Hisba tare da yarinyar da kuma wadanda suka tsinto ta, a nan ne kuma hukumar ta bazama neman iyayen yarinyar domin an bi mata hakin ta. Sai dai a nan gaba zaku ji sauran labarin.
Labarai
Sarkin Kano Khalifa Muhammadu Sunusi na biyu, ya naɗa Ɗan Sa a matsayin Chiroman Kano.
Mai martaba sarkin Kano Dakta Khalifa Muhammadu Sunusi na biyu, ya buƙaci dukkanin hakimansa da ke faɗin jihar nan da su mayar da hankali wajen gudanar da aikin su bisa gaskiya da riƙon Amana.
Sarkin ya bayyana hakan ne a lokacin da ya naɗa DSP Aminu Lamiɗo Sunusi a matsayin Chiroman Kano, kuma babban ɗan fadar Sarki, yau Juma’a a fadar sa.
Khalifa Muhammadu Sunusi na biyu, ya ce ya naɗa DSP Aminu Lamiɗo Sunusi a matsayin Chiroman Kano, ne bisa cancanta da zuminci da kuma gogewarsa akan aikinsa na ƴan sanda, tare kuma da taimakawa al’umma da yake yi a koda yaushe.
Mai martaba sarkin ya kuma taya Chiroman Kano, murna bisa wannan naɗin da aka yi masa, tare da fatan zai zamo jakada na gari musamman wajen samar da cigaban Al’umma da kuma masarautar Kano.
Wakilinmu na masarautar Kano Shamsu Da’u Abdullahi ya rawaito cewa taron naɗin ya samu halartar gwamnan jihar Kano Injiniya Abba Kabir Yusuf, da sarakunan gargajiya daga wasu daga cikin jahohin ƙasar nan.
Labarai
Za mu magance matsalolin da hukumar Hisbah ta Dala ke fuskanta – Shugaban ƙaramar hukumar Dala
Ƙaramar hukumar Dala ta ce za ta yi bakin ƙoƙarin ta wajen magance matsalolin da hukumar Hisbah ta ƙaramar hukumar Dala ke fuskanta, domin ƙara ƙarfafa musu gwiwa wajen gudanar da ayyukan al’umma.
Shugaban ƙaramar hukumar Suraj Ibrahim Imam ne ya bayyana hakan, a lokacin da jami’an hukumar Hisbah ta ƙaramar hukumar Dala, suka ziyarce shi a ofishinsa, domin taya shi murnar nasarar cin zaɓe da suka yi, tare da sanar dashi halin da hukumar Hisbar ke ciki a halin yanzu.
“Daga cikin ƙalubalen da zan yi ƙoƙarin magance wa akwai samar da ruwa da wutar lantarki da kuma samar wa hukumar kayan aiki, bisa yadda suke fama da rashin su, “in ji Suraj Imam”.
Shugaban ƙaramar hukumar ta Dala Sura ya kuma yi kira ga babban kwamandan hukumar Hisbah ta jihar Kano Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa, da ya ƙara kulawa da walwalar hukumar ta ƙaramar hukumar Dala bisa ƙalubalen da suke fuskanta.
Da yake nasa jawabin kwamandan hukumar Hisbah ta ƙaramar hukumar Dala Mallam Umar Bala Muhammad, ya ce sun ziyarci shugaban ƙaramar hukumar ne domin taya shi murnar nasarar cin zaɓe da kuma sanar da shi halin da hukumar ke ciki, domin haɗa ƙari da ƙarfe wajen magance ƙalubalen da suke fuskanta.
Wakiliyarmu Hadiza Balanti ta rawaito cewa Mallam Umar Bala ya kuma ƙara da cewa a shirye hukumar hisbar ta ƙaramar hukumar Dala take wajen gudanar da ayyukan al’umma babu gajiyawa.
Labarai
Mun dakatar da karɓar kuɗin haraji a Fagge har sai an kammala bincike – Shugaban Ƙaramar hukumar Fagge
Ƙaramar hukumar Fagge ta dakatar da dukkannin harkokin karɓar haraji har zuwa lokacin da za’a kammala bincike, don tabbatar da cewa bangaren harajin nayin aiki bisa doka domin ciyar da ƙaramar hukumar gaba.
Shugaban ƙaramar hukumar ta Fagge Salisu Usman Masu ne ya bayyana hakan yayin zantawar sa da tashar Dala FM Kano, a safiyar yau Talata.
Salisu Usman ya kuma bayyana cewar duk filotan da aka yanka aka sayar ko aka bayar ba bisa ƙa’ida ba shima an soki shi.
Shugaban ya kuma yi kira ga ƴan kwangila waɗanda suka watsar da ayyukan da aka basu da su dawo bakin aiki ka’in da na’in.
A cewar sa, “Na fahimci irin kalubalen da ke damun al’umma a ɓangaren lafiya a ƙaramar hukumar mu ta Fagge; kuma za mu yi ƙoƙarin samar da kayan aiki domin magance matsalar, “in ji shi”.
Masu ya kuma bayyana cewar ƙaramar hukumar ta Fagge za ta inganta harkar ilimi da tsaro, da Lafiya, inda kuma yi kira ga duk wani mai kaunar ci gaban karamar hukumar Fagge da ya taho a hada hannu ko da shawara zai bayar dan ciyar da karamar hukumar gaba.
-
Nishadi5 years ago
Ina neman mijin aure – Rayya
-
Labarai4 years ago
Hamisu Breaker ya kai kan sa wajen ‘yan sanda
-
Nishadi5 years ago
Mansura Isah ta yi kaca-kaca da Sadiya Haruna
-
Manyan Labarai5 years ago
KAROTA: An baiwa Baffa Babba wa’adin kwanaki bakwai
-
Labarai5 years ago
Auren dan Panshekara da ba Amurkiya ya samu cikas
-
Lafiya2 years ago
Rahoto: An gano wani gida da ake gini da takardun Kur’ani da Alluna
-
Manyan Labarai5 years ago
Sabuwar damfarar da ta fito a Kano
-
Nishadi5 years ago
An gano daliban da Adam Zango ya dauki nauyin karatun su