Connect with us

Labarai

Dalilan da ya sa aure ba ya dadewa a Kano

Published

on

Limamin masallacin juma’a na hukumar shari’a ta jihar Kano dake kan titi Abdullahi Bayero a karamar hukumar Nassarwa, Malam Murtala Muhammad Adam, ya ce abubuwan dake kawo yawaitar mace-macen aure a cikin al’ummar hausawa na da nasaba da rashinn sanin karantarwar addini.

Malam Murtala, ya bayyana hakan ne jim kadan bayan kammala hudubar sa ta juma’a, inda ya ce” Da yawa daga matasa na yin auran jari wanda zaka ga sun aure a basu gida, a basu mota harma jari mai gwabi wanda hakan ya kan jawo mutuwar zuciyar matasa, kuma a karshe auran baya zuwa ko ina sai ya mutu sakamakon kwadayi da a ka saka a ciki. Wasu matasa kan sa karya a cikin auren, yadda za su aro kayan sawa da motoci karshe bayan anyi auren sai ka ga biyan kudin gidan haya ya gagara sai sai ka ga aure na mutuwa ba wani dadewa a ka yi ba a gidan miji”. Inji Malam Murtala.

Limamin, Malam Murtala Muhammad Adam, ya kuma bukaci iyaye da su guji yi wa ‘ya’yan su auren dole tare da zurfafa bincike ya yin neman auren ‘ya’yan su sakamakon gudin abun da ka iya zuwa ya dawo.

 

 

Hangen Dala

Yau shugaban kasa zai dawo daga Faransa

Published

on

Bayan ziyarar aiki ta kusan mako biyu Zuwa kasar Faransa a yau litinin ake saka ran shugaban kasa zai dawo gida Nigeria.

Cikin sanarwar da hadimin shugaban kasar kan harkokin yada labarai Bayo Onanuga ya fitar ya ce kowa ne lokaci daga yanzu shugaban kasa Asuwaju Bola Tinubu zai sauka a Nigeria domin cigaban da harkokin mulkin kasar.

Continue Reading

Labarai

Zan gina makarantun Islamiyya da ta Boko don tunawa da Mafarautan da aka kashe a Uromi – Rurum

Published

on

Ɗan majalisar Wakilai mai wakiltar ƙananan hukumomin Rano, da Kibiya da Bunkure Kabiru Alhassan Rurum, ya yi alƙawarin gina makarantu guda biyu na Islamiyya da na Boko, a garin Torankawa da ke ƙaramar hukumar Bunkure, don tunawa da mafarautan da aka kashe a garin Uromi ta Jihar Edo a kwanakin baya.

Hakan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da mataimakin ma musamman ga ɗan majalisar Fatihu Yusuf Bichi ya aikewa Dala FM Kano, Sanarwar ta ce hakan na zuwa ne yayin da Rurum, yake jajantawa al’ummar garuruwan da Iyalan mamatan 16 da aka kashe, a garin Uromi da ke ƙaramar hukumar Essan ta jihar Edo.

 

Rurum ya kuma buƙaci Mafarauta daga yankin Arewa da su dakatar da zuwa kudancin kasar da sunan Farauta, don su mutane ne dake yawo da kayan daji kuma akwai banbancin yare tsakani da hakan ke sanyawa ana yawan cin zarafin su da sunan matsalar tsaro.

 

Honarable Kabiru Alhassan Rurum, bayan addu’o’i na musamman da ya yi ga mamatan, ya kuma bai wa iyalai da ƴan uwan su haƙurin jure rashin, tare da bai wa iyalan waɗanda kisan gillar ya rutsa da su gudunmawar Naira Miliyan Biyar, domin a ɗan yi cefanen kayan abinci.

Continue Reading

Labarai

Za mu fara ɗaukar mataki akan masu zance a cikin Mota – Hukumar Hisbah

Published

on

Hukumar Hisbah ta jihar Kano ta ce ta shirya tsaf wajen ganin ta kawo ƙarshen zancen da wasu Masoya suke yi a cikin Motoci, domin daƙile ɓarnar da ke yaɗuwa ta hakan a wasu lokutan.

Mataimakin babban kwamandan hukumar Hisbah a Kano, Dr. Mujahideen Aminudden, ya bayyana hakan ne yayin zantawar sa da Dala FM Kano, a ranar Juma’a 18 ga watan Afrilun 2025.

 

“Ɗaukar wannan matakin ya zama dole kasancewar lamarin na neman ya zamar wa al’ummar jihar Kano alaƙakai, “in ji shi”.

Dakta Mujahidden ya kuma yi kira ga iyaye da su sanya idanu kan tarbiyyar ƴaƴan su, tare da rage buri wanda hakan ka iya kawo ƙarshen taɓarɓarewar tarbiyyar ƴaƴan nasu.

Continue Reading

Trending