Connect with us

Labarai

KAROTA ba ta da hurumin yi wa mutane tara a kan kullen Corona -Baba Jibo

Published

on

Wasu mutane a birnin Kano sun yi kukan cewar Jami’an hukumar KAROTA su na kama su a cikin masallacin Idi a yi musu tarar kudade har Naira dubu biyar.

Masu korafin dai sun bayyana cewar sakamakon dokar kulle Jami’an jami’an na yi mu su tara a cikin masallacin idi. A ida a ke yankewa masu babur hukuncin biyan tarar dubu uku yayin da mu su babur mai kafa uku a ke yanke masu hukuncin biyan tarar dubu biyar.

Wakilin mu Yusuf Nadabo Ismail ya kai ziyara masallacin Idin, ya kuma iske tarin masu babura wadanda su ke jiran a yanke musu hukunci a lokacin.

Harma wakilin na mu ya zanta da wasu daga cikin mutanen wadanda su ka bayyana yadda a ke yi mu su tara, Usaini Abdullahi mazaunin unguwar Gidan Zoo wanda ya ce” Na kawo wani mara lafiya zuwa asibitin Murtala kawai sai na ji kawai an kama ni a ka kai ni cikin filin Idi tare da cin tara ta”.

Shi kuwa wani matashi mai suna Magaji Idris cewa ya yi Na je ‘yan Lemon a kawo lemo zuwa cikin Fagge kawai sai wani jami’in KAROTA ya kama ni ya kai ni cikin masallacin Idi a ka kuma cini tarar dubu biyar.

Sai dai kakakin kotunan jihar Kano, Baba jibo ya ce”KAROTA ba su da hurumin yin tara a harkar kullen covid 19, domin kuwa wannan ba hurumin ta ba ne”.

Mun kuma tuntubi mai magana da yawun hukumar KAROTA Nabulisi Abubakar Kofar Na’isa wanda ya bayyana cewar” Wanda ya tabbata ya yi laifi kotu c eke da ikon ta ci tarar mutum kawai dai idan jami’an sun kama mutum za su kai su wajen kotun tafi da gidan ka a yanke mu su hukunci”.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Labarai

An kama wani matashi da zargin sacewa almajirai kayan sawa

Published

on

Shugaban kungiyar Bijilante na yankin unguwar Hausawa dake karamar hukumar Tarauni a Kano, Usaini Haruna Kailo, ya shawarci iyaye da su kara kulawa da tarbiyyar ya’yan su domin rayuwar su ta zama abar koyi a nan duniya dama ranar gobe kiyama.

Usaini Kailo ya bayyana hakan ne a yayin zantawar sa da wakilin mu Hassan Mamuda Ya’u, bayan kama wani matashi da su ka yi, da zargin diban kayayyakin sawa na almajirai cikin wata makarantar tsangaya a unguwar Hausawa ‘yan babura.

Ya ce” Matukar iyaye za su kara kulawa da tarbiyar ya’yan su babu shakka za a rage yawaitar samun lalacewar su”.

Da yake nasa jawabin matashin da a ka kama ya ce” Wannan shi ne na farko kuma shi ne na karshe ba zan kara satar kayayyakin mutane ba”.

Wakilin na mu Hassan Mamuda Ya’u ya rawaito mana cewa, Kwamandan Bijilanten Usaini Haruna Kailo ya ce, za su mika matashin da su ka kama wajen jami’an tsaro domin matakin da ya dace a kan sa domin hakan ya zama izina ga sauran matasa.

Continue Reading

Labarai

Covid-19: Gwamnatin Kogi ta karyata hukumar NCDC

Published

on

Gwamnatin Jihar Kogi ta musanta rahoton hukumar dakile yaduwar cututtuka ta kasa NCDC cewa mutum biyu sun kamu da cutar Coronavirus a jihar.

A ranar Larabar da ta gabata ne dai hukumar ta NCDC ta sanar a shafinta na Twitter cewa an samu bullar cutar Covid-19 a jihar ta Kogi inda tace mutane 2 ne ta tabbatar sun kamu da cutar a jihar.

Sai dai a cikin wata sanarwa da kwamishinan lafiya na jihar ta Kogi, Dakta Saka Haruna Audu ya musanta rahoton, inda sanarwar ta bayyana rahoton na NCDC a matsayin labarin kanzon kurege ne da bashi da tushe balantana makama.

Ya ce” A shirye gwamnatin Kogi ta ke wajen kare rayukan al’ummar ta, kuma ba za ta sanya siyasa a cikin sha’anin kiwon lafiya a jihar ba”.

Sai dai hukumar NCDC ba ta ce komai ba dangane da ikrarin na gwamnatin jihar Kogi.

Continue Reading

Labarai

Covid-19: Buhari ya nemi sake ciyo bashi

Published

on

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya sake aikewa da wata wasika ga majalisar wakilai domin sahale masa ya ciyo bashin dala Biliyan 5.

Wasikar da shugaban majalisar wakilan Femi Gbajabiamila ya karanta a gaban majalisar a yau alhamis, ta bayyana cewa, za a yi amfani da bashin ne domin cike gurbin kasafin kudin bana, na manyan ayyuka.

Kazalika ta cikin wasikar shugaban ya kuma ce za a yi amfani da bashin wajen kara tallafawa jihohi domin yaki da cutar corona.

A kwanakin bayane dai majalisa ta sahalewa shugaban kan ciyo wasu bashi na biliyan 22.

Continue Reading

Trending

error: Content is protected !!
en_USEnglish
en_USEnglish